Free Episode
Assalamu alaikum
Mun kusa gama free episodes insha Allah. And the paid episodes will insha Allah come on telegram. Na gaji da replying cewa ba'a fara payment ba 😅, so zanke including payment details a kasan episodes daga nan har zuwa sanda za'a gama free episodes ɗin.Nagode sosai da kaunar da kuka nuna mini kullum, Allah ya bar mu har gaban abadan. Safiyya will be worth your money and time, that I promise you 💕.
Nayi sauri na mayar da wayar cikin jaka ta dan kar ya ga abinda nayi saving number ɗin sa da shi. Ya fara yi min tambaya game da department din da nake da kuma yana yin da nake ciki, ni kuma nayi masa duk bayanin da nake ganin ya dace sannan na sanar masa da cewa ina gidan uncle ɗina ne, zuwa nake yi kullum. Muna haka aka fara kiran sallar magrib dama yamma tayi sosai, muka tashi ya taya ni tattara takarduna da ba katantawa nayi ba na zuba su a cikin jaka sannan yace "let me take you home" na bude ido ina kallon sa "ya hade hannayen sa "Please" na girgiza kai da sauri "no. In dai ba so kake yau in kwana a gadon asibiti uncle Ahmad ya balla min kafa ba" yace "saboda me?" Nace "in yaga wani ya kai ni gida, ai karshen karatu na kenan. Besides, nazo da mota" yayi ajjiyar zuciya "Finally an baki motar kenan" muka fara tafiya inda nayi packing nace "da kyar. Farko ai bai yarda a bani motar ba tunda na lalata waccan, sai yace sai dai Mukhtar yake kawo ni school kullum kuma yana zuwa yana daukana, ni kuma....." ya bata rai "waye Mukhtar" nace "cousin dina ne, a gidan su nake zaune" yace "ohh, that guy that picked you up the other day?" Nace "yes, shi" ya girgiza kansa "I don't like that" na tsaya ina kallon sa da mamaki "why not. Menene matsalar?" Ya daga kafada "kawai dai. But tunda kinyi mota ai shikenan ko? Yanzu ke kike zuwa da kanki ko?" Nace "yes" and then I saw relief a fuskarsa.
Muka karasa na tsaya a gaban motar ina kokarin dauko key. Yabi motar da kallo, noticing cewa daga ledar ta aka bare ta "wow. Rich kid" nayi murmushi "zaka fara ko?" yace "na daina. But it is a good one. Really. Congratulations" na shiga na zauna nace "thanks". Ya rufo min kofar yace "I will call you, for real yanzu dai" nayi murmushi "i will be glad if you do".
A lokacin duk mu biyun tunani muke munyi hitting jackpot, bamu san cewa kaddarar mu a chakude take da several heartbreaks ba, heartbreaks ɗin da zasu barmu with nothing but bitter sweet memories.
****. ****. ****. ****. ****. ****
Nayi ajjiyar zuciya na ajiye wayar a gefe, da ace a lokacin na san kaddarar da take bi na da ban neme shi ba, da ko ya neme ni ba zan bari ya same ni ba ballantana har in tarwatsa rayuwarsa kamar yadda nayi a yanzun. Na mike na dauko kaya na na saka, doguwar riga mai fadi sosai da hula, ba zan iya tuna rabon da in saka comb in taje kai na ba, na tabbatar yanzu ko na saka comb din ba zai wuce ba, ban kuma san ranar da zan taje shi ba and I do not care.
Na fita na tarar da Daddy suna yin physiotherapy da nurse dinsa, an siyo masa wani machine da zai taimaka masa wajen motsa hannunsa automatically ko da yana bacci ne dan a dan karawa muscles din hannun karfi. Na zauna ina kallon su ina jin yadda zuciya ta take cigaba da karyewa, a duk abinda ya same ni babu abinda yafi dukan zuciya ta kamar rashin lafiyar mahaifina, zan iya sake going through duk abinda nayi going through and more idan da ace in nayi haka zai samu lafiya. Na tashi na koma kitchen na kira Hassan ina son inji ko sun samu wani sabon labarin, a lokacin ne yake gaya min uncle Ahmad ya kawo musu motocin da nace ya siya musu tun kafin in taho, ni na manta ma da maganar dan na dauka ba zai siya ɗin ba, yanzu ma nafi tunanin ya siya ne kawai saboda yaji daɗi na zabi auren Mukhtar akan Mustapha, na tabbatar da Mustapha na zaba da ba zai sayi motocin nan ba sai dai ni insan yadda zanyi in siya musu, suna ta murna, ya bawa Hussein shima yayi ta min godiya, sai na tambaye su labarin su Mommy "ya maganar auren Safina? Any development?" Yace "ana ta shirye-shirye, kamar dai a Katsina za'a yi daurin aure, I don't know ko za'a yi wani event din again a can. Amma naji Mommy tace za'a yi dinner anan Abuja sannan zata yi yini a gidan Hajiya, kuma kamar a Abujan zasu zauna" nace "okay. That's nice. Angon fa? Kun haɗu da shi?" Yace "chafdi. Ni wannan mijin nata already ma bai yi min ba tun kafin in ganshi. Can you believe har yau bai je ya gaishe da Mommy ba? To katsinan ma Mommy tace sun ce bai je ya gaishe su ba. Kin taba jin irin haka?" Nayi dariya "kai Hassan kar ka zama mai yaɗa kananan maganganu mana kamar mace, tunda dai ita tana son kayanta shima kuma yana sonta ba shikenan ba, na tabbatar ai yan katsinan sunyi binciken su kafin su ce sun bashi ita". Sai kuma yayi min maganar abinda yake raina tun tafiyar Mommy "dazu da nayi maganar Hajiya sai na tuna da sakon ta, munje gaishe ta ranar nan tace mu gaya miki ki kirata. Kamar fa itama tana fushi ne akan batun yaya Mustapha. Ki kirata kinji yaya?" Nayi ajjiyar zuciya nace masa zan kirata ɗin, sai dai a raina nasan bani da karfin zuciyar yin hakan, I already have enough problems on my plate.
YOU ARE READING
Safiyyah
RomantikCome, let me tell you a story, a story of a man and a woman both blessed and also doomed. Let me tell you a story of love, of a heart crying out for love, reaching out for love, only to be grabbed and pulled away by cruel hand of destiny. Come, let...