33-34 Gwaggwon Biri

18 2 0
                                    

*HAFSATUL-KIRAM*

©Mai ƙosai

  FCW

Babi Na 33-34

Sauke ajjiyar zuciya na yi daidai lokacin da ya dire zancensa, abu ɗaya ne ya tsoratar da ni cikin maganar shi cewar lafiyar ɗana ko 'yata za ta iya taɓuwa, amma bacin wannan duk abin da ya lissafo ko a ƙasan silifas ɗina.
       Ina cikin wannan saƙe-saƙen ne aka turo ƙofar ɗakin da nake ciki. Mu duka har likitan muka bi sawon ƙofar da kallo, idanuwana suka sauka kan fuskar yaya Lawan da ya yi shigar ƙananun kaya wanda suka sake fito masa da tsantsar kyawunsa. Sai dai gubar gabar da ke tsakanina da shi ta yi saurin yin tasirin sarrafa mini shi izuwa ga muguwar mummunar halittar da ta zarta ta gwaggwon Biri.
     Ya soma magana da likita cikin harshen turanci yana mai tambayar shi yaya lafiyar tawa take?
Nan likitan ya shiga kora masa bayani kamar yadda ya mini.
     Sosai na ga ya shiga cikin tsananin tashin hankali da damuwa, ni kam cikin zuciyata faɗi nake,
     'Aikin banza, jefa agwagwa a ruwa! Nuna tausayawarka gareni, da shiga cikin tashin hankalinka ba zai taɓa tasiri cikin zuciyata ba balle har na ji ina mai tausayawa rayuwarka.'
        Ya ciro wani kati da ke gaban rigarsa ya miƙawa gandorobar da ke tsaye kanmu, ta amsa tana mai karantawa kafin ta ba shi izinin ganawa da ni.
           Ya ƙaraso inda nake da azamarsa yana mai ƙoƙarin cafko hannuna, na yi saurin janye hannun na haɗe fuskata tamkar ban taɓa sanin mece ce fara'a ba.
Cikin wata iriyar murya ya ce,
   "Me ya sa haka Hafsa? Ni fa jininki ne, kuma mai burin zama mijinki a..."
Na soma bin shi da wani gafalallen kallon mahaukacin banzan da ya yi sanadin tsinkewar kalamansa. A hasale na ce,
  "Kai ka ga na yi maka kama da wacca za ta aureka, ka zama mijinta? To bari ka ji, kai ka yi kaɗan ka mallake ni domin ni kurwata ta babban ƙasurgurmin maye ce, wallahi idan baka fita na dai na ganin wannan mummunar halittar taka ba da gwara na yi ta kallon tsaka a kanta ba, sai na ruguza maka kai yanzu ba sai anjima ba."
Nan ya soma fitar da wani huci sai ka ce kububuwa, amma ya gaza ce mini komai sai ni ce ma na sake furta,
      "Daga yau, daga rana mai kama da ta yau kada ka kuskura ka sake nuna min kalarka a gabana, ka bar ni na yi rayuwata ni kaɗai kamar yadda na ke yi."
     "Ba zan taɓa barinki ba HafsaI! Tabbas na yarda ni ɗin mahaukaci ne amma mahaukaci akan ki, kuma na ci alwashin sai na komar da ke gida, ko da kuwa gangar jikinki ce." Ya faɗa a zafafe.
   Ina shirin yin magana likita ya dakatar da ni ta hanyar yi mini izini da na yi shiru, yayin da ya nemi yaya Lawan da yabar ɗakin domin na samu na huta.

     Tun zuwan yaya Lawan na ji zaman asibitin gaba ɗaya ya gundure ni. Na shiga fafutuka da ƙoƙarin ganin na tsere daga asibitin, sai na gaza samun mafita. Tilasta wa kwanyata tunani, ya haddasa mini wani nauyayyen ciwon kai, ina hawaye bacci ya yi awon gaba da ni.
         Wajen yamma na farka da wata muguwar yunwa, sai dai sam na ji lokacin bana buƙatar cin komai, ni dai kawai burina na bar asibitin koma ta halin ƙaƙa ne.
      'Ba fa za ki bar asibitin nan ba ta halin nuna gardamarki'   Wani sa shi na zuciyata ya ankarar da ni haka.
      'To me ya kamata na yi?' Na tambayi kaina. Na lumshe idanuwana cikin tsanaki da san bawa ƙwaƙwalwata damar da za ta iya lissafo mini hanyoyin da zan bi don barin cikin asibitin. Sai dai ayyana mini take yi kawai dabara ta rage tawa, kamar yadda mai buɗe kwangin zuma ke nemanta.
     Lumshe idanuwana na yi, wanda take wani majigi ya shiga haska mini wata rayuwa da na yi da baba, wacca ta sake taso mini da tsanar inna.
     
