23-24 Ƙauyenmu

11 2 0
                                    

*HAFSATUL-KIRAM*

©Mai ƙosai

Babi na 23-24

Kallon kaka kawai nake yi da rinannun idanuwana. Murufan idanuna kuwa har sun kumbura saboda tsabar zubar hawaye.
"Ta yaya kaka?" Na sake jefa mata tambayar.
"A gobe baba Larai ke shigowa ƙauyen nan, domin ɗaukar yaran da iyayensu ke son turawa aikatau ta kaisu aikatau. Kema a gobe za ki bita, ki yi nesa da ƙauyen nan. Wannan hanyar kaɗai ita ce za ta sa ki yi nesa da abin da mahaifiyarki ke so."
Jin kaka kawai na yi, ina son kuɓuta daga kaidin mahaifiyata. Ina kuma jajantawa kaina da nisan da zan yi da kakata, wacca ita nake kalla a yanzu na ji daɗi.
"Me ya sa za ka tafi ka barni baba?" Na ce ina sake rushewa da kuka.
A washegari, baba Larai ta zo ƙauyenmu. A ranar muka ɗunguma ni da kaka muka je wajenta. Kaka ta shaida mata abin da take so da ita.

"Ba ki da matsala. Zan ajjiyeta har tsawon lokacin da kika buƙace ta. Zan sama mata aikin yi." Cewar baba Larai.
Jin furucinta ya sa kaka murmusawa. Ni kam kuka nake yi, zan yi nesa da kaka.
A ranar na baro ƙauyenmu, na baro mahaifata saboda kawai son zuciyar Innata. Yayin da gafe guda nake jin tsantsar tsanarta cikin zuciyata. Ko kaɗan bana jin cewa wai zan yi kewarta don na yi nesa da ita.

Na baro ƙauyenmu, zuciyata cike da ƙiyayyar mahaifiyata da ta yaya Lawan, wanda ya kasance mutumin da ya sake nakasta zuciyata. Har abada ba zan iya mancewa da irin yaudarar da ya yi mini ba. Ba zan taɓa iya yafe masa ba, domin ya cutar da zuciyata ta hanyar dasa mata soyayyarsa.

Garin Abuja, shi ne garin da muka yi wa tsinke. Na ji sunan ne ta bakin direban da zai ja ragamar motar da muke ciki, zuwa garin.
Har muka isa gidan da zamu ina faman tunani da takurawa ƙwaƙwalwata wajen gano mini hanyar da zan bi na illata zuciyar yaya Lawan.
Sosai na shagalta da kallon falon cikin gidan, ina rakuɓe jikin kujerar da baba Larai ke kai, kamar wacca take jiran ta ji an ce kyat ta zura a guje. Shigowar matsakaiciyar kyakkyawar mata falon, ya ba wa baba Larai damar sakkowa daga kan kujera zuwa ƙasa ta shiga kwasar gaisuwa, inda ni ma na mara mata baya.
"Yaya dai?" Matar ta shiga tambayar baba Larai.
"Hajiya wannan jikata ce, iyayenta ne suka yi hatsari suka mutu, shi ne na amsota wajen dangin mahaifinta na ce bari na kawota ita ma ta zo ta kwashe tabarrakinki."
Na yi kasaƙe jin irin ƙaryar da baba Larai ta shatato, tuni kuma wani bigire na ƙwaƙwalwata ya shiga ankarar da ni cewar 'ta yi haka ne don sake kuɓutar da ke daga sake afkawa cikin wani taskon.'
"To madalla! Babu damuwa je ki gobe za mu yi waya." Muyar matar ta katse ni daga hasashen da nake yi kan baba Larai.
Matar ta shiga shaida mini cewar 'na saki jikina da ita, kuma zamana na wasu 'yan kwanaki ne domin aikina yana ga wata kasar ne ba wannan da muke ciki ba.'
Ɗaki ta kai ne wanda shi ne masaukina, sai da ta nuna mini yadda zan yi amfani da komai musamman ma cikin bayi sannan ta ja mini ƙyauren(ƙofa) ɗakin ta fice.
Da ƙyar na iya sarrafa famfon, na ɗauro alwala na dawo ɗakin tare da gabatar da salla. A ɗaɗɗare na kwana a ɗakin, har ma ya zamana cewa na iya rayuwa cikinsa. Sai dai kowane dare da wayewar daren tashi nake yi cikin kewar kakata wacca baƙar ƙaddarar da tadako mini tsalle cikin rayuwata ta raba ni da ita, har na tsallake mahaifata na zo wani garin da ba nawa ba.
Ban wani kasance ina ayyuka da yawa cikin gidan ba, kasancewar na lura hajiyar na da tarin ma'aikata burjik.
Satina guda a cikin gidan. Ranar wata talata na tashi da wani irin ciwon kai, sakamakon kwanan daren da na yi ina nazarin tuna rayuwata da ta babana, wanda haka ya haifar mini da kasancewa cikin fitar da kuka mai tsananin sauti, kewar baba ta zagwanyo mini sosai.
Ina zaune ina faman safarar tunanina da na wayi gari cikinsa, hajiya ta turo ƙyauren ɗakin da nake ciki gami da sanar mini da cewa,
'gobe baba Larai za ta zo za ta wuce da ni wajen da shi ne zai zama dawwamemmen wajen aikina'
Take kuma tasa na yi mata alƙawarin ba zan ba ta kunya ba, zan zamo mai aikata duk abin da aka umarce ni da shi. A daren wannan ranar a ka zo a ka yi mini passport na barina kasar da nake ciki, na yi matukar kuka sosai ganin zan sake yin nesa da kaka.
"Inna kin cutar da rayuwata, kin ruguza mini farin cikina, kin sabauta rayuwata"
Na rushe da matsanancin kuka, har sai da na ji kaina tamkar zai rabe gida biyu kana na tsagaita.

