Chapter 6 (The contradiction)

15 3 0
                                    

*RA'AYIN ZUCI...*

CHAPTER:6
#The contradiction#

Kafin nayi wani yunquri tuni Faridah tabar gurin idanunta na zubar da hawaye, A wannan lokaci ina tsayene kawai amma daga ciki bani da maraba da mutum-mutumi, da ƙyar na iya tattaro suran ƙwarin gwiwar daya rage min, ganin na nabi bayanta da gudu ina kiran sunanta. Sai dai ko waiwaye batayi ba ta ratsa ta ƙofar falon da zai mayar da ita part ɗinsu ta ɓacewa idanuna gabaɗaya.

"innanillahiwainnailaihirraji'un!" na sake furtawa ina ƙoƙrin ɗora hannuna bisa kaina, Cikin azama da hanzari Hajar tayi saurin janyoni tana watsa min harara ta ce,"uwar me kike jawa salati dan na mari waccen mara kunyar?" Tayi maganar tana tsareni da idanu cikin jin haushin ɗabi'ata.
Rasa amsar da zan bata nayi sai kawai na raɓa ta gefanta na koma dakin na tattaro mata jakarta da mukullin motar da tazo dashi naja hannunta muka fita harabar gidan, cikin alamun roqo na hada hannayena biyu na ce,"Don girman Allah Hajar ki tafi gida wllh bana so hajiya ta fito ta sameki, idan ta fito gurin nan Allah ne kaɗai ya san irin abinda zai faru. Iya wanda ya faru tsakaninki da da Faridah Attahiru ka ɗai ya isa haka please Twiny." Nayi maganar cikin sanyin murya

"Ai dole ki turata ta gudu tunda baki taki abin arzuqi ba munafukar Allah ta'allah wadda bakya tsoron Allah." na tsinkayi muryar Hajiya cikin hargagi a tsakiyar kaina, zuciyata ce tai wani irin amsawa kafin inyi wani yunƙuri tuni jikina ya ɗauki rawa. bansan lokacin dana ɗaga kai ina kallonsu ba.

Hajiya ce a gaba Faridah na take mata baya se Aisha Sulaiman wadda ta kafeni da idanu tana aika min da sinqi-sinqin harara wadda tasa naji na qara karaya.

Ganin yanda suka nufo gurin babu annuri a saman fuskokinsu ne yasa nayi hanzarin tura murfin motar na rufe zuciyata na tsananta bugu tamkar zata tsaga tsakanin qirjina ta fito, a zahiri so nake in shiga tsakanin Hajiya da Hajar yasa nayi wannan yunƙurin da sauran guzarin da ya rage min.Sai dai ban kai ga ida nufina ba Hajiya tasa hannu ta hankaɗeni gefe, sannan tasa hannu ta buɗe murfin motar ta cakumo wuyan rigar Hajar ta fito da ita daga cikin motar. Banda haki babu abinda Hajiya keyi amma sabida fitina da rigima irin nata bata fasa ida mnufarta ba

Kafin nayi wani yunƙuri tuni ta haɗa Hajar da jikin motar ji kake bum. Sannan ta ɗaga hannu da nufin ta zabga mata mari Hajar tayi saurin riqe hannunta ta ce," ke Babba ce Hajiya. So don't do things that make you lose your dignity in my eyes." ta faɗi hakan tana ƙoƙarin cire hannu hajiya dake wuyan rigarta.

Cikin shammata Aisha Sulaiman ta saukewa Hajar wani lafiyayyen mari me shiga a gefan fuskarta na dama, sabida yanda marin ya shigeta seda ɗankunnenta Na ɓangaren dama ya fita. Shirune ya ratsa tsakanin kunnuwan mu babu wanda ya iya cewa ƙale, sai hajar wadda ke riƙe da gefan fuskarta. Kallo ɗaya zakai mata ka fahimci ranta a mugun ɓace yake to the extent, sauke hannunta tayi daga riƙon da taiwa kumatunta. Lokaci guda ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya wadda ta fallasa haƙiƙanin ɓacin ran dake shimfiɗe a ƙirjinta, al'amarin daya ƙara firgita sauran nutsuwata kenan, na yunƙura da nufin in dakatar da ita sabida nafi kowa sanin halinta idan ranta ya ɓaci.

Hannu tayi saurin ɗaga min fuskarta a ɗaure babu salama ta isa gaban Faridah Attahiru ta tsaya tana mai ƙare mata kallo from head to toe. Sannan tayi murmushi mai sauti ta ce,"lallai mamanki tana matiƙar sonki Faridah, tunda ta kasa haƙuri a lokacin da kikaje mata da shedar yatsuna kwance a saman kumatunki." Hajar ta faɗi hakan tana jinjina girman lamarin a ranta, sedai kafin muyi aune tuni ta ƙara ɗaga hannu ta zabgawa Faridah wani sabon marin wanda yaci uban wanda tai mata a farƙo. A fisace Aisha dake tsaye tayo kan Hajar gadan-gadan da nufin ta cakumeta hajar tai mata wani kalan ihu wanda yasa taja da baya ba tareda ta shirya ba, a haukace ta juya ta kalli Hajiya ta ce," irin abinda kikaji a lokacin dana mari ƴarki irinsa Mama takeji kullum idan kuka addabawa ɗiyarta, tana jin fiye da haka a duk lokacin da kika ƙuntatama Bilkisu. Ko da yake barin dena wahalar da bakina wajan tuna miki matsayinki, kona faɗa ma bazaki gane ba tunda son zuciya yayi maki yawa." ta faɗi hakan tana ɗauke idanunta daga kanta sannan ta juya ga Aisha da Faidah ta ce"idan tashen rashin kunya kukeji wllh ni uwarku ce a wannan fanin." ta qare maganar tana watsa musu mugun kallo
Gabaɗayansu rasa wanda zaice ƙala akayi sabida sun haɗu da gamonsu, ita kuwa Aisha kasa motsin kirki tayi don bata taɓa zaton a danginsu Bilkisu akai ƴar bala'i Kamar Hajar ba. Wannan karon ita kanta Hajiya abin ya girgizata ba kaɗan ba, hakanan sai taji zuciyarta ta sosu ranta yai mata baki.
Babban takaicinta shine yanda Hajar ta rufe ido ta tsuga mata rashin kunya son ranta, amma kuma ina tsaye na kasa dakatar da ita. Kallo ɗaya zakaiwa Hajiya ka karanci mugun nufin da take ƙullawa ga rayuwata, duba da irin kallon tsanar da take watsa min.
Murmushi Hajar tayi bayan ta karanci yanayin Fuskar Hajiya sannan ta ce,"Hajjaju naga kamar akwai abinda kike son furtawa amma zuciyarki taƙi baki haɗin kai..... Na san duk abinda zaki ƙulla ba zai wuce kisa Yusuf ya saki Bilkisu ba. Bayan haka babu wani abu da zaki iya mata ya cutar da ita, amma kafin nan barin haska maki wani abu. Nifa wannan gyaran da naiwa yaranki banyi musu don komai ba sai don na kowa musu hankali sabida na lura basu da shi at all. Sannan Dan munayi muku shiru kuna aikata abinda kukaga dama akanta it does not mean that mu ƴan uwanta does not love her, kawai muna yi miki kawaicine sabida ke kaɗaice Aminiyar da Mama take da ita ne!"
Bata jira jin abinda Hajiya zatace ba ta juya tana kallon Su Aisha dake tsaye.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 04 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RA'AYIN ZUCI... THE OPINION OF THE HEART Where stories live. Discover now