KYAKKYAWAR FAHIMTA PAGE 7

1 0 0
                                        


KYAKKYAWAR FAHIMTA

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 7:

Hannun ta ta ji an dafe cikin sauri ta d'aga kai suka yi Ido biyu da Ihsaan Wanda idanun sa suke a kumbure saboda kukan rashin Yah Jiddah, cikin dasasshiyar murya ya ce,

"Ke Wai ba an ce Kar a sanar da shi me ke faruwa ba saboda yanayin aikin da ya tafi yi?"

"Ai tunda ka ga ya kira da No shi ta Nigeria ya dawo qasar ka bari na sanar da shi halin da ake ciki ko zai taimaka mana"

"Ki bari har Abbah ya dawo ko a bamu izinin sanar da shi, ke dai duk rashin ji na kin fi ni se ki dinga kafewa akan abu kamar namiji"

Harara Balqis ta banka Masa sannan ta ce,

"Ko abinda ya fi namiji ba in baka kiyaye ni ba se na b'arar maka da haqora"

Ummah ce ta fito daga band'aki idanun nan nata jawur, kallon su ta yi ta kad'a Kai sannan ta kama hanya zata shige d'akin ta, bakin ta na furta,

"Allah ya shirya ku, muna cikin wannan mawuyacin halin amma ku kun ga ta yin fad'a, a zato na b'atan Jiddah zai zame maku darasi,"

Jikin su ne ya yi sanyi, Balqis ta zabga tagumi nan da nan hawaye ya fara zuba mata, kallon Ihsaan ta yi ta miqa masa wayar Jiddahn Dan ta tabbata idan har Yah Major zai ci gaba da kira to fa za ta dauka ta sanar da shi komai.

Karba ya yi ya latse wayar gaba d'aya ya kashe ta sannan ya shiga d'akin Ummah cikin kwanukan da take ajiye kud'i ya saka wayar ya bar gidan gaba d'aya.

**********************

Tafe suke cikin wani irin surquqin daji ba gida gaba ba gida baya, motar nan ba abinda take da ya wuce tashi Sama sannan ta dawo ta daki qasa,gaba d'aya Jiddah da sauran matan da ke cikin motar sun jiqata, tun suna Kuka har suka danganta suka dena kukan,wani irin mawuyacin numfashi kawai suke fitar wa, Muido ne ya kula da yanda jikin Jiddah ya sake kamar ta Suma,gaba daya ya juya ya hau jijjiga ta, gani ya yi baya iya riqo ta da kyau sakamakon shi ya na zaune ne a gefen driver,cikin tsawa ya bada umarnin a tsaya,wani wawan burki motar ta ci ta tada qura sannan ta tsaya a tsakiyar dokar dajin, yamma ce sakaliya rana ta dakko fad'uwa wajen ya d'auki wani irin yanayi Mai dad'i saboda ruwan da aka tafka tun daren jiyan,gashi har a wannan lokacin akwai alamun hadari wataqila a sake yin wani ruwan Saman, fita Muido ya yi cikin hanzari sannan ya bud'e bayan motar ya fitar da Jiddah daga ciki,sannan ya d'auki ruwan robar da yake Sha ya watsa Mata a jikin ta,nan take ta ja wata ajiyar zuciya mai qarfin gaske sannan ta bud'e idanun ta a Saman fuskar kyakkyawan bafulatanin da a baya take mutuwar son ya furta mata kalmar so, wata iriyar zabura ta yi ta na waige waige Dan ganin inda suke, ta na ganin su a daji ta ji wata iriyar juwa ta deb'e ta ta na qoqarin sake faduwa sumammiya,

"Ta tabbata kenan sace ni ka yi? Me na yi maka? Me na yi maka mummuna da na cancanci haka a gare ka? Ka San kuwa yanda zuciya ta ta baka babban matsayi a cikin ta?"

Kafin Jiddah ta sake yin wata maganar Muido ya zabga wani uban ihuuu ya ja baya ya daga bindiga Sama se zabga harbi yake, drivern shi da ke tuki ma se washe baki yake saboda ganin halin da shugaban shi ya shiga na farin ciki da murna, a wajen su idan suna cikin farin ciki ko baqin ciki da harbe harben bindiga suke expressing kan su.

Wani irin kallon tsana da qiyayya Jiddah ta wurga wa Muido, ganin irin kallon da take masa ne ya sanya shi yin saurin Sanya ta a gaban mota shi ya koma baya ya zauna da sauran matan da ke baya,

"Ja mu je D'an Gumel tun kafin ra'ayin Mata ya sauya akan 'yan Maza su yi b'arna, ka San mata ba su da tabbas"

Da gudu Wanda aka Kira da D'an Gumel ya ja mota suka ci gaba da nausawa daji Jiddah kuwa ji take kamar ta bud'e marfin motar ta fita idan ma mutuwa ne gwanda ta mace da dai ta zauna a hannun wadannan azzaluman.

KYAKKYAWAR FAHIMTAWhere stories live. Discover now