47-48 Mummunan al'amari

22 2 0
                                    

HAFSATUL-KIRAM

©Mai ƙosai

Babi Na 47-48

Kallonta kawai Afna ke yi jin ta yi shiru a zancenta.

  Ɗan guntun murmushi Hafsa ta yi, tana sake jefa ƙwayar idanonta cikin ta Afna.
     "Me ya faru kike bi na da kallk tamkar wata tsohowar mayya?"

   "To ai na ji wani banbarakwai ne aunty, har yanzu ni kin saka ni a duhu me ya sa bakya ƙaunar uncle? Wane laifi ya aikata miki haka da zafi?"

    "Wannan ba huruminki ba ne Afna, labarina dai na baki kin kuma ji yadda gwagwarmayar rayuwata ta kasance ki je kawai."

   "A'a aunty don Allah ki sanar da ni me ya faru?"

Sauke numfashi ta yi, tana jin wani abu na tsikarar zuciyarta, bata son tuna komai ba kuma ta son wani ya ji sirrin sai dai ya zama dole a gareta ta sanarwa da Afna ko dan na cinta kamar wata kuturuwa.

  "Bayan sabon shafi na rayuwata ya buɗe na ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da walawala tamkar wani abu wai shi ƙunci bai taɓa taɓa zuciyata ba.

Burina a kodayaushe na faranta rayuwarsa sai dai ban samu nasara ba. Kwatsam na tsinci yaya a wani halin da ban taɓa tsammani ba, ko a mafarki ban taɓa kawowa zan ci karo da shi a hanyar al'amarin ba. Ranar da idanuwana suka gano min mummanan al'amarin ta kasance ranar bakwai ga watan yuli, na dawo daga wani taron wayar da mata da muka yi, na hangi motarsa a fake wajen ajjiye motoci hakan ya tabbatar min da cewa ya dawo yana gari, duba da yadda aikinsu ke kasancewa ba kodayaushe suke zaune a gari. Ciki da murna da farinciki na nufi sashensa, a hankali na tura ƙofar ɗakin turus na yi ganinsa kwance a ƙasa, gefensa kwalabene sosai kuma duk a buɗe suke da alama an sha abin da ke cikinsu, ban gama tantace ainihin hasashena ba hancina ya kwaso min warin giyar da ya cika ɗakin, nan take jikina ya mutu, a hankali nake ɗaga ƙafata har na isa inda yake kwance, na murgina shi take idanunsa suka faɗa cikin nawa.

   "Me ya sa yaya? Mene ribarka? Giya why?"

Na yi maganar ina ƙoƙarin ɗago shi, sai dai jin yadda ya riƙe hannu gam ya sa na soma bin sa da kallo, a yadda na fahimce gefensa ma kamar ba iya giya kaɗai ya sha ba, to mkwalaben mene ne kuma bayan na giyar? Ban samu amsar tambayata ba na ji ya janyoni jikinsa ya matseni gam-gam duk yadda na so ƙwacewa na gaza, ga shi a maye amma tabbas na gaza, take ya soma aika min da wau irin saƙonni, na soma fizgewa don san kaucewa abin da yake son yi, ji na yi kaina ya bugu da lokar gefen gado take na zube ƙasa jini ya soma tsiyayo min idanuna suka soma ganar min dishi-dishi ban san me ya sake faruwa ba sai farkawar da na yi na ganni kwance babu sutura jikina. Yaya lawan kwance gefena tamkar wani mushe yana sauke gwauron numfashi, motsin ne ya farkar da shi, take ya miƙe yana rarraba ido kamar ɗan shege, hannunsa ya miƙo da nufin taɓani na yi saurin janye jikina, sai a sannan wani kuka ya kufce min, na shiga rerashi tamkar babu gobe. Shi ke nan na rasa mutuncina, na rasa darajata da ƙimata ta ɗiya mace, me ya sa za ka kassara min rayuwata yaya? Na ƙarasa maganar cikin rauni da kuka.

  "Don Allah Hafsa ki saurareni, wallahi ba da nufi..."

   "Ya isa!" Na faɗa da wani irin amo.

   "Babu abin da za ka ce min, na tsaneka na tsani kallonka, kada ka sake haɗa numfashi da ni, kada ka sake nuna ka san fuskata."

