KYAKKYAWAR FAHIMTA 1

34 1 0
                                    


*KYAKKYAWAR FAHIMTA*

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 1:

Da misalin qarfe biyu da rabi 2:30Pm na ranar litinin sha biyu ga watan August 2018 hadari ne sosai ya had'o a cikin garin na Abuja Iska se kad'awa take ko ta Ina, garin ya yi duhu qirin kamar gabatowar magariba, kowa ka gani gudu yake yi domin neman mafaka,Wasu daga cikin masu motoci sun gudu sun shige ababen hawan su dan gudun dukan ruwan saman da in ya fara ba a San lokacin tsayawar shi ba, Banda gudun ababen hawa da qarar su tare da hayaniyar mutane da ke d'aga muryar su domin Wanda suke magana da su su Ji su ba abinda ke tashi a wajen.

Gefe d'aya kuma adaidai wannan lokacin ba abinda ya fi mahimmanci a wajen 'yan jaridun mu na qasa da ya wuce  son sanin shin ya shari'ar da aka gabatar a babbar kotun tarayya da ke cikin garin Abuja ta kasance a yau?

Major Muhammad  Labbo ne a  gaban 'yan jaridun da suka tsare gaba suka tsare gefe da gefen shi kamar an fad'a masu matsawa da yawan tambayoyin su ne zai sanya shi basu amsar komai da sike da buqatar sani a wajen shi, a bayan shi kuwa sojoji biyu ne tsaye sai muzurai suke yi suna jiran ko ta kwana su bawa major d'in nasu kariya, gefe d'aya Kuma Barrister Haladu Kangiwa ne shima tsaye cikin cincirindon manema labarai, wata tambaya da aka yi wa Major Muhammad Labbo ne ta Sanya kusan dika manema labarai suka tattare suka koma wajen shi domin Jin kalar amsar da zai basu, cikin kamalar shi da nutsuwar shi ya ke bada amsa kamar haka.

"Kamar yanda mutanen qasar Nigeria suka sani wannan qara da aka gabatar gaban kotu tun 02/03/2018 har yanzu ana ta faman gumurzu ba a kawo karshen ta ba, muna fatan a wannan watan komai yazo qarshe, dangane da amsar tambayar ku Kuma a gaskiya bani da hurumin amsa wannan tambaya duba da cewa magana ta na gaban kotu, bincike da ake ta yi shi ne zai warware komai, ku ci gaba da hakuri sannu ba ta hana zuwa, muna roqon mutanen Nigeria musamman mutanen mu na arewa da mu dage da addu'a har Allah ya fitar da mai gaskiya a wannan shari'a mara gaskiya a yanke masa hukunci daidai da abinda ya shuka."

"Idan na fahimta yanzu kenan dai ranka ya dad'e Major Labbo ka na nufin har yanzu ba a gano wad'anda ke shigo da makamai cikin kasar nan tamu ba har ta'addanci da kashe kashen bayin Allah ya yawaita?"

Kafin ya bud'i baki ya bada amsa, d'aya daga cikin sojan da ke bashi kariya ya bud'a hanya dandazon mutanen da ke wajen duk sun dare Major Labbo ya ratsa ta cikin su ya wuce, Kai tsaye jikin motar shi da aka bud'e masa ya nufa ya shige cikin izza da mazantaka.

Kamar ruwan nan jira yake Major Labbo ya shiga mota nan take ya sauka kamar da bakin k'warya, 'yan jaridun nan kuwa basu da zab'in da ya wuce na su nemi mafaka kada ruwa ya dake su da kayan aikin su, ba tare da sanin 'yan jaridun ba aka fitar da shi ta boyayyiyar qofa aka tura shi mota hannun shi daure cikin sarqar da ake daure masu laifi, a guje motar ta bar harabar wajen, Wanda ya ja hankalin 'yan jaridar da ke ta baza Ido Dan ganin ta Ina za su fito, duk wani yunqurin su na ganin sun Samu zantawa da qasungurmin mai laifin amma  inaa hakan ya ci tura, dole suka hakura suka samu mafaka Wasu Kuma suka shiga ababen hawan su suka bar wajen.

Zaune yake cikin kujerar shi ya lumshe Ido ya na tunanin wannan shari'a da ta qi ci ta qi cinyewa, ji yake kamar ya ajiye aikin shi ya huta, abubuwan se qara tsauri suke yi, ya rasa ta Ina complications d'in da ke cikin shari'ar suke zuwa, menene abun wahala? Hukumar rundunar soja ta qasa ta yi nasarar Kama d'aya daga cikin manyan y'an bindiga da ke garkuwa da mutane a jihohin Kebbi,Nigeria, zamfara, da katsina zuwa Wasu sassa na arewacin qasar nan tamu Kama daga Kano Kaduna har zuwa Abuja da shi da yaran sa, amma har yanzu an k'i yanke musu hukunci ana ta d'aga karar tare da Jan lokaci, da alama daga wannan zuwan ba zai sake halartar kotun ba tunda dama son ji da ganin yanda za a yanke musu hukunci ne ke Kai shi ba wani abu ba, hukumar su sun yi iya nasu qoqarin sun gama a matsayin su na Wanda ke kishin kasar su ta gado , yanzu ya rage wa kotu ta zartar da hukunci bisa adalci ko Kuma a bar maganar ta salwanta kamar yanda ake yi a sauran criminal cases da aka Saba yi,tunanin shi ya sake fad'a wa bangaren Wasu daga cikin  manyan sojojin qasar nan da ke ta qoqarin danne Wasu bayanai, menene alaqar su da wannan case d'in? Me yasa suka yi ruwa suka yi tsaki a lamarin?

KYAKKYAWAR FAHIMTAWhere stories live. Discover now