   Da guduna na shiga cikin gidanmu, jin cewar baba ya dawo daga cikin gari ta bakin baba Iro. Na iske shi zaune jingine jikin bango ya haɗa kai da guiwa, har na isa gare shi bai farga ba, sai da na saka hannayena biyu na tallafo kansa tare da ɗago shi.
     Idanuwansa sun yi ja sosai kamar an zuba musu garwashi.
     "Babana me ke faruwa?"
Ya yi murmushin ƙarfin hali, fuskarsa a dame tamkar damammiyar fura kana ya furta,
     "Babu komai Hafsana!"
        "Ta yaya za ka ce mini babu komai baba, bayan na hango damuwa cikin ƙwayar idanunka?"
Ya ɗan kurmusa kaɗan, kana ya ce,
      "Babu komai Hafsana! Ke dai ki ci gaba da haƙuri da wannan rayuwar. A kuma duk lokacin da kika tsinci kanki cikin uƙubar rayuwa kada ki manta da ambaton Allah, domin shi ne mai yaye dukkan wata damuwa da take nuƙurƙusar kowane bawa, ki zama mai juriya, da haƙuri domin wata rana za ki iya tsintar kanki a inda babu ni sai ke kaɗai, cikin rayuwar da babu wanda zai iya taimakonki sai Allah, cikin rayuwar da baki da kowane irin gata sai na Allah."
      Na kamo hannunsa ina hawaye na ce,
   "A'a babana, ka dai na yi mini zancen rabuwa da kai, da kai na saba, da kai nake rayuwata, dukkan tsanani yana tare da sauƙi baba, tare za mu mutu, tare za mu tafi duk inda za ka."
Baba ya ɗan murmusa kana ya ce,
   "Ina so ki sani cewa duk yadda na so mu yi rayuwa tare da ke tabbas mutuwa za ta raba mu, kada ki manta Allah yana faɗa cikin suratul-Nisa'i aya ta 78, inda yake cewa: "Duk inda ku ka kasance mutuwa za ta riskeku, ko da kun kasance a cikin ganuwoyi ingantattu..."
   Shigowar Inna cikin ɗakin, cike da hargagi, da hargowa ya katse baba.
      "To magulmata! Masu tuƙa tuwo da allura, na rantse da buwayar Allah ni ce nan ajalinka sai dai idan ba na raye." Ta yi furucin, tare da ficewa a fusace.
     "Babana da gaske za ta iya kashe ka?" Na tura masa tambayar a ba zata.
     Ya shiga girgiza mini kai tamkar ƙadangare, da san kawar da kalamanta daga gareni cikin kwanyar kaina.
      "Ko kaɗan, ɓacin rai ne kawai Hafsana! Ɓacin rai ne ya sakata furta haka. Ta yaya za ta kashe mijinta uba ga 'yarta guda ? Ko da a ce na mutu ajalina ne ya yi amma ba ita ce sila ba."
Na hau girgiza kaina ina son tare ruwan hawayen da suke san sakko mini saman kuncina kana na ce,
      "A'a Babana! Ba zan taɓa lamunta ba, muddin na wayi gari babu kai, sai na yi shari'a da ita."
      "Hafsana!" Ya faɗa da ƙarfin gaske, cike da kakkausar murya. Kafin ya ɗora,
      "Kada na ji, kada kuma na gani! Ban lamunce ba, sam ban yarje miki shari'a da mahaifiyarki ba, ko kin manta ne ita ce silar samuwarki, ita ce ta kawo ki duniyar da kike shaƙar iska har kike jin daɗinta? Kul! Ba na so sam."
Ban ce masa ƙala ba, na cakumi hannunsa na cusa cikin nawa ina mai ambaliyar da ruwan hawaye tamkar an buɗe famfo.

       "Daman kin yi furucin Inna, ga shi kin kashe shi kin ji daɗi kin huta." Na yi maganar bayan na buɗe maganaina.
      "Inna kin tozarta ni, kin tozarta rayuwar 'yarki da kanki, kin raba ni da farin cikin raina, kin sanya mini hijabi mafi muni ga jin daɗin rayuwata, me na aikata miki haka? Wace irin ƙiyayya ce haka kike yi mini? An ya ni jinin ki ce kuwa?"
     Na rushe da matsanancin kuka ina mai yin matokari da kaina da jikin ƙarfen fuskar gadon da nake kai, wanda haka ya sake raunana raunanniyar zuciyata da ke kwance a ƙirjina.

