A Forever Thing

1.5K 43 12
                                    

Free Episode

Salam all 🙋🏻

This is the last Free Episode of Safiyya.

To continue this journey with Safiyya and Gidado send your 500 naira to

0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access Bank

Sai a tura evidence to this number through telegram

0704 203 0419

Posting of paid episodes will insha Allah only be on telegram.

Please in kin turo evidence ta Whatsapp ban saka ki a group ɗin telegram ba to na duba ban ganki a can ba, ayi min magana ta telegram ɗin Please. Nagode.

Nagode da soyayya. It means a lot to me. Nima ina son ku sosai.

Gidado ya karbi shawarar Abba sosai, dan tun da suka yi maganar ya dukufa da yin adduoin neman zabin Allah. Babu dare babu rana. Ya kuma cigaba da shirye shiryen duk da suka kamata na bikin. Yan'uwansa sunzo na kusa da na nesa, maza da kuma mata. Da yake Abba da Mama first cousins ne sai ya zamana yan uwan duk daya ne babu banbanci, duk kuma treatment daya ake basu.

Yan'uwansa samari da suka zo gari suka kuma fahimci a gidan da yaje ya boye kansa duk sai suka tattaro suka dawo gidan, sa'annin Gidado suna bangaren da yake while sa'annin Haidar suma suka tare a bangaren da yake. Gidado bai ji dadin haka ba saboda an takura masa an hana shi zama yayi hira shida zuciyarsa, shi da safiyyan shi. Sai dai kuma a wani bangaren yaji dadin hakan dan cikin kwanaki biyu kacal sai gashi yana hira da dariya sosai a cikin su. Wani lokacin idan suka nutse a cikin hira har mantawa yake yi da cewa wai aurensa ake yi, kuma wai baya son yarinyar da zai aura. Sai dai kuma yana iyakacin kokarin sa gurin danne wa dan baya son yanuwansa su fahimta har suyi ta yayata maganar a cikin dangi. Sai dai kuma yanuwan are making it extra difficult for him. Casually someone would ask him "ina yarinyar nan kuma da ka susuce akan ta kwanan baya?" His answer to that question was always "Allah yayi mata rasuwa" daga haka ba sa sake tambayar sa. In wani ma ya dauko tambayar sai a samu wani ya hana shi dan kar su taɓa wa angon feelings din sa. Sometimes kuma su kan tambaya "wannan gidan na ka ai yafi wancan girma Gidado, me ya sa ka chanja?" And shi kuma ya kan amsa musu da cewa "amaryar ce tafi son wancan". Alhalin ita amarya ko ganin gidan ba ta taba yi ba sai da masu yi mata jere suka je suka yi suka dauko mata pictures da videos.

Gidan da za'a kai amaryar mai kyau ne, dan sosai iyayensa suka nuna masa gata a siyan gidan kamar yadda suke nuna masa gata a komai. Part dinsa daban na matar daban sannan a waje kuma akwai bangaren baƙi maza sannan da part din ma'aikatan gida (boy's quaters). A bangaren sa akwai bedrooms biyu da parlor, a nata bangaren akwai bedrooms uku da parlor. Part din baƙin kuma parlor ne karami da dakuna biyu.

Kamar yadda iyayen ango suka yi kokari wajen kure adakar su akan gidan Gidado haka bangaren amarya su ma suka yi nasu kokarin, dan duk dakunan da suke part dinta babu inda ba'a cika shi da kaya ba, kaya kuma na gani na fada wa da suka yi dai dai kuma suka dace da tsaruwar gidan. Abin har sai da ya bawa dangin angon mamaki, dan a binciken da suka yi wa iyayen amarya basu samu labarin cewa suna da irin wannan kuɗin ba.

A bangaren amarya tun a week to bikin Mommy ta tafi can Katsina suka cigaba da kammala shirye shiryen su, duk wani shiri da za'a yi wa amarya na gyaran jiki anyi wa Safina shi, ita kanta ta san tana da kyau, ta kuma shirya siye zuciyar angon na ta da wannan kyan nata da kuma duk kan wata kissa da kisisina da Allah ya halicci mata da ita. Ta san cewa akwai challenge a gabanta amma kuma ta shirya karbar sa hannu bibbiyu dai har zata samu muradin zuciyarta. Ta yarda da kalmar hausawa da suke cewa mahakurci mawadaci.

Mommy tayi mata shirin duk da akeyi na gyaran amare dan taimaka musu wajen sauke hakkin aure da zai hau kansu, amma Mommyn ba ta san cewa ita ma da kanta Safinar ta gama siyan duk wadannan kayan har ma da wadanda suka fi na Mommyn. A shirye take tsaf da yin amfani da dukkan baiwar da Allah yayi mata wajen ganin ta mallaki Habibin na ta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 24 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SafiyyahWhere stories live. Discover now