Free Episode
*Her🧕🏻*
Ya dago kai yana kallona da fuskar mamaki, nayi sauri na mayar da nawa idanuwan kasa tare da rike numfashi na dan na san abinda zai biyo baya "Mukhtar?" Ya tambaya cikin mamaki "Mukhtar fa kika ce? Are they blackmailing you? Cewa suka yi in baki aure shi ba zasu gaya wa duniya abinda kika aikata?" Na fara girgiza kaina amma ban ce komai ba, na fahimci dama tunda yana jin zafin uncle Ahmad dole zaiyi retaliating akan zabin nawa duk kuwa da cewa shi ne da kansa ya lissafa min har da Mukhtar din a cikin options dina. Amma ban dauka zai dauki zafi haka ba.
Cikin fada ya sake tambaya ta "baki bani amsa ba, are they threatening you?" Mommy ta shigo da takardu a hannun ta, ta tsaya tana kallon sa sannan ta kalle ni cikin alamar tambaya, ban ce komai ba ta mayar da tambayar ta kansa. Cikin dacin rai ya nuna ni yace "wai Mukhtar. Wai Mukhtar zata aura"
Ta zame ta zauna akan kujera tana dafe kirjin ta "na shiga uku ni Sa'adatu. I thought you hated that guy. You said it yourself several times." A hankali nace "I never hate him, he is my cousin. I just don't love him. Kuma har yanzu bana son sa. Bana masa soyayya irin ta aure amma duk kunsan cewa shi yana so na and at least that is something". Mommy ta nuna waje da hannun ta "and so does Mustapha. In dai soyayya ce Mustapha yafi Mukhtar son ki. Yafi su son mahaifin ki da yanuwanki. Yafi kowa dace wa da auren ki. Da kika ce ba zaki aure shi ba na dauka Abdul zaki aura knowing fully well cewa ba kya son auren Mukhtar. Ashe zaki iya zaben wanda kika ambata xewa ba kya so akan Mustapha? Gwara kikai kanki inda na tabbatar ba son Allah da Annabi suke miki ba akan ki zauna a inda za'a fi ko ina mutunta ki?.........."
Ta cigaba da fada muryarta har shakewa take yi yayin da ni kuma na saka hannayena biyu na toshe kunnuwana tare da rintse ido na. Da bi ar da nake yi a duk sanda ake kokarin chanja min ra'ayi akan abinda na riga na yanke shawara akan sa. Sai da naji na daina jin muryarta sannan na dube ido na ina kallon Daddy shima yana kallo na idonsa cike da mixed emotions. "Wani abun Ahmad ya gaya miki a waya sanda ya kira ki wanda ya saka kika yanke wannan hukuncin?" Ya tambaya muryarsa da sanyi akan dazu.
Na girgiza kaina tare da goge hawayen da bansan sanda na fara zubar da su ba nace "bani da wani zabin ne Daddy. Ba zan iya auren Mustapha ba. Abdul baya sona. Bazan iya auren wanda nake so ba. Bani da zabi Daddy" ya gyara zamansa "waye wanda kike so ɗin? Ki gaya min waye shi ni kuma zan aura miki shi in dai har na bincike shi naga ya chanchanta. Zan aura masa ke kuma in mayar masa da ɗan shi. Waye shi?"
Na mike tsaye "ba ɗan shi bane ba Daddy. Ba ɗan shi bane ba. Ban san waye uban ɗan ciki na ba amma ba nashi bane ba. Ba zan makala masa laifin da nake da tabbas ɗin ba shi ya aikata ba. Ba zan bata tsakanin sa da iyayensa in kuma bata masa suna a gari ba"
Ya dafa kujera ya mike shima, bacin rai yana sake dawowa fuskarsa "kina da shaidar cewa ba shi bane ba kenan? In har ba ki san waye ba zai iya zama shi ɗin ne kenan. Wato da ki bata tsakanin sa da iyayensa gwara ke kin bata da naki iyayen ko? Da ki bata masa suna gwara kin bata naki sunan kin zauna da tabo na har abada a tare da ke, gwara kin auri wanda ba kya so wanda shima kuma ba son Allah da Annabi yake yi miki ba, gwara kin zauna da ɗan da in ya girma ya tambaye ki waye ubansa baki da amsar da zaki bashi ko? Gwara kinyi watsi tare da fatali da duk sacrifices da mahaifiyar ki tayi domin ki, domin ki samu kyakkyawar rayuwa ko? She gave you everything, she gave her very life for you". Ya karasa cikin daga murya.
Nace "but I never ask for it. I never ask for any of this. I wish she didn't do what she did. I wish she let me die"
Na juya da sauri na fita daga dakin ina kuka, ina jiyo muryar sa yana kwalla min kira "Safiyya, come back here" ban waiga ba ballantana in koma.
A waje na samu kujera na zauna na kife kaina ina cigaba da rusa kuka na. Har cikin zuciya ta a lokacin fata nake ina ma dai Ammi bata yi duk abinda tayi ba. Da yanzu ban samu kaina a cikin wannan matsalar ba dan ko shakka babu abinda tayi din shine silar shiga ta halin da nake ciki.
YOU ARE READING
Safiyyah
RomanceCome, let me tell you a story, a story of a man and a woman both blessed and also doomed. Let me tell you a story of love, of a heart crying out for love, reaching out for love, only to be grabbed and pulled away by cruel hand of destiny. Come, let...