Free Episode
Na zame na zauna akan kujera cikin mamaki "aure Daddy? Safina ce zata yi aure amma ni ban sani ba? How? Why? To wa zata aura ma?"
Yace "ba ta gaya miki ba kema? Kuna magana kuma?" Na gyada kai. Na san mun dan samu falling out da Safina kwanan bayan nan, and must issue din mu na san laifi na ne saboda yadda na zama very rude to her a watannin nan, hakan kuma yan ada dangantaka da mood dina da kullum bashi da kyau. Amma ban dauka har zata iya yin aure ba tare da na sani ba. And ko shekaran jiya munyi chats da ita. We even talked about magana ta da Mukhtar.
Nace "muna magana Daddy, amma ko alama bata nuna min ba. Wa zata aura kuma?" Ya girgiza kai "ban sani ba, they didn't tell me and I didn't ask tunda sun nuna ban isa ba. Ba ki san samarin ta ba?" Na yi shiru ina tunani "Safina bata da saurayi. Ni dai ban san wani saurayi da take kulawa ba" na tuno da yadda takan takan yi min kallon zautacciya duk sanda muke tare in taji muna waya da Gidado. Tace soyayya irritating dinta take yi.
"How can she do that?" Na fada a fili. Daddy yace " ba laifin ta bane ba. Am sure Sa'adatu ce zata hana ta fada dan tana so ta bata min rai, tana so ta nuna min nata ikon" nayi ajjiyar zuciya "babu komai Daddy kar ranka ya baci, we don't need them. We can do this alone. Su je suyi mata aure, Allah ya sanya alkhairi. All we have to do now is hire someone, kamar a nurse haka that can take care of you, sai kuma mu nemi a house keeper da zata ke shigowa ko da twice a week ne tana kula da gidan, and I can drive, duk inda zamuje zan iya kai mu" yayi shiru yana kallo na da murmushi a fuskarsa, sai kuma ya girgiza kai "Safiyya kenan. Kin dauka damuwa ta kenan? Wanda zai kula da ni? Damuwa ta shine wanda zai kula da ke idan babu ni. I don't want any enmity between you and them saboda ko babu dangantaka ta jini su yan'uwanki ne, ba na son in babu ni ki rasa wanda zaki yi turning to. Ke ba yanuwan uwa ne da ke ba, and in akayi auren ki da Mukhtar yan uwans sun zama na mijin ki, ke ba older siblings ne da ke ba. In na mutu ya zaki yi?"
Na koma na zauna ina jin wani kadaici yana lullube ni. Tamkar Ni kadai ce a duniya. Ya cigaba "shi yasa da farko naso auren ki da Mustapha, at least it will strengthen the bond between you kuma ba zasu yi spilling secrets dinki ba. And you will still have Ahmad a matsayin uba ba matsayin uban miji ba, zai kuma saka ido ya ga cewa basu cuce ki ba. But now, now I don't know what to do sai dai addu'ar Allah ya kara ara min lokaci"
Na gyara zama "amma Daddy ba ka ganin wannan tafiyar da suka yi suka barmu ta nuna true intentions ɗin su? Ta nuna cewa ba soyayyar Allah da Annabi suke yi mana ba?" Yace "Allah kadai ya san abinda yake ran bayin sa. I don't know abinda ke ran Mustapha, amma na san Sa'adatu is not cruel, stupid but not cruel, she is just scared that she will loose everything" nayi kokarin gane maganar amma ban fahimta ba sai na chanja magana "I still have the twins" yayi murmushi "yes, and they are the more reasons why dole in gyara tsakanin ku kafin in bar duniya, if not, you will loose them too, dan babu yadda za'a yi su juya wa uwarsu baya saboda ke".
Daga nan na tashi na shiga kitchen na hada wa kaina smoothie na zauna ina sha ina jimamin abinda ya faru, har lokacin na kasa yarda wai da gaske Safina ce zata yi aure amma wai daga ni har Daddy bamu sani ba, kuma naji a raina babu abinda nake son sani irin wanda zata aura ɗin, waye shi? Yaushe suka hadu? A ina suka haɗu? Nayi kokarin mantawa da abin in fuskanci abinda yake gaba na amma sai naji na kasa. Na koma daki na dauko waya ta na kira Hassan, dole ai na san twins zasu sani musamman tunda suna Nigeria. Hussein ne ya sauka da murna a muryarsa ya gaishe ni "yaya da ke za'a taho? Kun fasa zama acan din? Mun dauka ai cewa kuka yi sai kin haihu zaku dawo Nigeria" nace "no Hussein ba dani za'a taho ba, kun yi waya da Mommy kenan?" Yace "eh dazu ta kira mu tace gasu nan zasu taso. I thought gaba daya zaku taho ai" nace "a'a, ita da Mustapha ne ka dai, ni da Daddy muna nan" naji chanji a muryarsa "but why? Me yasa zasu taho su barku ku kadai? Gashi Daddy babu lafiya ke ma kuma haka?" Nace "Mommy tace bikin Safina za'a yi. Kun sani?" "Bikin yaya Safina?" Ya mayar min da tambaya ta, nayi ajjiyar zuciya, basu sani ba suma, ya sake tambaya "wa zata aura?" "I don't know Hussein. Actually abinda na kira ku in tambaya kenan, daga ni har Daddy bamu san komai akan auren ba, and it hurts ne that bamu sani ɗin ba" ina jin sa yana magana da Hassan a kusa da shi, sai Hassan ɗin ya karba ransa a bace "but this is not right. Kawai tace mana zata je Katsina tun last two weeks kuma har yanzu bata dawo ba. She didn't tell us anything" nace "babu komai. In sun karaso kwa tambaye su details din sai muji" ya cigaba da fada sai na kashe wayar dan nasan idan ya fara ba dainawa zai yi, shima yayo gadon zuciya irin ta su Daddy.
YOU ARE READING
Safiyyah
RomanceCome, let me tell you a story, a story of a man and a woman both blessed and also doomed. Let me tell you a story of love, of a heart crying out for love, reaching out for love, only to be grabbed and pulled away by cruel hand of destiny. Come, let...