KYAKKYAWAR FAHIMTA PAGE 4

5 0 0
                                        

KYAKKYAWAR FAHIMTA






WRITTEN BY HAERMEEBRAERH





PAGE 4:





"Ke zo nan, Ina Zaki je? Baki iya gaisuwa ba ne?"

A matuqar rikice Jiddah ta koma asalin wajen da take zaune ta hau in ina gaisuwar da ya yi ikirarin ko bata iya ba, se ya tabbata a yau ta kasa furta ta a Saman labb'an ta, zuciyar ta ce kawai ke ayyana gaisuwar amma bakin ta ya qi bata had'in Kai ta furta a Saman labb'an ta.

Ganin irin halin da ta shiga ne ya Sanya Major Muhammad Labbo sassauta d'aure fuskar da ya yi, ya Sanya kyakkyawa Kuma qayataccen murmushi a Saman fuskar shi wadda ta Sha aski Babu gashi ko d'aya, labb'an sa masu fad'i da tudu irin na Jiddahn ya mayar cikin bakin shi alamar qunshe dariya, cikin son yin dariya ya durqusa ya fara gaida Ummah da ke musu dariya shi da Jiddah.

"Lafiya qlou muke alhamdulillah soja ga wuta ga yaqi, yanzu ka ke tafe da yammar Nan? Ko sanar da zuwan ka ba ka yi ba amma, domin kuwa da na ji daga bakin Yaya dan ko d'azu shi da Abdunnasir sun zo gidan nan Yara suna makaranta, ka ga da zai sanar da ni ka na nan tafe"

"Ai kuwa dai wannan zuwan na bazata ne, aiki ya yi yawa na gaji da ganin masu laifi shine na ce bari na zo na ba wa idanu na abinci da mutanen kirki"

Ya na maganar idanun shi na kan fuskar Jiddah wadda ta sunkuyar da Kai qasa ta na Wasa da zoben azurfar da ke yatsanta na dama, Ummah ce ta d'auki kwandon gaban ta da ke d'auke da ragowar  yankakken cabbage da lettuce,tumatur albasa da tattasai Wanda shi suke zuba wa a Saman danwake idan an siya, rufe wa ta yi sannan ta wuce ciki ta na Masa iso.

"To Ummah gani nan zuwa"

A gaban Jiddah ya tsaya ya Dan duqa daidai fuskar ta yana ci gaba da kallon fuskar ta ya ce,

"Ina wuni? Da fatan na same ku lafiya? Ya exams? Kun gama ko da saura? Auntyn ki na ta damu na akan na Kai ki hutu Abuja yaran ki na kewar ki"

'Kaiii ya akai guy d'innan ya San Ina rubuta jarabawa?' ta ayyana a cikin zuciyar ta.

"Har yanzu Baki yarda na San komai game da ke ba ko? Tom aljanu na ne suka fad'a min"

Cikin sauri ta daga Kai ta kalle shi,sannan ta ce,

"Dama Maza su na yin aljanu ne Yah Major?"

"Kwarai da gaske mana, baki da labari? Ina zuwa na gama gaisawa da Ummah na zan zo na baki labari"

Cikin sauri da nuna alamar tsoro ta ce,

"Ah ah ni bana so, wa ya sani ma ko a wajen yi wa mutane mugunta ka samo su..."

Da sauri ta kulle bakin ta ta na zare fararen idanun ta ta na kallon shi, murmushi ya yi sannan ya wuce d'akin Ummah wadda ta gama had'a Masa abinci da abun Sha, Dan ta San ko gidan su ya je ba zai ci abinci ba sai ya zo wajen ta, a cewar shi idan ya zo gida ya na son ya samu sauyin abinci na gargajiya.

Bismillah ya yi kafin ya samu waje ya zauna, gaisa wa suka sake yi da Goggon tashi sannan ya wanke hannu da ruwan da ta aje Masa a roba, ya sake Bismillah ya fara cin abincin.

Kamar wadda aka wurga haka ta fad'a d'akin, ta na shiga kuwa ta zauna dafff da shi kamar zata shige masa jiki, cikin qara da murna ta ce,

"Yahhhh Majorrrrr ! Sannu da zuwa na gaji da baccin karyar, Yah Major na yi kewar ka ka jima baka zo ba,"

Cikin fad'a Ummah ta zari wayar charger da ke gefen gadon ta ta lafta wa Balqis da ke naniqe wa Muhammad Labbo a jiki ta na murnar ganin shi, saukar bulala a jikin ta ne ya Sanya ta tsanyara wata sabuwar qarar tare da rungume shi da kyau ta na kuka, cikin nuna alamar lallashi ya hau buga bayan ta, sannan ya ce,

KYAKKYAWAR FAHIMTAWhere stories live. Discover now