7-8 Neman kuɗi

20 3 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/GR6qeSui32A1rvwaBywJyK

whatsapp group👆👆

*HAFSATUL-KIRAM*

©Mai Ƙosai

Babi Na Bakwai Da Na Takwas

Wani yawu ta haɗiye dunƙulalle da ƙyar, kafin ta sake kai kallonta kan fuskar yarinyar.

"Ki faɗa min babu wanda zai kashe ki ina tare da ke, kar ki ji shakka ko tsoro kin ji"

Cikin rawar murya, da wani irin amo maras daɗin ji ta soma magana,
"Mamana kullum sai ta dake ni, saboda wai bana kawo mata kuɗaɗe da yawa. Ni kuma bana son tallan da take ɗora min, na sha gaya mata karatu nake so irin yadda su Hansa'u suke yi, bata ba ni abinci sai na yi mata ciniki sosai. Na faɗa mata barazanar da nake fuskanta ta ce min ba komai ba ne indai a har neman kuɗi ne mutunci ba abu ne da za a duba kyautuwarsa ba. Kalamanta da son cika muradinta suka samu gurbi a zuciyata, sai na soma nema mata kuɗi afujajan ko ta halin ƙaƙa, sai dai duk da haka duk yadda na so samu bana samu domin duk wanda zan tunkura sai ya nemi mutyncina ni kuma ba zan iya bayarwa ba, shi ne ta ce min wajen nema ko a yaƙeka ko ka yaƙe wanda kake neman tare da shi, wato dai ko na siyar da mutuncina ko kuma na kawo ƙarshen wanda zan samu kuɗin idan ya so saurannaiki ya rage gareni, bani da wani zaɓi dole na fara sakarwa maza gangar jikina tun da burinta da farincikinta na kawo mata kuɗi, garin haka ne wani ya so keta min haddina akan na ba shi jikina ya bani kuɗi, na ƙi na je na sanar da mama, amma sai ta ce idan irin haka ta faru ban bi ƙudurinsu ba na dawo mata sai ta nakasta ni, kuma ko da wasa kar ta kuskura ta ji maganar nan abakin kowa idan ba haka na lahira sai ya fi ni jindaɗi, ta ci gaba da gargaɗina akan na yi duk mai yiwuwa na na nemar mata kuɗi ko ta haɗin ƙaƙa, ta yi alƙawari duk wanda na gayawa labarina sai ta kashe ni na bar duniyar."

Ji ta yi kalaman yarinyar kowace gaɓa na hawar mata kai, kanta ya soma jujjuyawa.

'Wace irin uwace wannan da za ta ɗora 'yarta kan gurɓatacciyar hanya?' ta yi wa kanta tambayar cikin zuciyarta.

"Ke nan bakya zuwa kowace makaranta?"

"Tun tasowata ban san mene ne ilimi ba, ban san mece ce makaranta ba."

"Ina mahaifinki yake?"

"Ban san shi ba, ban san kalarsa ba."

"Ya salam!" Ta yi maganar tana dafe kanta. Ba ta sake tankawa ba ta miƙe ta bar ɗakin, zuciyarta na suya. A ɗakinta ta dira, kan sofa ta zauna tana jin magamganun yarinyar na sake jujjuyawa a kwanyarta.

"Aunty!" Muryar Afna ta daki kunnenta.

Jiki a sanyaye Afna ta samu waje ta zauna sharaf, tana mai ajjiye jakarta gefe kafin ta saki wani marayan kuka.

Da ido Hafsa ke bin ta da kallo, jin kukan na hawar mata kai ya sata magana,

"Kin san bana son kuka Afna, me ya sa kike son takura min da yawa? Mece ce damuwarki?"

"Aunty bazan sake zuwa makarantar nan ba, ki sauya min wata."

"Me? Kin san kuwa me kike faɗa? Du-du shekaru nawa ne suka rage miki, me ya faru ki sanar da ni bana son damuwa."

"Wani ne yake takura min bana so aunty na gaya masa bana so amma yaƙi ya daina."

Da sauri Hafsa ta miƙe ta isa inda Afna ke zaune tana sillar da ruwan hawaye, hannunta ta kamo da ƙarfi kafin ta ce,

"Ki yi min bayani dalla-dalla yadda zan fahimta, kada ki ƙara haukatar da ni Afna."

"Wani sabon ɗalibi aka kawo SS3 shi ne yake takura min, kullum sai ya zo inda nake ya yi ta taɓa ni, wai dole sai mun yi soyayya na gaya masa ni ba soyayya aka turo ni yi ba shi ne ya ce to na ba shi abin da zai sanyaya zuciyarsa, da na bijire masa shi ne ya rufe ni a aji bayan an fita break yaso keta min haddina aunty, ta karfin tsiya ya cire min rigata ya cire min siket ɗina, su Nasma ne suka je suka sanar da shugaban makaranta amma da yazo sai ya goya masa baya saboda ya faɗa masa ƙarya da gaskiya, kuma da man ance baya laifi a wajen shugaban makarantar, shi ne ya ce wai ai laifina ne don haka kar ya ji maganar a ko'ina."

HAFSATUL-KIRAMWhere stories live. Discover now