KYAKKYAWAR FAHIMTA 2

14 0 0
                                    


*KYAKKYAWAR FAHIMTA*

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 2:

Kamar abun Wasa washegari da safe kowa na hada hadar shi wani maqocin su Muido ya shigo rugar  tasu a guje ya na kuka ya na burgima da ihun a je a taimaki shanun shi, Banda fulatanci ba abinda yake sakewa,tsabar tashin hankalin da yake ciki ko d'igon hawaye babu a idanun shi, da kyar Mahaifin Muido ya samu nasarar Sanya shi ya natsu ya yi masu bayanin abinda ya faru, cikin fitar da numfarfashi bafulatanin nan ya ce,

"Sabi'u am chanu na sun halaka, an kashe min Chanu na da tumaki na shikenan maganar sulhu tsakanin mu da manoma ta kare, jiya jiya ka ke bamu chawara mu je a daidaita da manoma Kuma na yi na'am da hakan amma suka kashe min Chanu"

"Assha ! Ashha ! Amma wannan lamari be yi dad'i ba, yanzu dai ba lokacin ganin laifi bane, mu je mu ga barnar da aka yi maka se mu je wajen mai gari"

"Aradun Allah se na da'u fansa, aradun Allah ba zan hakura ba Sabi'u"

"Ka yi hakuri, amma tabbas ba su kyauta ba, da ka sani Kai ma da baka je gonar su ba tunda mun tsayar da magana za mu je a sake zama a yi sulhu, daure ka tashi mu je fada"

Su na Isa suka tarar da Wasu mutane uku Suma sun Kai koken an kashe masu ababen kiwon su, nan da nan kuwa Mai gari ya bada rashin gaskiya zuwa ga Fulani ,tunda da ba su saki shanun su sun shiga gonaki ba da ba a kashe masu su ba, duk bayanin da Wasu mutum biyu ke yi na cewar su fa tafiya kawai suke manoman suka far masu suka dinga saran dabbobin su ba tare da sun ji ba ko kuma sun gani ba, haka Mai gari ya toshe kunnen sa ya ba su rashin gaskiya, wannan abun da ya yi kuwa ba qaramin Sosa ran Fulani ya yi ba, har suka fara zargin ko dan asalin Mai garin ya had'a dangi da hausawa ne ya Sanya shi tsaida rashin adalci a gare su.

Haka fada ta tashi ana ta hayaniya,duk jikin Malam Sabi'u ya yi sanyi har ya Isa gida,Muido na dawowa da qannen shi daga islamiyya Mahaifin sa ya labarta masa komai, akan abinda ke faruwa, sannan ya umarce su da su dinga kiyaye Kai ababen kiwon su wajen da bai dace ba.

Abinci suka ci suka Sha ruwa Muido ya zauna sassaqa wa Adda Petel da Sa'ade 'yar tsanar icce, gefe d'aya kunnen shi na jiye Masa duk wata hirar da iyayen nashi suke yi,ba zato ba tsammani ya ji maganar mahaifin shi na fad'in,

'Bad'ejo ni fa ina tunanin anya ba za mu sauya wajen zama ba? Tsaro da kwanciyar hankali sun yi qaranci a wajen nan, gamu da Yara qanana Ina Jin tsoron wannan rikicin da aka fara Kar abun ya yi tsanani kamar yanda akai waccan shekarar'

'Malam kamar ka shiga zuciya ta, Ina matuqar Jin tsoron yanda na ji kana bada labarin hasalar da mutanen mu suka yi akan wannan lamarin,gashi Suma bangaren makiyayan ba dama'

'Allah dai ya yayyafa wa wannan lamarin ruwan sanyi, gobe zan ga yanda za a yi in shaa Allahu'

'Allah ya Kai mu'

Malam Sabi'u ne ya juya ya kalli Muido da ke miqa wa Addah Petel  'yar tsanar da ya sassaqa Mata ya na tsokanar ta da babbar banza, Yara su yi Wasa da 'yar tsanar itama ta yi,cikin kulawa Malam ya kira sunan Muido ya ce,

'Ka na ji na ko?'

'Eh Baffah Ina Jin ka'

'Nashe gobe Kar a fita da chanun nan ko Ina Kai ma Kuma ka samu waje ka zauna da qannen ka a gida Kar ka je ko'ina mu jira mu ga me zai je ya zo'

'To Baffah Allah ya kaimu'

Da haka suka ci gaba da hirar su kafin daga baya kowa ya kama abinda zai yi.

Washegari da asuba Malam Sabi'u ya dawo daga masallaci ya ga rugar ta yi shiruuu ba mutane a waje sosai, jikin sa ne ya yi sanyi, sannan ya qara tabbatar wa da kan shi barin wajen nan shine ya fi alkhairi a wajen shi da iyalan shi, dan haka da ya Isa gida za su fara Shirin tashi daga rugar.

KYAKKYAWAR FAHIMTAWhere stories live. Discover now