RA'YIN ZUCI....
Chapter 4
#the rivalry#
Duk abinda yakeyi ina lura dashi ta gefan idanuna don ban nuna alamar da zata sanar dashi naasan da wanzuwarsa a dakin ba, juyar da kaina gefe nayi ina wasa da shimfiɗaɗɗen zanin gadon dana shimfiida tun bayan fitarsa.
Seda ya gama rage kayan jikinsa tsaf sannan ya daga ka ya sauke idanunsa a kaina, still ban motsa ba ina jin tasirin qwayar idannunsa a gabadaya ilahirin jikina. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tako gabana da nufin ya ranqwafa kamar yanda ya saba, cikin azama na miqe na fara qoqarin
lalubar wayata wadda ke ajiye Saman bedside drower dina.
Kafin yayi wani yunquri nayi saurin miqewa nabar masa dakin zuciyata a cike fal da haushinsa. A can qasan zuciyata na ce,"ko uwar me ze gaya min oho" na qare maganar ina jan gajeran tsaki wanda nake da tabbaci akan cewar bejini ba.
Ina fita kai tsaye daya dakin na shiga na kulle qofa don bana buqatar ya biyo bayana, na dade a tsaye ina kai komo sannan nayiwa kaina masauki a kan qaramin gadon da aka qawata dakin dashi. Shiru nayi ina tunanin wanda ya kamata in kira akan matsalar dake cimin tuwo a kwarya, lumshe idanu nayi a lokacin da naji kaina Yana qoqarin sarawa. Nan take se naji ina tausayawa duk wata mace da mijinta ke qoqarin qarowa abokiyar zama, banyi aune ba naji ruwan hawaye yana kwaranya a saman zagayayyiyar fuskata.
Komawa da baya nayi na kwanta sosai nayi balance. har lokacin ban ajiye wayar dake hannuna ba, na dade idanu na a lumshe suna zubar da hawaye sannan na budesu tar akan wayar, cikin nutsuwa na Fara qoqarin neman number din Ya Zainab. cikin yaqinin cewar zata Bani shawarar da zan samu mafita akan matsalar dake damuna.
Banyi qasa a gwiwaba na doka Mata kira Amma har ta katse ba tai picking call din ba, share hawayen nayi se kawai na lalubo number din Hajar nai dailing don ta Debe min kewar kadaicin dake tareda ni a wannan lokacin. Bugu daya nayi mata ta daga cikin nishadi ta ce,"Matar sir Yusuf. duk yanda akai kinje gidan mu ne ko?" Tayi maganar tana juya qwayar idanunta, cikin salon da ya zame Mata tamkar dabi'a
"Malama ni bazan kulaki ba. tunda kikai tafiya Baki min sallama ba" nayi maganar ina daure fuska tamkar tana Gabana babu alamun wasa a tareda ni.
"Hmmm bazaki gane ba Bilkisu. nima tafiyan yazo min ba shiri ne wllh shiyasa na tafi banyi miki sallama ba,But be patient Hajjajo, In sha Allah i will buy you something sweet idan Zan dawo Kaduna kinji?""Uhmm Allah yasa karki Saba alqawari na San halinki sarai." na firta hakan cikin yanayi me dauke da kasala
"Ke tsaya don Allah. ya naji muryanki haka What's wrong?"
"Ba abinda ke damuna yanayi ne kawai Hajar!" Na Fadi hakan ina lumshe idanu
"Fafah Are you okay ?"
Gabana ne yay wata irin faduwa Jin sunan da Hajar ta kirani dashi, Amma sai na dake ban nuna mata alamar komai ba na ce,"me kike zaton zai dameni Hajar?"
Gyara zamanta Hajar tayi tamkar tana zaune a gabana ta ce,"wllh idan nai rantsuwa bazanyi kaffara ba cewar akwai abinda ke damunki a qasan zuciyarki Bilqis, Amma tunda bazaki gayamin ba shikenan gobe ina dawowa gidanki Zan fara sauka,ko gida ba zanje ba sai kin sanar dani abinda kike boye min..." tana gama Fadin haka ta katse Kiran tana tunanin akan sauyin da tai katari dashi a cikin muryata.
YOU ARE READING
RA'AYIN ZUCI... THE OPINION OF THE HEART
FantasyRayuwar ko wani dan-adam a duniya tana gogaiya ne da irin tasa qaddarar. a gareni ma hakanne ya kasance lokacin da sanadi ya kaini makarantar kwana, tafiyata jihar Bauchi shine ya zama shafin farko a littafin tawa Ƙaddarar. daga ganin farko da muka...