*RA'AYIN ZUCI....*CHAPTER 3
#the accidental marriage#
Tun daga wannan maganar ban ƙara firta komai ba. haka tafiyar ta kasance a tsakaninmu tamkar masu ciwon baki. wanda hakan ba ƙaramin daɗi yaymin a raina ba don ban shirya yin magana mai tsaho dashi ba, har lokacin zuciyata a hasale take dashi. na kasa manta abinda kunnuwana sukai katarin ji yana furtawa ga abokinsa Doctor Umar, har yanzu ban huce da jin zafin kaifafan kalaman da suka ratso ta tsakanin laɓɓansa ba wayanda naji yana furtawa ga likitan dake karanta masa halinda rayuwata ke ciki ba ɗazu. wannan yasa na maida hankalina ga window ɗin motar ina kallon yanda mutane keta hada-hadarsu.
komawa nayi na jigina bayana a jikin kujerar da nake zaune akai tareda lumshe idanuna, a haka ya juya kan motar ya shiga cikin layin mu har lokacin ban motsa ba.Horn yayi a bakin get kimanin wucewar mintuna uku, sannan ya tsayar da motar banyi motsin kirki ba balle in samu ƙarfin gwiwar fita daga motar. Inaji ya buɗe motar ya fita ba tareda yace dani ƙala ba, nima banyi gigin dakatar dashi ba don banga dalilina nayin hakan ba.
Murɗe kujerar motar nayi ta yanda zanji daɗin jingina kamar yanda nake buƙata, na jima ina tufka da warwara a ƙalla sai da na shafe mintuna shabiyar sannan na buɗe motar na fita. Cikin rashin guzari nake tafiya tamkar wadda na shekara ina jinya, komai na rayuwata yanzu baya min daɗi kamar yanda na baiyana a baya. A haka na isa jikin ƙofar falon zuciyata cike taf da tarin fargabar abinda zan tarar, tura ƙofar nayi daga can ƙasan maƙoshina nayi sallama. Abin takaici yanda nabar falon na tafi Asibiti ba haka na dawo na sameshi ba, kamar zan kurma ihu haka na dinga bin pillows ɗin da aka baza a tsakar falon da kallo.
ajiyar zuciya na sauke mai zurfin sosai ina jin yanda takaicin abin ke ƙara mamayata. Daga can ƙasan ruhina na ce,"ya ubangiji ka ƙaramin haƙuri akan duk abinda zan gani na ɓacin rai a cikin gidanan, sannan ka nuna min ranar da zanji daɗin zama a ɗakin mijina kamar yanda sauran mata sukeji a ɗakunansu." nayi adɗu'ar cikin gajeran sautin da babu me iya jina.
Takun takalman da naji sautinsu na fitowa daga hanyar kicin ɗina ce, tasa na juya da hanzari ina kallon Direction ɗin gurin. bisa ga mamakina Faridah Attahiru ce hannunta ɗauke da soyayyen ƙwai cikin faranti, kamar yanda nai kasaƙe ina kallonta itama ido ta zuba min tana kallona. Kimanin gushewar mintuna uku sannan na sauke idanuna ƙasa don bansan abinda ya kamata ince da ita ba.
Ɗan gajeran murmushi ta saki wanda sautinsa ya kutsa cikin kunnena sannan ta ce,"kin daɗe sosai a inda kikaje Bilkisu. Nayi zaton a can inda kika kai ziyarar zaki kwana."ta firta hakan tana ƙara tsareni da manyan idanunta, waƴanda babu komai a cikinsu face tsantsar fitsara da rashin kunya.
Kasa amsa mata nayi don bansan abinda ya kamata ince mata ba, a nitse na lumshe idanuna sannan na ƙara buɗesu tar akanta na ce,"idan zaki soya ƙwai don Allah ki dena soyawa a nan. Ƙamshinsa yana ɗaga min hankali sosai." nayi maganar a sanyaye tamkar ba daga tsakanin laɓɓana ta ratso ta fito ba.
Tsareni tayi da ido cikin tsananin mamakin jin abinda na firta, amma da yake ƴar duniyace sai ta gaggauta shanye mamakinta ta ce,"masu baiwar ɗuwawun haihuwa su ya kamata su firta haka a martaba maganarsu. ba juya irinki ba wadda baki iya ubn komai ba sai dai kici kiyi kashi, ina ganin zaifi miki alkhairi ki tanadi hujjar da zaki gamsar da Hajiya akan fitar da kikayi." ta firta hakan tana jifana da kallon ƙasƙanci, wanda yasa naji a zuciyata na muzanta ainun.
Zuciyata ce tai wata irin motsawa wadda tasa allon ƙirjina ya fara barazanar darewa gida biyu, cikin wani irin yanayi mai narka zuciya na sauke mata rinannun idanuna cikin nata, cikin yanayi irin na zallar kaɗuwa. duk yanda naso na daure a wannan taƙin juriyata sai da ta raunata ainun, sai kawai na samu kaina da yin murmushi wanda ya taimaka wajen baiyana halinda zuciyata ke ciki. Kasa cewa komai nayi na daure na danne zuciyata gudun kar in rusa ribar haƙurina ta hanyar biyewa Shirman Faridah Attahiru!
YOU ARE READING
RA'AYIN ZUCI... THE OPINION OF THE HEART
FantasyRayuwar ko wani dan-adam a duniya tana gogaiya ne da irin tasa qaddarar. a gareni ma hakanne ya kasance lokacin da sanadi ya kaini makarantar kwana, tafiyata jihar Bauchi shine ya zama shafin farko a littafin tawa Ƙaddarar. daga ganin farko da muka...