KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 5:
A zaune ta tadda Ummah ta na qirga kud'ad'e masu yawa ta na murmushi, itan ma murmushi ta yi ta na cewa,
"Da dikkan alama komai ya yi daidai Hajiya Ummah, Umara ce ko Hajji?"
"Allah ya kira mu 'yar nan ba Dan halin mu ba, sai Dan rahamar sa da kyautar sa"
"Ameeen ya Allah Ummah"
"Uhumm Ina Jin ki, wace magana ce a bakin ki?"
Da Jin haka sai Jiddah ta daburce ta kasa furta komai,jikin ta ya yi sanyi qalou, da wanne Ido za ta kalli mahaifiyar ta ta ce bata son auren d'an Yayan ta akwai wanda yake burge zuciyar ta? Akwai Wanda take ganin zata iya rayuwar aure da shi za ta ji dad'in zama da shi Sama da d'an d'an uwan ta? Gaskiya idan ta yi wa Ummah haka za ta Sanya ta a bakin ciki mai yawa, ita Kuma har abada bata fatan ta sa iyayen ta a qunci, fatan ta ta zamo yarinya mai biyayya a koda yaushe,sannan ta wani fannin bata tab'a Jin qiyayyar Yah Major ba, kawai dai bata Jin soyayyar shi a ran ta kamar yanda take Jin qaunar wannan bawan Allah da ko sunan shi bata sani ba, sannan ta ya zata fara ture alqawarin shekaru ta kawo uzirin soyayyar da ba a ma fara ta ba, gashi bata da tabbacin shi wannan bawan Allah son ta yake ko Kuma burge shi kawai take.
"Kin yi shiru, ko akwai matsala ne?"
Kud'in gaban ta ta ture gefe saboda ta samu damar bawa d'iyar ta cikakken lokaci da hankalin ta.
"Ammm Ummah dama cewa na yi, Yah Major ya kawo min waya kin gani kuwa? Ki na ganin ya kamata na riqe wayar ba mu yi aure ba?"
Dan guntun tsaki Umman ta yi ta na murmushi,
"Har kin sa hawan jini na ya kusan tashi, ai na zaci cewa za ki kin fasa auren shi, baki ji yanda hankali na ya tashi ba, Jiddah auren Junior alkhairi ne a gare ki ke da 'yan uwan ki,ko bayan rai na Ina fatan za ki zama mai biyayya a gare mu domin samun ingantacciyar rayuwa a nan gaba, maganar riqe wayar da junior ya sai maki ai kema kin San ba wata matsala, ko ba komai d'ana ne shi fa? Yayan ki ne zai iya sai maki waya ko ba maganar aure a tsakanin ku, ballantana akwai maganar aure, ki ka sani ko kewar ki yake Yana so ya dinga Jin muryar ki idan baya nan?"
Cike da Jin matsananciyar kunya Jiddah ta miqe zata bar d'akin tre da fad'in
"Kaiii Ummahhhh"
Dariya Ummahn ta yi ta sake Jan kud'in ta gaban ta ta na lissafi, d'akin su Jiddah ta koma ta kwanta bayan ta Sanya wayar da ke kashe a caji, bata sake tab'a wayar ba har se da suka yi sallar isha'i, lokacin Sudais ya shiga gidan ta dakko ta nuna masa, albarka ya Sanya wa wayar ya Kuma gargad'e ta da Kar ta kuskura ya kama ta tana wani shashanci da wayar, ya had'a har da Balqis saboda ya San yanzu qarfin riqe wayar zai koma hannun ta ne.
Bayan sun ci abincin dare kowa ya kwanta, Sudais ya shiga d'akin mahaifiyar tashi da ke zaune zaman jiran shi, nan suka tattauna akan gagarumin abinda suke qulla wa ba tare da sanin kowa ba a gidan, suna tsaka da maganar suka jiyo dawowar Mahaifin su, a lokacin qarfe goma sha d'aya na dare ta gota, sallama Sudais ya musu sannan ya wuce soro inda yake kunna maganin sauro ya saka tabarma da zannuwa ya rufa ya yi baccin sa da pillow.
Balqis, Jiddah da Ihsaan kuwa a d'aki d'aya suke kwana, shi yasa kullum idan ya na yi masu rashin kunya Balqis ke cewa,
'Dole ka rai na mu tunda ka ga wajen kwanan mu yaro'
'Da da gado da katifa a wajen kwanan naku da ban raina ku ba, ku na fama da wata tsohuwar katifa tun ta auren Ummah ai dole raini ya shiga tsakani'
A duk sanda ya fad'i haka da kyar ake raba su dambe shi da Balqis,watarana Kuma idan bata Jin fad'an se ta kyale shi su yi ta cacar Baki.
YOU ARE READING
KYAKKYAWAR FAHIMTA
RomanceKYAKKYAWAR FAHIMTA ke Sanya Mata da miji su yi zama na amana cikin so da qauna da kulawa tare da tarairayar junan su,haka zalika KYAKKYAWAR FAHIMTA na sa qasashen duniya su zauna lafiya, kamar yanda KYAKKYAWAR FAHIMTA na iya zaunar da qasa lafiya...