Free Episode
Littafin Safiyya is 500 naira via
0779484494
Nafisa Tafida Usman
Access BankSend the evidence via telegram or WhatsApp to
0704 203 0419
Posting of paid episodes will be on telegram only.
Kwana biyu bayan zuwan su Katsina, Gidado ya saka Safina ta turo masa address ɗin matar da aka ce yaje ya gaisar anan Abuja, sunan ta Hajiya, kuma kamar yadda Safina ta gaya masa mahaifiyar ta ma tana tare da Hajiyar a lokacin. Dan haka ya shirya ya ɗauki Haidar suka tafi tare. Tun daga gate ɗin shiga gidan suka fahimci cewa wannan gidan masu kuɗi ne, real kuɗi, tsohon kudi.
A bakin gate mai gadi ya tambaye su gurin wanda suka zo, Gidado yace "Hajiya, ina fatan tana nan ai ko. Am sure ta san da zuwan mu" maigadin yayi murmushi yace "ko sirikin na mu ne? Tun safe Hajiya tace zata yi bako, tace mai neman auren Safina ne zai zo, ai Mommyn Safina ma tana gidan. Allah ya sanya alkhairi ya sa da mu za'a yi" Gidado ya danyi shiru yana kallon sa, babba ne sosai kuma daga ganin sa kasan ya san jiya ya kuma san yau, irin masu aikin gidan nan da suka zama yan gida. Sai yayi amfani da damar sa yayi kokarin sanin wani abu akan Safina. "ka san Safina kenan sosai" mai gadin yace "sosai ma. Safina ai kamar jika take a gidan nan. Mahaifiyar ta ma a gidan nan ta tashi tun tana karama har aka aurar da ita har yau kuma nan shine gida a gurin ta. Ai yayar mahaifiyar ta ce matar gidan nan. Kuma tunda ita ta rike ta sai ta zama kamar ƴa ce a gidan. Safina kuma kaga ta zama jika ce. Kai kuma ka zama sirikin mu. Allah dai ya sanya alkhairi" Gidado yayi murmushi "na kusa zama. Not yet. Nagode Baba. Ameen. Dan Allah a sanar musu mun zo"
Mai gadin ya bude musu gate suka shiga da mota sannan ya kira wata yarinya da tazo wucewa yace ta je ta gaya wa Hajiya baƙin ta sun zo. "Saurayin safina ne?" Yarinyar ta tambaya cikin rada amma su Gidado sunji, mai gadin ya fara yi mata fada "maza ki tafi aiken da nayi miki, ku baku da aiki sai shegen tsegumi".
Su Gidado suka fito daga motar a tare, Haidar ya zagayo side ɗin Gidado yace "tana nan ne?" Gidado ya kalle shi yace "wa?" Haidar yayi murmushi "ita ɗin dai" Gidado ya bata rai "zaka koma gida wallahi" Haidar yayi dariya "wai naga sai wani bobboye ta kake yi ne. I just want to see her in lissafa mata irin abubuwan da nake so da kuma wanda bana so. Kasan ana gama bikin ku can zan koma. Though ba Safiyya bace ba amma wancan alkawarin bai karye ba. Har na zaɓi daki ma" Gidado yace "tsakanin ku ne wannan, ni ina ruwa na?" Haidar yace "to ai baka haɗa ni da ita ba dan haka akwai ruwanka a ciki, dole kai zan bawa sako ka isar mata. Ina fatan ta iya girki, ina nufin girki irin five stars standard ɗin nan".
Kafin Gidado ya bashi amsa aka yi musu magana aka ce su shiga. Suka jera suka tafi, sai Gidado ya samu kansa da murmushi yana tuno irin soyayyar da take tsakanin Safiyya da girki. She and Haidar would have been friends. She even promised him that. Ya tuna da wani lokaci da tayi wannan alkawarin.
****. ****. ****. ****. ****. ***
Waya suka yi da safe a muryarsa ta fahimci cewa he was stressed. Da ta tambaye shi dalili sai yayi mata complain cewa aiki ne yayi masa yawa a office, har zuwa rana ma da suka kara wayar still bai kammala aikin da yake yi ba. Da yamma sai gata ta baro hostel dinsu ta dauko motar ta tazo har office ɗin sa ta kira shi a waya tace ya fito ya ga wani abu. He complain cewa aiki yayi masa yawa amma shi kansa ya san cewa ba'a cewa Safiyya "no" dan yanzu sai ta saka masa kuka. Dole ya rufe office ya fito ya same ta a mota, ta bude masa gaba tace "get in" ya shiga yana kallon ta "what?" Tace "to ka rufe motar mana so kake mutanen da suke waje su ga abinda zan nuna maka. Sirri ne" yayi ajjiyar zuciya "Piya! Aiki nake yi wallahi. Dole a yau zan gama aikin nan kuma ko rabi ban yi ba. Ko kina so a kore ni ne?" Tace "waye zai kore ka? Abba ko uncle Habib? You own dis school. Oya, close the door" ya jawo kofar ya rufe "yes ma'am" sai kawai gani yayi ta saka mota a giya ta fara tafiya, ya bude ido "what are you doing Piya? Ina zaki kai ni?" Tace "I am kidnapping you, kuma sai an biya ni ransom zan dawo da kai".
YOU ARE READING
Safiyyah
Roman d'amourCome, let me tell you a story, a story of a man and a woman both blessed and also doomed. Let me tell you a story of love, of a heart crying out for love, reaching out for love, only to be grabbed and pulled away by cruel hand of destiny. Come, let...