77-78 Farin ciki

8 1 0
                                    

HAFSATUL-KIRAM

  ©Mai kosai

      FCW

Babi Na 77-78

Yau kwana biyar da bacewar su Hafsa, wanda an gaza gano inda suke. Su kuwa suna can yayin da Hafsa ke fuskantar barazanar mutuwa muddin ba ta janye karar da ta shigar ba, wannan ya sa ta fahimci ba garguwa aka yi da su ba shiryayyen shiri ne da aka shirya musu, fatanta Allah kar ya sa su cutar da Nisha wacce bata ji ba, ba ta gani ba, wacce ba ta da hannu ko kaɗan cikin al'amarin.

Tana zaune ta yi zugum, wanda yanzu sallar ma ba sa barinta ta yi, sai barazana da kuma yu mata wasu kananun cutarwa.

Turo kofar aka yi wacce ta bawa hasken da ke waje damar haska ɗakin da take ciki, wani gajeran mutumi ne ya shigo ya sha jar jaddara, fuskarsa sanye da bakin glass irin na no respect ɗin nan, kujerar da aka ajjiye masa ita ya ja ya zauna yana kallon fuskar Hafsa da ta faɗa, leɓenta kuma duk ya bushe saboda kishi na ruwa.

Wata arniyar dariya ya bushe da ita, sai da ya gama tsula iskancinsa sannan ya haɗe fuska tamkar wanda aka yi wa bushara da mutuwa, cikin gadara da izgilanci ya ce,

   "Yaro bai san wuta ba sai ya taka. Ke a tunaninki zamu barki ki ci galaba akanmu? Shi ya sa tun farko muka dinga gargaɗinki da ki janye karar amma ke ga mai taurin kai ko? To bari ki ji zamu iya kasheki kuma mun kashe banza, zamu batar da ke yadda danginki zasu gaji da nemanki har su hakura kin ga ita kuma maganar kara babu ita, tun dole sai da wacce ta shigar za ayi. Yanzu zabi ya rage gareki ko rayuwarki ko mutuwarki?" Ya karasa yana bushewa da dariya.

Murmushin gefen baki ta yi, kafin ta kalli cikin idanuwansa wanda ya cire bakin tabarau ɗin da ke manne saman fuskarsa.

  "Duk wanda ka ga ana yaƙi ya janye to rago ne, ni kuwa ba ragowa ba ce dangina kaf babu rago don haka sai inda karfina ya kare, idan kana tunanin hakan da kuka yi zai sa karar ta mutu to kunyi kuskure domin ni bani ce boss ɗin ba mataimakiyarsa ce, don haka shege ka fasa tsakanin ni da ku."

  "Haka kika ce"

Ta ɗauke fuskarta tare da bawa iskar wajen ajjiyar zantukan kalamansa.

A fusace ya mike, ya kalli wani shirgegen kato dake tsaye kansu, kana ya ce,

   "Kada ku kuskura ku raga mata, kai idan ta kama ku ci mutuncinta ina nufin dukanku ku yi mata fyaɗe ku illata mata rayuwa sannan ku ɗau video ɗin ku watsa a kowace kafar yaɗa labarai, daga karshe ku yi mata yankan rago." yana faɗin haka ya fice da sauri, inda katon ya take masa baya.

Jikin yaya lawan ya warware sosai, don a yanzu babu abin da baya iya yi da hannunsa. Nan fa ya tashi hankalin duka mutan gidan akan lallai sai sun sanar da shi inda Hafsa ta tafi da baya ganinta. Ba dan ransu yaso ba suka shiga feɗe masa biri har wutsiyarsa, nan da nan hankalinsa ya kai kololuwar tashi, ya dinga faɗa akan ta yaya za a boye masa wannan al'amarin.

Babu shiri ya kira wajen aikinsu tare da sanar da su abin da ke faruwa da kuma neman taimakonsu kan al'amarin. Sanan za a iya bibiyar layinsu a ga inda ya kai magaryar tukewa ya sa yaya lawan bayar da umarni akan a bibiyi layin, nan a ka gano karshen matsayarsa kan titin jigawa.