Duk yadda ya so na saurare shi, na ƙeƙashi idona. Na miƙe ciki wani irin karsashi na fice daga ɗakin na nufi sashena, ban samu kowa ba na hakan ya sa na ji daɗi sosai nan na faɗa bayi na gyara jikina, ko da na fito ban iya aikata komai ba, domin zazzaɓi ne ta rufe ni sosai. Duk yadda Dija ta so sanin asalin damuwata yadda ta ganni cikin wani irin yanayi na kasa bata dama, kowacce ƙofa na rufeta. Domin a raina na yi alƙawarin babu wanda zai san wannan sirrin. Kwana biyu da wannan al'amari yaya ya tattara ya bar ƙasar, sai dai kullum yakan kirani sau babu adadi, yakan kuma turo mun da saƙon karta-kwana, ban san wace ƙƙsa yaje ba sai da Nisha take gaya min, bana sonsa ko kaɗan bana jin ƙaunar wani ɗa namiji cikin zuciyata, to idan ma na aminta na amincewa mutum me zance da shi ranar daren farkonmu? Zan faɗa masa cewa ɗanuwana ta ƙwace abu ma fi daraja a wajena?"

Kuka kawai take yi, Afna ma na rera nata, hawaye shaɓe-shaɓe kan fuskarta. Take ta shiga tuna tata rayuwar da ba za ta taɓa mancewa da yadda ta kasance marainiyar ƙarfi da yaji. Duk da cewa ta kasance da rashin uwa, amma ai mahaifinta na raye. Matar babanta ke riƙonta, riƙon da ya zama silar taɓarɓarewar rayuwarta. Riƙon da ya yi mata katanga da mahaifnta, ya daina ciyar da ita, kula da ita, tufatarwa, nemar mata da lafiya, da bata ilimi.
Rashin samun kyakkyawar kulawa ta lalatar da ita, dangin mahaifinta suka ƙi amsarta, mahaifiyarta kuwa daman ba 'yar nan ba ce, bata taɓa ganin danginta ba tun da ta taso, idan ta tambaye ta sai ta ce, 'wata rana za ta kaita ta gan su'. Tsintar kanta cikin mawuyacin hali ya sa ta fara bara, don neman abin da za ta riƙa sakawa a cikinta.

Ta shafe sati tana bara babu wanda ya damu da inda take zuwa, babu wanda ya damu da yaya take rayuwa. Cikin hakane ta haɗu da 'yan iskan ɓata garin da suka sauya ƙaddarar rayuwarta zuwa baƙa ƙirin. Ranar asabar da misalin takwas na dare, tana kan hanyarta ta dawowa daga wani gidan masu kuɗi da ta samu take ɗan aiki ana bata abinci, tana tsaka da tafiya ta ji taku a bayanta bata kawo komai ba kasancewar tasan hanyace ta wucewar jama'a duk da wani lokacin jefi-jefi mutane ke gittawa ta wajen. Shan gabanta aka yi mutane uku, dukansu cikin shiga ta rasjin dacewa, kafin ta yi yunƙuri ɗaya ya sa hannu ya tsohe mata baki nan suka jata wani kango tana turjiya da kuka amma hakan bai sa sun sarara mata ba.

   "Don Allah kar ku cutar da ni, ku ƙyaleni na yi tafiyata."

Kunnen uwar shegu suka mata, maganarta kuwa tamkar amshin shata haka suka ɗauketa, dukkansu ukun babu wand aya ɗaga mata ƙafa, ta ƙarfi da ya ji suka keta hafdinta suka ƙwace mata darajarta suka yi mata fata-fata. A nan suka yasar da ita suka bar wajen, ita kuma bata sake sanin halin da duniyarta ke ciki ba sai farkawar da ta yi ta ganta kwance kan gadon asibiti. Nan take samun labati fyaɗe aka yi mata kuma an yi mata lahani sosai, wani ne ma da ya shiga kangon yaganta yashe a ƙasa, shi ne ya kawota asibitin. Likita Dija ita ce ta amshi kulawarta domin tana buƙatarta, kasancewar ta samu matsalar yoyon fitsari wanda ya sa tilas sai ta ga likitar fannin mata wato gyneclogy.

Gyara ko sharhi ƙofa a buɗe take.
     08130266650 whtsapp only plz

Mai ƙosai✍️

HAFSATUL-KIRAMWhere stories live. Discover now