KYAKKYAWAR FAHIMTA
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 3:
Zaune yake luntsume a cikin kujerar had'ad'd'iyar motar da aka sace shi daga hannun hukuma se gudu drivern yake da alama inda za su je akwai nisa, lumshe kyawawan idanun shi ya yi tare da sauke sassanyar ajiyar zuciya, murmushi ne kwance a Saman fuskar shi mai cike da gashi duguzummm Wanda da gani ya jima Bai samu aski ba, yaran shi ne ke yi masa bayanin yanda Babban ogan su ya sa a had'a gadar zare dan a kub'utar da shi daga hannun hukuma, wayar da ake miqa Masa ya karba, cike da ladabi ya fara magana cikin harshen fullanci da hausa,
"Allah Saini barka da war haka......
Miyetti masin Allah Saini Allah wadi barka, se mun iso"Abinda ya fad'a kenan ya miqa wa Wanda ya bashi wayar da farko, sannan ya Kara lumewa cikin kujerar tare da lumshe idanun shi kamar mai son ya yi bacci, nan kuwa ba bacci yake ba tunanin ta ne fall cikin zuciyar shi.
"Jiddah"
Shi ne sunan da ya furta a hankali, Wanda idan ba mutum ya natsu ba ma ba zai ji me ya ce ba da kyau.
"Se na cika alqawari na akan ki hankali na zai kwanta, idan da fari an yi min fin karfi wannan karon ban dawo da Wasa ba, ba zan tab'a barin ki ba, sai na mallake ki, sai kin zama tawa ni kad'ai,saboda ke nake ci gaba da rayuwa a yanzu,"
Waiwaye.......
Tafe take cikin uniform d'in ta na makarantar boko se tsiyayar da zufa take, sakamakon zafin da ake bugawa a garin na Kamba dake a qaramar hukumar Dandi,Rana ce ta kwalle sosai kamar zata tafasa kwakwalwar d'an Adam, tasbihi kawai take ga Allah saboda idan ba Allah ba ba mai gudanar da wannan lamari, ga rana, ga zafin da ake zabgawa Kuma dan Adam ya ci gaba da rayuwa be narke ba ko ya qone.
Murmushi ta yi da ta yi wannan tunanin, har ta na ayyana,
'Wai wa ya ga Jiddah Black ta qone, ko ta narke ta zama kitse'
Ledar hannun ta da ta yo cefane ta qara damqe wa tare da sake rataya jakar makarantar ta a kafad'ar ta ta dama, cikin sauri take taku dan son Isa gida da wuri ta watsa ruwa, qanwar ta ce ta yanko daga wata kwanar da ke gaban ta ta na dariya,itama Jiddahn dariyar ta yi sannan ta ce,
"A gaskiya Iska na wahalar da mai kayan Kara,ko dake bahaushe ya ce sa Kai ya fi aikin bauta ciwo,yanzu dai gashi takun da ki ka wuce ni da shi kad'an ne,ga uban sauri ki na ta zabga wa dan Kar na wuce ki,amma kin qi ki dena wahalar da kan ki a banza"
"Oho dai na riga ki isowa gida woooo"
Da gudu Balqis ta fad'a cikin gidan nasu saboda ganin Jiddah ta kusan riga ta shiga ciki, cikin raha da walwala suka karasa cikin gidan nasu na haya Wanda yake da dakuna biyu kacal ba kitchen ba parlour se tsakar gida mai fad'i da bandaki biyu.
A gefen tabarmar da mahaifiyar su da suke Kira da Ummah ke zaune Suma suka zauna suna maida numfashi,da sauri suka cire hijaban su suna gaishe ta cike da girmama wa,domin kuwa Jiddah da 'yan uwan ta sun samu cikakkiyar tarbiyyar Islama wajen mahaifiyar su.
"Lafiya qlou 'yan albarkan Umman su,an dawo kenan, ya jarabawar to?"
"Eh Ummah mun dawo jarabawa Kuma alhamdulillah"
"Da kyau, Allah ya muku albarka ya bada sakamako mai kyau mai albarka,Jiddah ya naga kayan miyan yau kamar da yawa?"
"Eh Ummah ba laifi yau ya mana arha gaskiya,bari na je na watsa ruwa zafi nake ji sosai"
"To ya kamata kam maida hankali ki yi sauri kafin Ihsaan ya dawo ya kama maku masifar ya deb'o ruwa Kuna sheqarwa a banza gashi yamma ta gabato a yi a zo a dauraye plates d'in anjima"

YOU ARE READING
KYAKKYAWAR FAHIMTA
Roman d'amourKYAKKYAWAR FAHIMTA ke Sanya Mata da miji su yi zama na amana cikin so da qauna da kulawa tare da tarairayar junan su,haka zalika KYAKKYAWAR FAHIMTA na sa qasashen duniya su zauna lafiya, kamar yanda KYAKKYAWAR FAHIMTA na iya zaunar da qasa lafiya...