KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 9:
D'aki Balira ta koma dan tabbatar da cewa Muido bai farka ba saboda tsananin tsoron shi take ji itama, hukuncin Muido baya tsallake kan kowa sai dai idan ba a yi masa ba daidai ba, dan haka addu'a take ta yi Allah ya bata sa'a ta taimaka wa Jiddah ba tare da ya sani ba.
A can madafi kuwa matan nan dama abinci kala biyu suke yi, abincin Muido da iyalan shi, yaran shi da su matan yaran na shi,Wanda abincin su na alfarma ne ake masu Dan Jin dad'in su, abinci ne ake masu na irin mutumin da ya yi aikin wahala ya Sami halal d'in sa se ya ce bari ya ci Mai dad'i dan barje gumin sa,sai Kuma abincin jama'ar Annabi da suke kamo wa,shi kuma abincin mutanen da suke kwamusowa abinci ne mara kyan gani a Ido Kuma mara dad'i a baki, dan wani lokacin ana sane ake dafa jellop rice ba Maggi daga gishiri sai tattasai busasshe, ruwa kuwa na kogin garin suke ba wa mutane, su Kuma ruwan Leda suke sha Gorko Muido kuwa ruwan roba yake Sha.
Suna kammala abincin suka Kai na iyalin Muido da shi kan shi Muido'n d'aki da Ido suka yi wa Balira alama ta kuwa miqe ta fita kamar ba wajen su za ta je ba, Fure ce ta yi tsaki dan ita haka d'abi'ar ta take da kowa ma bata shiri har shi kan shi Muido'n da take mutuwar so,abinci ta ja ta hau zubawa abun ta hankali kwance.
Balira na zuwa ta d'auki plate d'in da aka zuba wa Jiddah soyayyan dankalin turawa da kwai se soyayyan nama shayi aka had'a Mata a cup karami se ruwan Leda guda d'aya,a hanzarce Balira ta ke sauri Dan Isa inda Jiddah take, ta na zuwa ta bud'e qofar da aka maqala wa kwad'o ba tare da an datse ba,ganin Jiddah ta yi jingine a jikin ginin wajen, idanun ta duk sun kumbura sun yi jawur, Jiddah kuwa Jin idanun nata take kamar ba nata ba, wani irin yaji da zogi suke yi mata ko gani bata yi sosai se dai dishi dishi.
Cikin yin qasa da murya Balira ta durqusa a bakin qofar ta ce wa Jiddah.
"Jiddah daure ki tashi ki ci abincin nan kafin Gorko Muido ya farka"
Wani irin kallo Jiddah ta bi Balira da shi, Wanda ya Sanya Balirar Jin nauyin sake had'a idanu da Jiddah, cikin dasasshiyar murya Jiddah ta ce,
"Ba ruwan ki da ci na ko Sha na,ki je ki ci gaba da faranta wa mijin ki ta hanyar shiga gidan mutane ki gane sirrin su ki je ki sanar da shi shi Kuma ya sace su ya Kai su inda ya ga dama ko ya kashe su ko ya azabtar da su"
Idanun Balira sun taru da kwalla dan kuwa ita kan ta tunda Muido ya ce ta je gidan su Jiddahn ta Kuma je ta ga yanda suke gudanar da rayuwa a gidan su gwanin sha'awa, sannan ta gane Jiddah yarinyar kirki ce se ta ji bata so ya sace Jiddahn, ba yanda za ta yi ne, da ta na da yanda za ta yi Kar hakan ta faru da tun a baya ta San yanda ta yi ta hana faruwar hakan, cikin rauni ta ce wa Jiddah,
"Ki gafarce ni Jiddah ni Kai na ba a son raina nake rayuwa a qarqashin ikon sa ba, an fi qarfin Mahaifi na ne, abinda baki sani ba shine hatta da abincin da za mu ci sai sun bamu izinin me za mu noma a gonakin mu, sannan se sun karbi haraji a kowacce gona da aka yi shuka cikin ta, hatta da 'yan kasuwa a garin Nan basu tsira ba,duk abinda ka ke siyar wa suna da kamasho a ciki, Mai garin garin nan kan shi se yanda akai da shi wato Mahaifi na, ba shi da katabus a karagar mulkin sa, ya na iya zartar da hukunci Gorko Muido ko shugaban Gorko Muido d'in su hukunta shi shi kan shi saboda be nemi shawarar su ba, dan da dare kuka shi go ne amma da Zaki ga kowacce unguwa ko layi akwai mutane da kayan soji da makamai, to yaran Gorko Muido ne da kuma Wasu qungiyoyin, idan suka ga dama suna iya zuwa su kwace wa mutum shanun sa da dabobin sa Kuma dole ya hakura dan ba yanda zai yi, kuma ba hukumar da za ta karba wa mutum haqqin sa su ne hukumar, da wannan bayanin nawa nake fatan Zaki gane abinda na yi maki tursasa ni aka yi dan Allah ki samu ki cinye ki bani kwanon na mayar saboda ki samu qarfi a jikin ki,tunda ya ce Zaki Sha wahala to fa tabbas Zaki Sha wahalar Indai ba kin aminta da qudirin sa bane"
YOU ARE READING
KYAKKYAWAR FAHIMTA
RomanceKYAKKYAWAR FAHIMTA ke Sanya Mata da miji su yi zama na amana cikin so da qauna da kulawa tare da tarairayar junan su,haka zalika KYAKKYAWAR FAHIMTA na sa qasashen duniya su zauna lafiya, kamar yanda KYAKKYAWAR FAHIMTA na iya zaunar da qasa lafiya...