53-54 Wata ɗaya

12 1 0
                                    

HAFSATUL-KIRAM

  ©Mai ƙosai

      FCW

Babi Na 53-54

Bayan ta daidaita tsayuwar motar ta fito, kamar yadda ta yi ɗazu haka ta biɗe bayan motar ta ciro jakar abiey cikin hanzari ta mayar da murfin ta rufe ba tare da ta ba shi damar ɗaukar tasa jakar ba. Abiey kuwa duk yana ankare da su, da yadda suke gudanar da al'amuran nasu, murmushi kawai ya yi ya nufi sashen kaka. Tana zaune tana ta faman bambami akan Hafsa bata shigo ba, sai shegen kulafucin aiki da saka abu a rai kamar wata mayya.

Abiey dariya yayi cike da murmushi a fuskarsa ya karasa yana faɗin,
    "Ke da wa kuma inna?"

Jin muryar Abiey ya sa tsohowar wangale baki tana jefa masa tambayar saukar yaushe. Zama ya yi kusa da ita yana bata amsa da yanzun nan. Gaisheta ya shigayi yana tambayar lafiyarta.

  Sai a lokacin Lawan ya shigo yana tsokar kaka.

   "Matar nan kina nan da rai da man?"

Dariya ta yi, tana aika masa da yatsu biyar kana ta ce,
    "Sai gyatumarka ta fara mutuwa sannan zan mutu don kaniyarka."

Cike da kunshe dariyarsa ya karasa kusa da ita yana gaisheta cikin ladabi da nutsuwa.

  Hafsa kuwa ko ɓangaren kaka bata nufa ba, ta wuce sashenta don alwashi ta ɗaukarwa kanta ba zata sake bari inuwarta ta haɗu da shi ba. Tana shiga ɗaki ta jefar da wayarta tana mai zama gefen gadon ragwajaf.

  "Me ya sa zaka mi  haka abiey? me ya sa zaka ce nazo na ɗaukeka kai da mutumin da kasan bana son ganinsa." Taune leɓen ƙasan bakinta ta yi, tana cizarsa kamar ta yi hauka haka take jinta.

Ɓangaren kaka kuwa hirar yaushe gamo ce ta ɓarke tsakaninsu, yayin da lawan ke ta jan kaka da ɓarkwanci da tsokana, ita kuma tana lailaye shi da magana. Har azahar Hafsa bata leƙa kaka ba, nan hankalin kaka ya yi mugun tashi, ko da Afna ta shigo sashen kakar kaka ce ta aiketa akan ta je ta dubo mata Hafsan.

A gaba Afna ta taso Hafsa akan lallai kaka tace tazo tana son ganinta. Babu yadda zata iya yi haka ta miƙe tabi bayan Afna, da man ba komai take yi ba sai faman tunanin da ya cika mata kwanya. Shigarsu ke nan, mai aikin kaka ta soma jere abinci alamar zaman ɓangaren kaka za ayi.

Bayan ta gaida kaka ta hau tambayarta lafiya kuwa bata shigo ba.

   "Lafiya lau kaka, karfa ki ɗaga hankalinki ina lfy aiki ne ya sha min kai."

   "Haka dai, ke wai alhuda-huda ce da bakya gajiya ne. Bakya samun hutu a rayuwarki. Wannan aikin anya iro ba za ta ajjiye shi don naga alama shi yake ɗauke mata hankali har ya sa take gujewa batun aure. Tana kallo ga yaruwarta nan har ta kusa juyewa." Kaka ta karashe maganar tana kallon sashen da baba iro ke zaune.

   "Ai aikin lada ne inna, ko wanda zaia aurenta ma yana da kyau ya ɗaga mata ƙafa ta ci gaba da gudanar da abinta, tun da dai bai kaucewa addini ba. Kuma aure in sha Allahu zata yi shi rai dai wai an cirewa fara kai."

    "Har zuwa yaushe? Har tsawon wani lokaci zata manta da rayuwarta ta baya ta fuskanci gaba? Duk wata mace an fiso ta mutu gidan mijinta ita kuma tafi so ta mutu babu aure meye amfanin rayuwar da za ace ba zaka raya sunnar ma'aiki ba, na gaji tabbas zata yi aure kuma so nake kar ya wuce wata ɗaya ka jini ko? Ka sakata ta fito da miji tun da taƙi ɗanuwanta." Kaka ta yi maganar a kausashe.

Take kirjin Hafsa ya fara dakan lugude, aure kuma? Me ya sa kaka zata yi mata haka. Bakinta ya mata nauyi amma a haka ta buɗe da ƙyar ta soma magana,
   "Aure kuma kaka? Haba don Allah..."

    "Rufe min baki, ai na dawo daga rakiyarki yanzu babu ɗaga kafa aure nan da wata guda, idan kika kai ni bango kuma wallahi nan da sati guda." kaka ta katseta da hanzari.
Tana shirin yin magana sallamar yaya Lawan ta katseta. Miƙewa ta yi ta nufi hanyar fita.

   "Ina kuma za ki je ba ki ga babanki ba ne?" kaka ta watsa mata tambayar.

   "Zan je na sha maganin ciwon kaine."

   "Duk yadda kika kai da gudun maganata za ki je ki dawo ne, shi ke nan yarinya ba za a gaya mata gaskiya ba, ince inda shi baban naki yana raye da tuni ba ki yi auren ba har kin ajjiye 'ya'ya"
Ita dai burinta ta fice bata ma tsaya jin abin da kakar ke cewa ba ta yi wuuf ta ratsa ta gefwnsa da tunda ya shigo ya kafeta da ido ta fice da sauri. Murmushi ya yi, don ya fahimta inuwa ce bata so su haɗa da shi.

HAFSATUL-KIRAMWhere stories live. Discover now