7

5 2 0
                                    

BA DUK ƘYALLI BANE GWAL
(When their heart collide)
CHUCHU JAY✍️
Chapter 7
    NASSARAWA STATE,LAFIYA ,ALƘALI LAYOUT ,GAWON ROAD ,NIGERIA.
    Wasu gidaje ne wanda suke kama da juna cikin Layout ɗin,madaidaitan gidaje ne da kana kallo zaka san masu shi suna cikin Rufun Ashirin Ubangiji,daga cikin ɗaya gidajen kuwa a falon su mai madaidaicin girma Wani dattijon Mutum ne zaune kan kujera ta zaman mutum ɗaya yayi da matan sa gudu biyu ke zaune ɗaya a ƙasa ɗaya kuma a kujerar dake Kallon sa,cike da fitina matar dake zaune kan kujerar wadda kana kallon ta kasan ita ce matar gidan ta biyu tace"Alhaji gaskiya maganar da nayi maka zaka Duba fa,domin na riga da na yanke hukunci tun rasuwar Halisa akan dole za'a yiwa Khafilat Adopting ƴar uwa daga gidan marayu,jifan tsuntsun biyu ne da dutse guda fa ga ladan kulawa da maraya ga kuma samawa Khafilat farin cikin ta,and Idan zan tuna koda Halisa ta rasu da nayi maka maganar ai ka amince,to yanzu gashi nan Halisa na neman Shekaru shida da rasuwa Khafilat ita kaɗai,kuma ai ba yina bane ,da saka hannun ka aka cire mun mahaifa dan ta lalace,Ni fa kaga idan ba zaka  yi Abinda nake so ba zan iya yi wa kaina kaima ka sani yauwa"...da Mamaki Matar dake zaune ƙasan daga gefen Maigidan nasu tace"Amma dai Saddiqa kina bani mamaki,shin wai Ni Saima ba ƴar uwar Khafilat bace ?mene Khafilat ke buƙata baya ga Saima wadda suke jini ɗaya ,baki ganin yafi akan aje a ɗauko wanda ba'a sani ba?jini ɗaya fa yafi ƙarfin wasa,ga Yayun ta nan, yara shida fa muke dasu cikin gidan nan aikuwa Khafilat ta wuce tayi kaɗaici,ga Salman yayan su baki ɗaya ,ga Sultan ga Khalid ,Saima ga kuma ƙanwarsu Samrat,menene kuma ake nema?"cike da rashin kirki mai gidan yace "shin dai Hadiza wani ya kira sunan ki a nan gurin ko?"
"Ka bar Ni da munafukar na ci mata mana,kuma ki cire Khalid daga jerin yaran ki tsinannu tunda bake kika haifa mun shi ba,Sunan Alhaji kawai suke amfani dashi tare amma bayan nan ba wani ƙarin Alaƙa, Allah ma yasa na Alhajin ne ba a yawan ta zubar kika samo ba,yauwa a cirewa yarana bakin miyar kuka kafin naci kan Kazar mutum ehe,wa zaki nuna wa kina da jerin yara huɗu nima cikina ya ɗauki uku kada kiga naki ya ɗauki Biyar har da ɓatatta,abun ai har da satar ƙwana ,".cewan Hajiya Saddiqa tana mai aikin yamutsa fuska.
    Cikin yanayin na gudun kada Alhajin Ya ɓatawa Saddiqa rai yace"a'a dai kin san duk lalacewa dai su Sultan yara nane,yanzu dai kada ki damu ,ina fita yau zanje Babban gidan marayu dake cikin lafiya na samo miki santaleliyar yarinya". saurin ɗaga hannu tayi tace"a'a Alhaji Ni ba a nan garin ma nake so ba,so nake muje gidan Marayu na Alheri dake cikin garin GASHUWA,sannan kuma ina san yarinya dai dai shekarun Marigayiya Halisa ,shekara sha uku kenan ,kaga nima zata na maye mun gurbin rashina ".ɗan shiru mai gidan nasu yayi yace"mene yasa sai Wannan gidan marayun?GASHUWA chan yobe fa kenan"wani mugun kallo ta bashi kafin tace"kaga malam Ni bance dole sai kaje ba,Zanje da ƙaina ƙanwata Sakina ta raka ni dama ai gidan marayun na mijin ta ne,kai bana so ma kaje ,da kaina zani".Komawa inda take Yayi yace"naji Matar arziƙi dan Allah ki saki ranki, zuwa ƙarshen watan nan kinga ai ya kusa ƙarewa da kaina Zanje na taya ki zaɓar duk irin  yarinyar da kike so"wani shagwaɓewa tayi tana mai kai masa dukan wasa a ƙirji cikin wata irin maƙirar kissa tace"ina sanka Alhaji na" ...da mugun  takaici uwar gida Hadiza tace"Ni Alhaji