chapter 2 (the Criticism)

26 4 0
                                    

*RA'AYIN ZUCI.....*
(the opinion of the heart❤)

Zm-Chubaɗo

Chapter 2

#the Criticism#
_Kiran da naiwa Yusuf a wannan lokacin.shine ya zama silar buɗewar babi na biyu a cikin littafin kaddarar rayuwarmu, Ƙaddarar data zama silar abubuwa da dama, waƴanda tunani bai taɓa hakaitowa ba. balle ya samu damar tsinkayar wani abu daga cikin abinda take ƙunshe dashi!_

_da bugun waya ɗaya takk muka samar da shaƙuwa mai girma a tsakanin zukatan mu. hakiƙa soyayya tana da girman sha'ani mai wahalar ƙaiyadewa, wanda ubangijine kaɗai ya san sirrin dake tattare a cikinta. A lokutan baya zuciyata a rufe take take ruf, kafin sanadi ya haifar da haɗuwata da Ɗan Attahiru. mutumin da ya sauya akalar rayuwata cikin ƙanƙanin lokaci, da kaifin harshen da ubangiji yay masa baiwa dashi. wanda zan iya fassarawa da makami mafi girma da haɗari ga zuciyar ko wacce ɗiya mace a duniya. Duk yanda zan siffanta muku yusuf da kalaman bakina ba zaku taɓa fahimta girman sha'aninsa ba, har sai kunyi nutso cikin labarin Hikayata sannan zaku iya fahimtar komai tareda maƙasudin faruwarsa._

_Juyawa nayi a hankali na gyara kwanciyata bisa ƙatuwar katifar da na shimfiɗe da lallausan zanin gado, sannan na ƙara ƙanƙame wayar dake riƙe a hannuna ina tunanin ta inda ya kamata na fara. Lumshe idanu nayi ina jin yanda ƙaunarsa ke ƙara farmakar zuciyata, kafin nayi ƙundumbala na danna hatimin kiran dake jikin wayar, ina jin yanda zuciyata ke harbawa._

_Wayar na manne a fatar kunnena ta fara ringing ban san sanda wani ƙayataccen murmushi ya ratso ta tsakanin laɓɓana ya fito ba. Sai dai ina ji kiran ya katse ba tareda ya ɗauka ba, murmushin dake kwance a fuskata ne yay ɓatan dabo tamkar bai taɓa wanzuwa a ilahirin fuskata ba, ajiyar zuciya na sauke tareda ɗora wayar a ƙirjina na ƙanƙameta ina sauke numfashi daƙyar._

_Na jima a haka ba tareda nayi gigin ƙara kiransa ba, haka na afka cikin duniyar tunanin dalilinsa na rashin amsa kirana, ina tsaka da wannan tunanin ƙarar kiransa ya karaɗe ilahirin kunnuwana._

_Misalta irin farin cikin da zuciyata ta shiga a wannan lokacin abune da ba zai kwatantu ba a gareni, hannu nasa na shafe ruwan hawayen dake kwaranya bisa fatar kumatuna, sannan na fizgo maganar dake maƙale tsakanin maƙoshina na ce,"Sherriey!" na kirashi da sunan da zuciyata ta raɗa masa tun farkon fara soyayyata dashi._

_Lumshe kamilallun idanunsa yayi tareda da sauke wani wahalallen Numfashi tamkar Yana gaba na. Kasa cewa komai yayi illa sauke ajiyar zuciya da yake yi, wanda sautinta ke kutsawa cikin kunnuwana ba tareda shamaki ba, cikin sautin muryarsa wadda na jima ina kewa a cikin ko wani dare idan na kwanta bacci ya ce,"An ɗauki lokaci mai tsayi ina fama da kewarki. ta yanda ba zan iya siffanta girman yanayin ba. bansan ta yanda zan kwatanta miki ki fahimta ba, amma nayi alƙwarin ba zan ƙara bari kiyi nisa dani makamancin wannan ba, no matter what happens to me sai nazo inda kike Ruhiey!" ya firta hakan cikin wani wahalallen yanayi mai kai farmaki ga zuciyar wanda ke sauraronsa._

_Rintse idanu nayi da ƙarfi ina jin yanda kalmansa ke yanka zuciyata suna samawa kansu mazauni, ban san me ya kamata in faɗa masa ba, amma har cikin zuciyata ina so na bashi labarin yanda nai kewarsa. Sai dai bansan taya zanyi Expressing how I feel about him ba!_

_Shirune ya biyo bayan maganarsa. sai dai ta tsakanin shirun dake kai komo a tsakanin mahaɗar kunnuwa da ƙwaƙwal. yake jin sautin kukana a hankali yana fita, wanda ke ratsa ko wace kafa ta jikinsa a lokaci guda, in a very calm voice ya langaɓar da kansa ya ce,"kuka baya taɓa zama magani ga abinda zuciya ke so Ruhiey. amma ina da yaƙinin cewa ganin juna zai iya ɗebe mana kaso tamanin a cikin ɗari na zugin dake kai komo a tsakankin zukatan mu. Gobe da safe zanzo gidanku taɗi, idan da Hali ina so naga BILKISU IBRAHIM SAMINAKA cikin ado mafi kyau da ƙawatuwa. wannan kaɗai ya isa ya bawa zuciyar YUSUF ATTAHIRU farin cikin da ya Jima beyi katari dashi ba." ya firta hakan cikin murmushi mai sauti_

RA'AYIN ZUCI... THE OPINION OF THE HEART Where stories live. Discover now