    "Jigawa" yaya lawan yayi ta maimaitawa da tunanin mai zai kaisu jigawa kuma?

Ita kuwa Hafsa cikin masu kawo mata abinci, ta yi nasarar zare wayar ɗaya daga cikinsu, da yake ta haddace lambar yaya lawan ya sa ta yi saurin aika masa da sakon kar-ta-kwana akan su bibiyi layin zasu same inda suke, kuma anyi garkuwa da ita ne saboda karar da ta shigar. Tana ji wanda ta sacewa wayar yana nema d bulayen wayarsa, ko da wasa ba su kawo cewa wayar na hannunta ba shiyasa ko tunkararta ba su yi.

A karo na biyu da bakin mutumin ya sake dawowa gareta ta naɗi duk wata muryarsa cikin wayar. Ta san duk abin da ya faɗa da man barazana ce, duk da tana tsoron shirun nasu, don har yanzu ko da wasa basu aikata ɗaya daga cikin abin da ya umarce su ba, abin da ta fi ganewa shi ne bukatarsu ta janye karar kawai ba wai kisa ba ko yi mata fyaɗen.

Nisha kuwa kullum cikin rokonsu take yi akan su sadata da yaruwarta, amma sun yi mata burus, karshe ma nuna mata suka yi zasu feɗe ta idan ta sake magana makamciyar haka, babu yadda zata yi haka ta zuge bakinta ta sanya mi shi kwaɗo, sai dai tana addu'ar Allah ya kubutar da su, ya kawo karshen zamansu a wannan dajin.

Tamkar a mafarki ta ta ji saukar karar bi digogi cikin kunnuwanta, abin da ya sanar da ita tabbas ana bata kashi kodai tsakanin waɗanda suka kamasu da yanuwansu ko kuma tsakaninsu da jami'an tsaro, bata gama nazarin ba aka banko kofar ɗakin da take ciki, nan aka fito da ita, sai a sanann ta yi ido huɗu da Hafsa ta rame ta yi duhu da ita tamkar ba ita ba. Da gudu ta rungumeta tana gawaye tare da tambayarta tana lafiya?

  "Lafiyata kalau Nisha, ki samu nutsuwa." cewar Hafsa tana shafa bayan Nisha.

Duk sai da aka tattare kartawan aka zuba su a mota, duk da a cikin musayar wutar da suka yi sai fa aka jarɓi wani a kirji wanda  take kuma ya shura.

Bayan sun samu nutauwa ne Abiey kw tambayarsu me zai kaisu jigawa, nan Nisha ta faɗa musu kudurin dake nashe cikin zuciyar Hafsa, sai ga shi su ba su je ba wannan iftila'in ya aukar musu. Nan ya yi ta musu faɗa akan ko nan gaba idan zasu wani waje su dinga sanarwa gudun irin haka.

Afna kuwa na manne da Hafsa, sai zuba santin murna ake yi.

Kwanansu uku da kuɓuta daga hannun waɗancen mutanen aka shiga kotu, inda hujjojin da ɓangaren su Hafsa suka bayyana ya sa alkali yanke hukunci da bai yiwa sauran daɗi ba, su kuwa kartawa da suka tsaresu da man shaharartun 'yan ta'addane waɗanda ake nemansu ruwa a jallo, a cikinsu wasu sunyi kisa, wasu kuma fyaɗe ne da sata, nan su ma aka yankewa kowannensu hukunci, hukunci da sam bai yi musu daɗi ba, asibitin kuwa tuni aka bayar da dikar a kulle shi, duk wasu masu laifi kotu ta jajjada da lallai a zartar musu da hukuncin da shari'a ta zartar musu, nan zaman ya kare zuciyoyin wasu farinciki zalla, yayin da wasu zukatansu ke a cukunshe bakikkirin tamkar tanderun da yaji wuta.

HAFSATUL-KIRAMWhere stories live. Discover now