"Kin ga ni ko? Daman na ce miki aiki sai kin gaji da shi, ga shi dai za ki ɗaga ki tafi wata ƙasar da tun da uwataki ta kawo ki duniya baki taɓa zuwa ba." Maganar baba Larai ta katse mini tunanin da nake yi a kan wane hali kaka take a yanzu?

"Ina son ganin kaka" Na ce da ita, yayin da ta ba ni amsa da ganinta zai yi wahala gare ni, inda ni ma na turje na kafe na tsaya kai da fata a kan lallai idan ban yi tozali da kaka ba to kuwa bazan sanya kafata na bar kasar ba zuwa wata kasar. Babu shiri baba Larai ta sanar da hajiya abin da ke faruwa wanda ba ta yi wata-wata ba ta sa aka yankowa kaka tikitin zuwa garin Abuja domin ganawa da ni kamar yadda na nema.

Lokacin da na yi arba da kaka ji na yi ina ma a ce ban amsa cewa zan bar kasar ba, wani zallan zunzurutun farin ciki ya nashe zuciyata, na yi wajen kaka tare da rungumota bayan na yi wancakali da jakar kayana da ke hannuna. Ji nake tamkar na haɗiye ta izuwa cikina.

"Kaka!" Na faɗa da wani irin amo, hawaye suka soma na su aikin, in da suka shiga kwaranyo mini saman kumatuna. Kaka ta sake rungumo ni tare da ƙanƙame ni zuwa wasu 'yan daƙiƙu kafin ta ɗago da kaina ta soma share mini hawayen da suke ta malalowa saman dandamalin fuskata.
"Hansatu! Idan har kika tafi kada ki dawo, ko da ace za ki sami saƙon rashina. Kada ki baro sabuwar duniyarki ki dawo tsohowar da kika jima a cikinta kina fuskantar ƙalubale da yawa.
Duk rintsi, duk tsanani da wahalar da za ki shaƙa a sabuwar duniyarki kada ki kuskura ki waiwayo gida. Ki daure ki fuskanci sababbun ƙalubalen da za ki iske a sabuwar duniyarki."
Sune kalaman da suka shiga tsakanina da kaka a wannan lokacin.
Na rushe da matsananincin kuka, daidai lokacin kuma amsakuwwar da ke wanze cikin filin jirgi ke sanar da lokacin tashin jirginmu, haka baba Larai ta ja hannuna muka soma hawa kan matattakalar da ke saƙale jikin jirgin, ina ji ina gani na yi nesa da kakata, zan yi nisan kiwon da ko kuka na yi ba za ta ji yo sautina ba balle ta rarrashe ni...

*Rashin Comment da share ya sa ni ma na rage yawan page*

Sharhi ko gyara ƙofa a buɗe take.

Mai ƙosai

HAFSATUL-KIRAMWhere stories live. Discover now