45-46 Zaman kotu

19 2 0
                                    

HAFSATUL-KIRAM

©Mai ƙosai

    FCW

Babi Na 45-46

  "Sunana Tajuddin Aikawa."
"Ko ka san wannan mutumin?" Na yi maganar ina nuna masa Mahrazu.
"Ƙwarai na san shi, maƙocina ne."
  "Ma sha Allah" Ko za ka iya fayyace mana yadda mu'amalarku take da shi."
"Gaskiya babu kyakkyawar alaƙa, saboda baya son hulɗa da mu 'yan unguwa. Ko a hanya muka gan shi muka yi nufin gaisawa da shi sai ya kauce ya haɗe fuska, wannan ta sa duk muka ja baya da shi. Matarsa ce kaɗai matanmu suka soma mutunci da ita, ƙarshe ita ma sai ya hanasu hulɗa."
"Ka tabbata"
  "Ƙwarai 'yar nan."
"Na gode, za ka iya komawa."
Na matsa kusa da Mahrazu na soma magana,
"Zan so ka sanarwa da kotu sunanka da matsayin aikinka."
"Suna na Mahrazu Yusif, ni ɗan kasuwa ne ba ma'aikaci ba."
"Mene ne matsayin Bahijja Hassanu a gareka?"
"Mata ta ce."
"Ko za ka iya gayawa kotu  shekarun aurenku nawa, da yadda zamantakewarku take tsawon shekarun?"
"Shekarar mu huɗu da aure, muna zaune lafiya, domin tana kyautata mini, tare da yi mini biyayya saboda ita mace ce mai yawan haƙuri."
"Wannan ya sa ka yi amfani da irin haƙurinta kake cutar da ita ke nan?"
"Objection ya mai shari'a! Bai kamata mai tambaya ta shigar da magana cikin bakin wanda ake tuhuma ba."
  "Barisa Hafsa a kiyaye." Alƙali ya ce.
Na ranƙwafa, kana na ce,
"Ina so kotu ta yi mini izini na gabatar da Dr. Khadija Ibrahim a matsayin hujjata ta biyu."
"Kotu na son ganin Dr. Khadija Ibrahim a gabanta."
Dija ta fito, ta tsaya.
   "Za mu so jin sunanki, da matsayin aikinki."
"Suna na Dr. Khadija Ibrahim, ni cikakkiyar likita ce wacce ke aiki a asibitin gwamanati.
"Kin san wannan" Na yi mata nuni da Bahijja.
"E, na santa. Mara lafiyana ce. Ta zo mini kwanaki uku da suka wuce, akan tana so ta zubar da cikin jikinta na wata huɗu, sai na nemi jin ba'asi, shi ne take ce mini bata son ta haihu ne saboda tausayin halin da yaran zai shiga saboda mijinta baya sonta, kullum cikin dukan ta yake yi. Lokacin ina tare da 'yaruwata barista Hafsa wato ke, sai muka yanke shawara muje gidanta mu taushi mijin bayan itama mun taushe ta. Mun je mun yi magana da shi, har muka ce za mu dawo, amma a daren sai ta sake riskar kanta cikin wani yanayi wanda sai da muka kai ta asibiti, dalilin kiran 'yaruwata da ta yi a wayar da ta bata, munje gidanta saboda mun ji kamar tana cikin hatsari sai muka iske ta a sume ga jini na zuba. Ko da na yi bincike sai na ga cikin ne ya fita, duk da bai fita duka ba sai da aka yi mata MVA(wankin ciki) mun kuma gano ta sami rauni a mahaifarta,  har sai an ɗorata a kan magunguna, wanda idan ba haka ba da wuya ciki ya sake zama a cikin mahaifar."

"Na gode Dr. Khadija, za ki iya komawa." Na ce da ita.

    "Ya mai girma mai shari'a wannan takarda ce da ke nuna gaskiyar binciken da likita khadija ta yi." Na yi maganar ina miƙa takardar.

Alƙali ya karɓi takardar ya duba, ya yi rubutu.

"Idan kotu ta sake ba ni dama, ina so zan gabatar da hujjata ta ƙarshe."

"Kotu na saurarenki."

Na zaro wayata, na shiga ɓangaren rikodin(recording) na taɓa wata ɗauka, na miƙawa alƙali na ce,
"Ina so mai girma mai shari'a ya saurari wannan ɗaukar sautin ta yadda za a tabbatar da duk hujjata gaskiya ce."

Alƙali ya kunna ɗaukar, take muryar Mahrazu ta fito raɗau cikin rikodin ɗin da na yi masa lokacin da muka kai masa takardar sammaci, yana kumfar baki da cika baki.

"E, an daketa. An yi mata lahanin sai me? Matarki ce ko tawa? Ba kotu ba koma ina ne ki kai ni, babu wanda ya isa ya sa na sake ta."

Kotu ta yi tsit tana saurara har ɗaukar tazo ƙarshe. Take gumi ya hau wanke fuskar Maharazu, ya soma firfita da hular kansa da ya cire.

