(When their hearts collide)Kallan Suwaiba dukkan yan Ajin suka juyo suna yi saboda kowa yasan ita ce ke zama ƙarshe wajen bada hadda saboda tsabar rashin yarda da kanta,ɗan murguɗa baki tayi ganin duk Attention ya dawo kanta tace"meye ne kuke wani kallo na kamar yau na fara bada hadda a farko".dariya sosai Nafisa tasa kafin tace"babu wanda yayi magana gashi kin bawa kanki Amsa ,kuma kafin kice wani abu dama Ni bance nafi kowa ba zan bada a ƙarshe na ƙara tisa karatu na shima hikima ce"dariya Yan aji suka saka wanda yasa malam Muhammad gyaran murya yace"ina fatan kun san cikin aji kuke ina san ku girmama kan ku domin kuwa bana so mu shiga taƙun saƙa da kowa,Malama Bismillah"ya maida maganar sa kan Suwaiba wadda ta ƙarasa gurin tana faman murmushi ,zama tayi gefen da suke zama idan zasu bada Haddan kafin tace"malam Barka da zuwa Ajin mu ,ya kamata kuma ace muma kasan sunan mu, sunana Suwaiba Umar,shi Umar ɗin ba wai sunan Baba na bane tunda nima ban san wane baban nawa ba,na zaɓi sunan ne domin ya kare mun yawa sannan kuma..".."ke karatu zaki bada ko tarihin ki"Malam Muhammad ya katse ta cikin taushin Murya, dariya yan Ajin suka saka lokaci guda kuma kowa yayi tsit kafin Suwaiba ta fara karatun ta cikin borin kunya.tun da ta fara karatun ta ɗauki wayar malam ɗin ta saka cikin Hijab ɗin ta, bayan idar da haddar da aka sha tataɓurza ta miƙe a hankali wayar na hannunta ta doshi sashen da Nafisa ke zaune,kafin ta kai ga ƙarasawa ringtone ɗin wayar ya karaɗe Ajin yayin da yake fitowa daga jikin Suwaiba Wadda ta maƙale a tsaye idanun ta a runtse,da Mamaki Malam Muhammad ya kalle ta yace"kamar ring tone ɗin wayata ne wannan a cikin Hijab ɗin ki ko Suwaiba Umar?"baki ɗaya Ajin yayi tsit kowa ya mayar da Kallan sa kan Suwaiba wadda
Idanun ta ke rufe sannan ta kasa bawa malam Amsa,tasowa yayin yazo inda take ,hannunsa ya miƙa Mata yace"ki buɗe idanun ki, ki bani waya ta sannan sai ki faɗa mun dalilin da yasa kika ɗauka ,mene kuma zakiyi da Ita,amma kafin nan Namiji ɗaya ya tashi yaje ya kira mun Malam Shu'aib"da gudu ɗaya daga cikin maza Ajin ya miƙe dan zuwa kiran Malam Shu'aib tsohon malamin su.a hankali Suwaiba ta buɗe idanun ta da suka fara zubar hawaye zuwa kan kuncinta , wayar ta ɗora masa akan hannun sa kafin ta fashe da kuka tace"dan girman Allah Malam ka rufa mun Asiri, ALLAH Ubangiji ma yana san mai rufa ma wani Asiri shima sai ya rufa masa ni wallahi ba ɓarauniya bace,ban iya ɗaukar Abun wani ba ka tambayi kowa ,dama dai Nafisa ce".Tashi Nafisa tayi tana mai faɗin"kan Uba?Ni kike cewa dama nice,hala nice na duƙa ba tsoran Allah na ɗauki wayar nan,ko kuma nice na Aika ki".cikin Sauri Suwaiba tace"Wallahi malam itace tace na ɗauko, ni ba halina bane"a hankali malam Muhammad ya kalli inda Suwaiba ta nufa da wayar ,tabbas saitin Nafisa ne dan kiris ya rage ta kai gare ta,gyara tsayuwar sa yayi yana mai Kallan su kafin yayi ƴar dariya yace"to Naji itace tace ki ɗauko amma tayaya ta faɗa miki bayan ba guri ɗaya kuke zaune ba ,ba Kuma ba nace tun kan kuzo Aji ba dan Ni kaina ban san da zuwa na ba".cikin Kuka Suwaiba tace"a paper ta rubuta min ta cilla mun ".da Mamaki yace"ina paper ɗin"."Na cinye"ta bada Amsa cikin sauri "Sa'adatu da tsoro duk ya cika ne tace"kai Suwaiba kiji tsoran Allah ,ina nan zaune kusa dake fa tun ɗa zu,Ni banga lokacin da Nafisa ta cilla miki paper ba". shigowar malam Shu'aib da Isma'il da Akram shine ya katse hanzarin kowa,komawa Malam Muhammad yayi yana mai faɗin"gata nan Malam ta faɗa muku Abunda tayi"kallan Nafisa dake tsaye Akram Yayi yace"ke da kike riƙe da ƙugu gaban manyan ki ɗa'a kenan?"cike da takaici tace"yo Boda Akram ba dole na riƙe ƙugu ba Suwaiba na mun sharrin da tunda nake ba'a taɓa mun irin sa ba,wai na rubuta mata a takarda ta saci wayar malam ta kawo mun".cikin Kuka Suwaiba da bakin ta yaƙi mutuwa tace"to ƙarya nake ne,kece nan kika ce na ɗauko"."muyi uwarki da ita "Nafisa ta faɗa a fusace tana fitowa daga inda take.tsawar da Akram ya daka mata shine Abunda ya tsayar da ita,kafin ta farga sai ga hawaye na bin kuncin ta.
