KYAKKYAWAR FAHIMTA PAGE 8

1 0 0
                                        

KYAKKYAWAR FAHIMTA

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 8:



Cikin murya mai kaushi tare da sakin hannun ta Muido ya ce wa Jiddah,

"Je ki zauna a can, gobe war haka kin zama mallaki na ke ma, gasu nan, waccan da ki ke gani ita ce uwar gida, sunan ta Fure, 'ya ce a wajen wani hamshaqin d'an kasuwa, wani informer na da ke cikin garin Kaduna ya sanar dani Mahaifin ta hamshaqin Mai kud'i ne in aka kama ta zai saki nera ga ta nan da kud'in uban ta muka Gina nan Kuma muka hana shi ita,wannan Kuma 'yar Mai garin nan Mariga ne,kyan ta da natsuwar ta ne suka ja ra'ayi na na sa liman ya aura min ita, Jiddah tunda nake ban tab'a son mace ba da sunan soyayya ba se dai ta burge ni, a kan ki na San menene so,na San ya ake ji idan ana Jin so irin na soyayya tsakanin mace da namiji, Jiddah bana qaunar safiya ta yi ban yi tozali da kyakkyawar fuskar ki ba,bana gajiya da kallon ki,a duk sanda nake kallon ki kyawun ki karuwa yake a ido na,tun daga ranar da na gane Ina son ki na ji ba zan iya barin ki ba tare da na aure ki ba,shine dalilin da ya sa na Sanya maki masu tsaron lafiyar ki ba tare da ke kin sani ba,duk Inda Zaki je akwai masu gane min duk abinda ki ke yi, da fari na so na sace ki saboda dangin mahaifiyar ki da Mahaifin ki suna da kud'i ko da ku baku da shi,akwai zumunci Mai qarfi a tsakanin ku ba za su tab'a barin ki ba sai sun biya kud'in fansa, Jiddah a yanzu na sauya ra'ayi na game da kab'ar kud'in fansa akan ki, auren ki shi ne fansar ki,Dan haka ki shirya gobe za a daura mana aure, sai dai ke ba kamar sauran Mata na ki ke ba, na yi maki alqawarin ba zan tab'a kusantar ki ba har sai kin aminta da ni da kan ki"

"Ai kuwa ranar da zan aminta da Kai ba zata tab'a zuwa ba har abada ni Jiddah da na aminta da dan ta'adda azalumi irin ka gwanda na mace ban yi aure ba, da ka duba ka ga dangin namu na da kud'i baka hango Ina da Wanda zan aura ba a cikin dangin?,ni Jiddah a yanzu a kaf duniyar nan bani da Wanda na tsana nake qi Sama da Kai,a baya na yi zaton Kai mutumin kirki ne, yanayin shigar ka da gemun ka ya yi kama da na mutanen kirki, na yi tunanin na sanar da iyaye na ba zan iya auren Yaya na ba da suka zab'a min saboda soyayyar mutumin da bai San Ina yi ba,ashe Kai din mayaudari ne , d'an ta'adda ne, azzalumi ne, me kashe mutane ne,ashe Kai ba alkhairi a tattare da Kai, to Ina neman tsarin Allah akan ka Ina roqon Allah da ya kare ni daga sharrin ka, ni Jiddah na tsane ka, na tsane ka, na tsane ka, ba na son ganin ka, ka taimaka min ka maida ni gidan iyaye na, Ummah na Bata da lafiya Kar wani abu ya same ta Dan Allah"

Cikin matsanancin kuka ta qarasa maganar ta tare da durqushewa a gaban shi ta kama kafar shi ta na masa magiya,Muido kuwa nan take duk had'uwar da suke yi ta fara gilma Masa a kwayar idon sa, murmushin ta da kunyar ta tare da tsananin kyan da Allah ya Mata sun yi masa, bayan iyayen sa da qannen shi be tab'a son wata halitta ba Sama da Jiddah, Dan haka Jin kalaman ta yake kamar saukar ruwan zafi a Saman fatar da ke cikin Sahara a tsananin zafin bazara,cikin matsanancin fushi ya fizge ta ya wurga ta tsakar gidan, ya bi ta da kafar shi ya take cinyar ta sannan ya durqusa a saitin fuskar ta, idanun shi da suka Sha kwalli suka rine suka yi jawur suke fidda wani ruwan masifa ya kafa Mata sannan ya nuna ta da yatsa kafin ya nuna kan shi, cikin baqin ciki da kunar rai ya ce Mata,

"Ni? Ni mace zata kalla ta ce wa bata so na Ido cikin Ido? Lallai Jiddah kin yi kuskure, Jiddah se kin yi danasanin wadannan kalaman naki, zan gana maki azabar da da kan ki Zaki kawo kan ki ki ce kin amince Zaki aure ni, zan gana maki azabar da Zaki manta da Wai iyayen ki sun zab'a maki Wanda Zaki aura, zan gana maki azabar da sai kin zo da kan ki kina rokon na aure ki Jiddah"

Cikin kuka da kafiya da taurin kan da bata tab'a sanin ta na da shi ba ta kalle shi hawaye na zuba idanun ta sun kad'a sun yi jawur ta ce,

"Har abada ba zaka ga wannan ranar ba, a yau na tsine wa ranar da na fara ganin ka a rayuwa ta, na yi Allah wadai da ranar da na fara Jin qaunar ka a rai na,Ina maka albishir nima ko da zaka dinga yankar naman jiki na ka na cin shi d'anye ne ba zan tab'a amince wa auren ka ba,Kuma shi Wanda ka ke cewa zan manta da shi ka San ko wanene? Zai iya zagaya duniyar nan domin nema na,Ina tausaya maka a duk sanda za ku yi Ido biyu da Yah Major, Ina tausaya wa rayuwar ka maqasqanciya a hannun Wanda zan aura"

KYAKKYAWAR FAHIMTAWhere stories live. Discover now