shin mene dalilin kira na da kayi, naji wai na tafi ko na baku guri".sheƙeƙe Saddiqa ta kalle ta tace"tashi kije dama Ni nace ya kiraki  dan ki sake sanin matsayin ki"..da mutuƙar jin zafi Hajiya Hadiza ta kalli Saddiqa tace"na gani ba sai kin kira Ni nan zan gane matsayi na ba ai,na sani amma ku abinda baku sani ba shine idan Ubangiji nasan mutum kada ka kuskura kai ɗan adam kace zaka wulaƙanta sa,Abunda kuke ke da Alhaji kuma ,akwai ranar ƙin dillanci"tashi tayi bayan ta ƙare maganar ta idanun ta na neman kawo ƙwalla tana mai tuna lokacin da take mace mafi soyuwa gurin Alhaji Bukar Mamman ,ita dashi dukkannin su mutanen Nassarawa ne sannan Auren su anyi shi ne bisa zumunci ,ita diƴar mace shi ɗan namiji, lokacin da suka yi Aure ba ƙaramar soyayya suke yiwa juna ba dan kowa a dangi maganar su yake iyayan sa kuma masifar santa suke yayin da ita a nata bangaren marainiya ce bata da kowa baya ga shi da iyayensa sai ƙanwarta guda ɗaya Wadda ke Aure a jihar Kano ,haihuwar fari tsakanin ta dashi ta haifi Salman wanda a yanzu yake da shekaru Ashirin da ɗaya iya adadi na kimanin tsawan Auren su,bayan Salman ta haifi Sultan wanda a yanzu yake da shekaru   sha takwas,sai Saima mai shekaru goma ɗaya sai kuma Autar su Samrat mai shekaru Biyar a yanzun, Saima da Khafilat yarinyar Hajiya Saddiqa sa'annine domin tare akayi goyan cikin su ,Khalid kuma Sultan ya basa shekara Guda inda shi a yanzu yake da shekaru sha bakwai.. Halisa wadda Hajiya Sadiqa ke magana ɗiyar ta da ta rasa da ace tana da rai a yanzu za tayi shekaru sha uku tsakaninta da ɗiyar Hajiya Hadiza wadda ta ɓace kuwa ƙwana ɗaya ne..mafarin tashin hankalin Hajiya Hadiza ya fara ne daga ranar da Alhaji yayi tafiya zuwa Bayelsa state ,abun mamaki da takaici bai tashi dawowa ba sai da Saddiqa akan cewa abokiyar karatun sa ce tazo wani aiki Arewa kuma bata da gurin zama shi yasa ya taho da ita gida,kasancewar ta mace mai haƙuri da fahimta sai bata ja abun ba har tayi ƙokari wajen rufe masa gurin Mahaifiyarsa akan cewa Saddiqa ƴar uwarta ce,kafin fa ta farga sai wasa ya chanza ,fafur ya nuna mata san Auren Saddiqa wadda ke Bin ta sau da ƙafa ,a lokacin watanni ta huɗu a gidan cikin Sultan kuma wata Uku, ba tayi yi yunƙurin hana sa ba ko masa gardama domin gudun Fushin Ubangiji tunda shine ya halarta Auren Mace huɗu ga namiji, sosai ta bawa zuciyar ta haƙuri ta maida Ubangijin ta wanda ta bawa zabin ta,duk yar da NENE Mahaifiyar sa ta nuna baccin ranta Musamman akan boye mata wacece Saddiqa da tayi bai hana ta ƙoƙarin waje shawo kanta ba akan ta yarda da Auren tayi haƙuri suyi Addu'a tunda a zaman ta da Sadiqa bata san halin ta na banza ba sai masu kyau.
    Bata fara sanin wacece Saddiqa ba sai da ta Aurar mata miji,abu rumi rumi yana tafiya kamar wasa Alhaji Bukar ya fara chanza mata zuwa wani mutum daban da bata sani,abun tun baya damun ta har ya dawo sakata shiga cikin matsanancin Hali Musamman yarda ya samo ɗabiar nuna Halin ko in Kula da yaran ta ,a haka dai suna tare cikin rashin daɗi har ya Kaiga ta samu wani ciki  bayan Sultan shekaru biyar da suka gabata kasancewar Alhajin yakan zo biyan buƙatar sa idan Sadiqqa bata nan, to a wannan karan ma taje ziyarar gida Bayelsa,.lokacin da ta kula da cikin ta shiga tashin hankali sosai dan ta gama ƙudira a ranta Hajiya Hadiza ta gama haihuwa da Alhaji, lokacin ita ma tana ɗauke da cikin Halisa ,wani tashin Hankali bai fara a gidan ba sai da Hajiya Hadiza ta haifi jaririyar ta inda itama Hajiya