   Kwana na ɗaya a asibitin aka yi mini sallama, na koma gidan kurkun da na fito. Ina zaune ina tunanin halin da abin da zan haifa zai riska.
     Gobe saura kwana uku hukuncin da aka yanke mini ya tabbata a kaina, duk da dai dole sai na haife abin da ke cikina, amma lokacin da likitoci suka ɗeba mini gobe ko jibi zan iya haihuwa.
    Na runtse idanuwana kaina ya shiga sara mini, lokaci guda kuma wata fargaba ta shigeni. Ƙirjina ya ci gaba da bugawa tamkar wacca ake yi wa kiɗan kalangu. Na soma jin ina ma ban gasgata abin da ake tuhumata da shi ba, to amma yaya na iya ba ni da wani zaɓi ne sai haka.
    "Idan na mutu za ki yi kewata kuwa hubby?"
      Wani bigire na ƙwaƙwalwata ya shiga tariyo mini da kalaman Nasir.
            "Zan yi kewarka har ta zautar da ni." Na tuna amsar da na ba shi.
     Yayin da ya ƙyalƙyale da dariya har yana riƙe ciki ya ce,
      "Ba zan so haka ba, amma ina so dai ki kula mini da abin da za ki haifa mana."
     Ya ƙarasa yana shafa saman fatar cikina.
     Ni kuma na sha mur alamar ba na san maganar da yake yi mini ko kaɗan.
       "Wai kai me ya sa baka da aiki sai maganar mutuwa.?"
     "Hmm! Ba za ki gane ba ne hubby, ita fa mutuwar nan dole ce ga kowace rai, ko Allah yana faɗa mana ma cikin suratul-Ankabut aya ta 57 inda yake cewa 'Ko wace rai mai ɗanɗanar mutuwa ce, sannan kuma za ku dawo izuwa gare mu.' Kin ga kuwa dole wata rana za ki wayi gari ba na raye, za ki mutu, zan mutu ko da muna so ko ba ma so, fatan mu dai mu yi kyakkyawan ƙarshe."
     Na yi murmushi kana na ce,
    "Haka ne! Amma ni dai ba na so kana yawan yi mini zancen ta sai na ji kamar tafiyar za ka yi ka barni ni ɗaya cike da kewarka. Kada ka manta Manzon Allah (S.A.W) yana faɗa mana cikin hadisin da aka karɓo daga Abu Hurairah in da yake cewa Manzon Allah(S.A.W) ya ce: Kada ɗayanku ya yi burin mutuwa kuma kada ya yi addu'ar mutuwa ta zo masa. Haƙiƙa idan ɗayanku ya mutu ayyukansa sun yanke. Ba abin da tsawon rayuwa yake ƙarawa mumini sai alheri. Muslim ne ya rawaito.' Ko ka manta da wannan hadisin ne?" Na faɗa ina kafe shi da idanuwana.
       "To malamata an gama, na daina faɗa"
        Ya faɗa yana mai shafa fuskata da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma ya shafa cikina da shi ya kai bakinsa saman cikin ya sumbace shi ya yi murmushi ba tare da ya ce mini komai ba.
       Na kife kaina kan guiwata, hawaye masu ɗumi na sake gangarowa kan dandamalin fuskata. Sabo turken wawa, ban taɓa sanin na yi sabo, da shaƙuwa da Nasir ba sai a yanzu da ba ya raye, me ya sa  za ka tafi ka barni cikin wannan yanayin? Don Allah ka dawo ka kwance ƙullin ɗaurin gwarmen da aka yi mini.
     Da dare, yayin da mafiya yawan fursononin gidan ke bacci, ni kuma Yalsha ta tasa ni a gaba, a kan lallai sai na bata labarina, da abin da ya sa ba na ƙaunar ta yi mini zancen mutumin da ya kawo mini ziyara.
Nan na shiga feɗe mata biri har wutsiyarsa. Kammala bata labarin na yi, wanda take na ji jikina ya ɗauki tsima  har izuwa lokacin da na ji marata na juyawa tamkar injin markaɗe na markaɗe kayan miya, da lokacin da na silale ƙasa, yana ta rufe maganaina.

Ƙofar gyara da sharhi a buɗe take.
    
    08130266650 whtsapp only

Mai ƙosai

HAFSATUL-KIRAMWhere stories live. Discover now