"Da wannan nake so kotu mai albarka, ta samarwa da Bahijja haƙƙinta, ta kuma hukunta Mahrazu akan laifin da ya aikata na uƙubanta Bahijja har ya yi mata silar haifar mata da matsala, na gode."
Na koma na zauna.

"Wallahi sharrin shaiɗan ne, kuskure ne. Ina son matata don Allah karku raba ni da ita. Bahijja ki yafe mini, na tuba." Ya yi maganar yana sharce zufar saman goshinsa.
  "Barista Hafiz ko kana da ja?" Alƙali ya ce.
  "A'a ya mai shari'a" Barista Hafiz ya ce.
Alƙali ya sunkuya ya yi rubutu, kana ya ɗago ya dubi jama'a ya ce,
"Kotu za ta je hutun rabin lokaci, kafin ta dawo tana shawartar Bahijja da ta sake tunani a kan son raba aurenta da take so ayi da mijinta Mahrazu."
Ya buga guduma, yana mai miƙewa tsaye.

Ko da muka fito, Bahijja ce ke rungemi da ni tana kukan ita fa ba ta son Mahrazu, da ƙyar na rarrasheta muka zauna kan wata kujera. Na kai dubana gareta, kafin na ce,
"Ki yi haƙuri Bahijja! Na san dole za ki ji ƙiyayyarsa cikin zuciyarki. Amma ki sani kashe auren ba shi ne mafita ba, domin burin kowace mace ta gari ta mutu gidan mijinta. Kuma na hango soyayyarki cikin idanuwansa tabbas yana sonki kawai dai son zuciya ya saka shi aikata haka, ki daure ki sake ba shi dama."
"Amma haka zai zauna ya ci bulus ke nan? Idan har na yafe masa hakan yana nufin zai iya sauyawa ya dawo yadda yake?" Ta jefo mini 'yan tagwayen tambayoyi.
"Bai ci ba, za ki nemi kotu da ta nema miki haƙƙinki, sannan yafe masan da za ki yi za ki iya sawa ya sauya fiye da yadda ba kya tsamani. Don Allah karki kashe aurenki, na tabbata iyayenki ba zasu ji daɗi ba."
"To ki sa a bi mini haƙƙin zalunta ta da ya yi." Ta yi maganar tana goge ruwan hawayen da ke shimfiɗe saman ƙunduguginta.
"Ke za ki nema." Abin da na ce da ita kawai. Haka muka cinye lokacin har aka koma cikin kotu.
Alƙali ya yi rubutu, bayan ya zauna ya ce,
  "Muna so kotu ta ji hukuncin da Bahijja ta yanke?"
        "A da na yanke hukuncin ƙin zama da shi, amma a yanzu na yafe masa. Sai dai ina so kotu ta bi mini haƙƙina a kan abubuwan da ya aikata mini." Cewar Bahijja. Yayin da shi kuma Mahrazu fuskarsa ta cika da maɗaukakin mamaki da farin ciki.
"Duba da yadda aka gabatar da hujjoji, da kuma yadda mai laifi ya yi nufar amsar laifinsa da bakinsa. Da kuma yadda Bahijja ta yi iƙirarin a bi mata kadinta, wannan kotu ta yanke hukunci a kan lallai Mahrazu ya biya Bahijja duk abin da ta kashe na hidimar kanta, sannan ya biyata tarar naira dubu ɗari."
Alƙali ya buga guduma, yana miƙewa tsaye. Nan kotu ta ta tashi.
Bahijja ta yo kaina, tare da rungume ni tana kukan farin ciki, da yi mini godiya. Ni kam wani daɗi nake ji yadda na tsaya na ƙwato mata 'yancinta.
Tun daga wannan rana, na sake zage damtse wajen tsayawa mata kan matsalolin su. Na buɗe ofishi na kaina, tare da ɗaukar ƙwararrun lauyoyi don mu haɗu mu samar da tsanin gaskiya, mu wanzar da ita a bigirenta.
A nan ne kuma na haɗu da Barista Mujahid, wanda ya nace mini da son na amince da soyayyarsa. Ni kuma na ri ga na ci alwashin ba zan yi aure ba sai na cika muradina, na son buɗe gidan marayu.
Yaya Lawan, shi ya taimaka mini sosai, ya tsaya kai da fata na samar da gidan marayu kamar yadda nake buri. Ya sa na zama 'yantacciya, ya sake mayar da ni ƙwararriya kuma jajirtacciyar lauya wacca al'umma ke alfahari da ita. Ban san da mene ne zan iya biyansa ba. Ban sani ba aurensa da yake kwaɗayin na yi ne zai sa na biya shi da alkairan da ya yi mini ko kuwa? Ko kuma wani al'amari ne daban da zai sa na biya shi da shi? Koma dai mene ne ina fata ya zama silar sanya shi cikin farin cikin da ba zai mance da ni ba, zan jira lokaci komai tsayinsa, zan jira, zan kuma yi tsumayin jiran abin da zan saka mi shi da shi ya sanya shi irin farin cikin da ya san ya ni ma.

Gyara ko sharhi ƙofa a buɗe take, 08130266650 whtsapp only

Mai ƙosai

HAFSATUL-KIRAMWhere stories live. Discover now