02

24 2 0
                                    

SOFIA
NOBLE WRITERS ASSOCIATION
Shafi na biyu

DUTSE EMIRATE COUNCIL

FADAR MAI MARTABA SARKIN DUTSE.His Royal highness Alhaji. Abubakar Hamim ɗan Abdullahi CFR.

Zaune cikin kaya na alfarma farare da ruwan madara har ta rawanin dake kansa wanda ake ma lakabi da naɗin turban fari ne sol kamar sabo don da alama ma bai taba sanya shi ba...Yana cikin falon sa mai kalar jinin sarauta wato kalar golden da kuma kujerun royal jajaye masu kwalliyar golden, falon na da tsayi sannan ɗauke da kujeru zubin kujerun dining akallah goma ko sama da haka ɓangaren hannun dama dana hagu.

Cike da natsuwa ta shigo cikin falon tana taku ɗaya ɗaya da kasaita fatar jikinta mai haske wanda ya nuna alamar hutu ya samu waje, kasancewar fara ce amma ba fara sol ba, sanye take da kaya na alfarma saman kayan alkyabba ce mai tsada tana tafe bayi ƴan mata guda biyu suna gyara mata bayan alkyabbar, gaba ɗayan su suka russuna suna gaishe da Mai martaba yayin da ya amsa musu da kai cike da kasaita, suka juya suka tafi.

Mai martaba ya juya yana kallon matan sa ta biyu.

"Ranka shi daɗe, yallaɓai Mai martaba, Sarki nah fatan kana lafiya?

Duk da yau ba ita ce da turaka ba amma ganin yanayin da suke ciki hakan ya sa taji ba zata iya jure kin zuwa wajan Mai martaba ba.

"Lafiya lau Gimbiya sarautan mata, *Mami* Fatan dai lafiya ko da yake na san kina cikin damuwa shiyasa na gan ki a fada"

"Taka warka lafiya sarki na mahaifin ƴaƴa nah,"Hmmmmmm" ta sauke wani ajiyan zuciya mai tafiya da kwanciyar hankali yayin da ta nemi kujerar da Matan sarki suke zama idan sune da turaka kasancewar Fulanin Haɗejia bata karaso ba sai ta zauna don tayi abin da ya kawo ta, Ta cigaba da cewa,"Mai martaba har yanzu shiru ban ga Yarima Omar ba ga garin yana ta duhu"

"Ki kwantar da hankalin ki, Yarima Omar fa ba karami bane yanzu ya zama saurayin da zai iya kula da kanshi, Amma kasancewar Galadiman Dutse sun fita wani taro da sassafen nan bayan naji sanarwan sai na aika dakaru biyu da wasika akan su taimaka su ɗauko Yarima a makaranta"

Ya tsagaita lokacin da suka ɗan ji hayaniya daga waje duk fadar ta fara duhu duhu kasancewar kusufin wata daya bayyana, a hankali Mai martaba ya kalli Fulani Mami ya ce,"Ina ganin sune suka dawo Mami"

Mami ta gyaɗa kai, annurin fuskar ta ya sauya cike da farin ciki wanda yake wanzuwa a cikin zuciyar ta, a daidai lokacin da suka shigo Yarima na gefen Galadimam Dutse suna tafe suna hira yadda kasan kamar shine ainahin mahaifin nasa don har kammanni suke yi.

Fulani Mami ta rungume Omar tana cewa,"Shin dama ka san da labarin kusufin wata shine ka tafi makaranta shalele nah"

Yarima yayi murmushi mai kayatarwa sannan ya ɗaura idanuwa akan telescope ɗin dake hannun sa yace,"Abbu ni ina son na koyi ilimin taurari ne"

Mai martaba ya kalli Galadiman dutse ya sake kallon Fulani Mami sai kuma ya dawo da kallon sa zuwa ga Omar ya ce,"Yarima me ya faru ne?

"Ko ɗaya Abbu babu abin da ya faru, ka manta kamin alkawari shiyasa ka siyo min mahangar abin da ke nesa"

Galadiman dutse ya gyaɗa kai yana mai yafito Omar da hannu ya ce,"Ya ka nan Omar"

Omar ya nunfasa ya isa gare shi, ya kwanta a jikin sa fuskar sa a ya muste, Galadiman Dutse ya ce,"Ba munyi magana da kai a mota ba"

SOFIA ✔Where stories live. Discover now