Saddiqa ta Haifo ɗiya mace amma ko a yanayi na jarirantaka ɗiyar Hajiya Hadiza tafi ta Saddiqa kyau sosai wanda hakan ya sake tunzura Saddiqa take ta neman hanyar da zata bi tayi maganin abun gashi Malamin ta ya gargaɗeta akan kadda tace zata gwada yiwa Hajiya Hadiza Asiri bayan wanda suka mata yayi backfiring ya Basu babbar matsala wadda ta rufe a ranta ita kaɗai dan ko ƙanwar ta Sakina da suke ciki ɗaya bata faɗa wa ba duk da kuwa yarda take bata boye mata komai,dalilin hakan yasa ta maida ragamar Ashirin ta kan Alhaji wanda duk yarda ya kai ga kama sa baya iya ƙin biyan buƙatar sa da Hajiya Hadiza amma fa sai a boye..wata guda da haihuwar Hajiya Hadiza aka nemi Jaririyarta mai suna Ni'ima aka rasa ,ko sama ko ƙasa haka aka neme ta babu labari,sosai Hajiya Hadiza ta shiga tashin hankali musamman da ya zamana Saddiqa ta kintsawa Alhaji kan cewa kuɗin jini ta bada ayi da ita inda shi kuma cikin yanayi na toshewar fahimta ya yarda har ya kai ga ya saki Hajiya Hadiza Amma Saki ba shine Saddiqa ke so ba ,tafi so Hajiya Hadiza ta zauna gidan nata tana ji kuma tana gani ta rasa Soyayyar miji da ita da yaranta,ita da kanta ta wanke ta tasa ya dawo da ita dan a cigaba da gashi, neman Duniya Alhaji yayi ma Ni'ima amma abun yaci tura inda daga bisani ya fawwalawa Allah yayin da ita ma Hajiya Hadiza tayi amma ta aminta da cewa muddin Ni'ima na raye Allah zai Turo mata da ita inda take..
*******************************************
  GIDAN ALHERI
    Kuka wiwi Nafisa take zaune a ɗakin su Khadija na rungume da ita tana bata haƙuri amma abun yaci tura kamar ana ƙara mata fetur,ɗagowa tayi tana mai zuƙar majina tace"yanzu kuna ganin Anmun adalci kenan,inaji ina gani Boda Akram ya wuce Yankee ya bar ni ,Kuma bai tashi tafiya ba sai da Safiyya? Ina kuke san nayi shiru,dan Allah ku haɗa wuta ku sani na huta da abun da nake ji"Hama uwar tausayi ce ta goge hawaye dake maƙale gefen idanunta ta matsa kusa da ita ta zauna tana mai kamo hannun ta tace"Dan Allah Nafisa ya isa haka,ina ce shi Brother Akram ɗin yace miki zai zo ya ɗauke ki mene na kukan nan,dan ya tafi da Safiyya kuma mene ita ma karatu taje ,idan kema kika dage ba sai ki bisu ba ƙoƙari kawai zaki ƙara".raba jikin ta tayi dana Khadijah ta kalli Hamamatu tace"kinji ai Hama ai matsalar Abunda Big Mummy ta gama faɗa mun kenan , nothing dey enta my bren,babu, duk abinda zanyi shine Abunda ke kara suya mun rai,turancin ma babu ta ina zan fara?"...Suwaiba dake tsaye tana tsoran magana ne tace"kiyi hakuri dan Allah Nafisa".kamar Nafi na jira ta miƙe tana mai cewa kada ki samun baki Suwai wallahi yanzu naka miki shegen bugu,dama ai abun da kike so kenan ,ina cewa kince baƙin cikina yana saki nishaɗi,to ga yanayi na nishaɗi nan kiyi amma kada ki sake bani haƙuri,shiru Suwaiba tayi dan tun Abinda ya gitta tsakanin su sama sama Nafisa ke amsa ta shima dan Big Mummy da Mummy Nadiya sun hana su gaba.basket ɗin da suke tara wanki ta kalla kafin ta maida kallon ta kan Khadija tace", sister Khadija akwai sabulu cikin drawer ɗin chan?..kaɗa Mata kai khadija tana mamakin sister da ta kira ta da shi.
Drawer ɗin ta nufa ta ɗauko sabulun wanki da Omo ta saka cikin ƙwandan ta fara ja ta fita,Kallan ƙofar Hama tayi tace"kada kice mun wankin mu duka Nafisa zata je tayi?and Ni kaɗai naji kamar sister ta kira ki yaya Dije". tashi Khadija tayi tace kuzo mubi bayanta muga ikon Allah.

TBC

Short chapter kuyi maneji..

BA DUK KYALLI BANE GWALWhere stories live. Discover now