71-72 Dija

6 1 0
                                    

HAFSATUL-KIRAM

   ©Mai kosai

             FCW

Babi Na 71-72

Kwana biyu ya rage su shiga kotu, a wanan lokacin an kirata da lambobi mabambanta ana yi mata barazana haɗi da kashedi ta janye karar, yayin da ita kuwa ji take tamkar sake ingizata suke yi.

Wani aiki ne ya tasowa yaya Lawan a Mina, tafiyar da babu shiri suka yita. Yaso ya gana da Hafsa ya yi mata sallama, ya kuma ajjiye mata sakon da za ta ji tana kaɗaicinsa.

Gefe guda barista Jahid na ta fafutuka wajen ganin ya samo bayanan da take so, sai dai ko kusa ko alama bai ci karo da abin da yake son samu ba.

Nisha ce ta shigo ɗakin, inda ta iske Hafsan kwance idanuwanta na kallon rufin ɗakin.

    "Yaya dai, duk shari'arce ko kuma tunanin yadda zata kaya ne?"

   "Hmm! Wallahi ke dai bari Nisha, wani abu ne yake damuna na rasa yadda zan yi in cire shi daga cikin zuciyata."

   "Uhmm! Ina jinki mene ne wannan al'amarin?"

   "Nisha ina son yaya Lawan, ina jin babu wani namiji da zan iya rayuwa da shi idan ba shi ba, amma gubar da ya zuba min ita ta ke hanani ganin duk wani farinsa. Tana sakawa ina jin ba zan iya gafarta masa ba."

  "Hmm! Hafsa ke nan. Ina da tabbaci kin san cewa Allah muna yi masa abubuwa da dama kuma idan muka nemi afuwarsa sai ya gafarta mata. Me ya sa ba za ki watsar da komai ba? Me ya sa ba za ki rungumesɓ shi hannu bibbiyu ki kyautata masa ki faranta masa matsayinsa na miji gareki ba. Na tabbata watarana zuciyar nan taki zata canza shi daga bakin da take gani zuwa fari, ke za ki lankwasata karki kuskura ki bari ta zama jagorarki. Ko bakyaso kaka ta yi alfahari da ke ranar gobe alkiyama?"

   "Ba haka ba ne Nisha, ina son cikawa kaka kudurinta, ina son faranta mata rai na kasa na kasa Nisha ki faɗa min me zan yi?"

   "Ki yi kokari mayar da komai ba komai shi ne abin da za ki yi Hafsa."

    "Ta yaya?"

" Ta hanyoyi da dama, da kike da damarsu. Na tabbata yaushe rabonki da ki kira yaya a waya ki ji lafiyarsa?"

   Kwaɓe fuska ta yi kafin ta ce,

   "Shi ma ai bai taɓa kirana ba."

  "A'a Hafsa ko da ace jikina kunnuwa ne ba za su gamsu da abin da kike faɗa min ba, babu yadda za ayi yaya ya kasa kiranki sai dai kawai ki ce baki ga kiran ba, ko kuma kin gani amma bakya jin za ki iya amsawa. N zauna da yaya tsawon wasu watanni, na ga haɗin da ya shiga sanadiyar kaunar da yake yi miki, har ina addu'a akan Allah ya bani miji kwatankwacinsa ko ma fiye da shi, domin yana da ɗabi'u masu kyau, sannan yana sonki fiye da tunaninki. Wallahi Hafsa kar ki bari shaiɗan ya yi tasiri a zuciyarki ya rabaki da yaya Lawan domin za ki yi babbar asara."

Shiru ta yi, ta san gaskiya Nisha take gaya mata, sau tari takan rasa dalilin da yasa take son take gaskiyar da suke son nusar da ita.

  "Shi ke nan zan gyara in sha Allahu zan gyara tsakanina da yaya."

   "Yauwa ko kefa"

Nisha ta ɗan numfasa kafin ta ce,

   "Af na manta abin da ya kawo ni ma, jahid ne ya kirani wai Dija na asibiti haihuwa, ya ce ya kira wayarki baki daga ba."

  Murmushj ta saki, haɗi da mikewa ta sakko daga kan gadon tana faɗin,

   "Shirya mu tafi yanzu, ai zama bai kama mu ba. Wai wayaga su Dija an zama mama." Ta karasa maganar tana sakin dariya.

   "Aikuwa dai kam, kafin kuma ke ma ki zama ba. Ni fa wallahi so nake ki yi ki gyara abin da za ki gyara kafin dawowarsa yadda za a sama mana baby boy ko girl."

Wani duka ta kai mata, ta yi hanzarin kaucewa tana dariya.

Ba su nufi asibitu ba sai da suka shiga wajen inna suka shaida mata, tare da nemawa Dija addu'arta.

HAFSATUL-KIRAMWhere stories live. Discover now