Fitar dasu akayi daga ajin jin yarda Suwaiba ta kafe ita kuma Nafisa na ƙaryata hakan,Malam Muhammad dake zaune office ɗin Headmaster na Islamiyyan ne yayi gyaran Murya ya kalli Suwaiba dake faman Gunjin kuka yace"ke kalli nan Suwaiba bana san wannan kukan da kike mun na rashin gaskiya,idanun ki ma ɗauke yake da rashin Gaskiya,ki saurareni nan, wallahi idan baki faɗa mun Abunda yasa kika ɗaukar mun waya ba zan miki abinda da bakin ki zaki faɗa dalilin da yasa kika ɗauka ,muddin kuma kika bari na tilasta ki domin ki faɗa ,to ki cire rai da cigaba da zama a mutum dan sai na mayar dake kunkuru".cike da tashin Hankali tace"malam Kunkuru Kuma?"gyara zaman da yayi ya haɗe rai yace "Kunkuru kuwa kuma haka zaki mutu babu mai iya dawo dake,idan kuma kina ganin wasa nake dan Allah ki bari nayi abinda nayi niyya"rufe idanunsa yayi yana motsi da bakin sa,ganin haka yasa Suwaiba rarrafawa inda yaƙe tana Kuka tana cewa"ɗan Allah Malam Kayi mun rai wallahi zan faɗa kada ka mayar dani Kunkuru,nice na ɗauka babu wanda ya saka ni,kawai ina so ne na saka cikin jakar Nafisa ne na ƙala mata sata".da Mamaki kowa dake gurin ke kallan Suwaiba ciki har da Nafisa da ta mutu a tsaye,Malam Shu'aib ne ya tako inda take yace"Suwaiba dan mene kike so ki ƙalawa Nafisa sharri?ina ce ɗakin ku ɗaya ,shin wani abu tayi miki da ya miki rashin daɗi da har kike san tozarta ƴar uwar ki haka?"ƙasa tayi da kai tana mai goge hawaye tace"Ni Malam ba Abunda tayi mun kawai ina jin a zuciyata wani abu a kanta mara daɗi ,ina ji kuma idan ban saka ta cikin baccin rai ba bana jin daɗi,idan nagan ta cikin Hali mara kyau sai ina jin farin ciki,Ni Ko Rashin lafiya take daɗi nake ji ban san mai ya sa ba". ƙarasa maganar tayi tana mai rushewa da kuka...riƙe haɓa Nafisa tayi tace"kan Uba, Suwaiba kawai ki daina wannan dogon Yaren kice baki so na kina san na Mutu kuma wallahi jikina yana bani sai kin rigani mutuwa ,kina Kallo kuma a duniya zanyi nasara kina sharar titin tunda de ke ba mutum bace,dama ai na faɗa ke munafuka ne wallahi mutane ne basu sani ba kowa ya saka Ni gaba". Headmaster Kabiru ne ya umarci Nafisa da tayi shiru baya san jin maganar ta kafin ya kalli Suwaiba yace"Suwaiba Ni bazan sa a dake ki ba amma ina so ki sani ita hassada ga mai rabo taki ce, sannan duk yarda kika so da ƙin Nafisa babu abinda zaki iya tunda Allah ne yayi mu baki ɗaya kuma shine ke da hukunci a kan mu lokacin da yaso,ke kanki nasan kin san Abinda kikayi bashi da kyau,kina ƴar Ƴarinya dake amma kina da irin wannan ƙiyayyar a ranki ina ga kin girma?a nan gidan baku da kowa sai juna idan kuka ƙi junan ku shin wane zai so ku?dole ne zaku fara da san junan ku kafin ma wani ya so ku,shi shaiɗan muddin muka ce zamu dauki zugar sa wallahi baza mu gani da kyau ba, Alhamdulilah amfanin nan ɗin ai dama dan ayi kuskure a gyara ne,shin kin gane laifin ki?"Saurin ɗaga kai Suwaiba tayi tace"wallahi malam na gane kuma bazan sake maimaita Abu makamancin haka ba,dan Allah Malam Muhammad ka yafe mun,kema Nafisa ki yafe mun wallahi bazan sake ba.shiru Nafisa tayi tana mai kawar da kanta musamman ganin irin Kallan kurillar da Akram yake mata wanda yasa take jin haushin sa dan gaba ɗaya yau babu abinda yake sai ɓata mata rai,koda tace ta haƙura a nan wallahi bata haƙura ba sai anyi wata Shari'ar gun Big Mummy ,ko dai a sakewa Suwaiba ɗaki ko kuma ita a sake mata..."Kin haƙura ai ko Nafisa"Akram ya faɗa yana Kallan ta,taɓe baki tayi tace Na haƙura malam zan iya tafiya?. Malam Shu'aib da take tambaya ne yace zata iya,bata sake bin takan kowa ba ta bar ofishin,Bin ta da sauri Akram Yayi dan yasan Nafisa Farin sani ba haƙurin tayi ba..kai tsaye Ajin su ta nufa domin ɗaukan jakar ta ,tana shiga kuwa kamar jira yan Aji suke suka fara tambayar ta abinda ya faru,ba tare da ta damu ba tace"sharri ne ta mun,ashe Ni zama nake da maƙiya ta Suwaiba ta tsane ni ban sani ba"ƙwafa tayi ta fita a Ajin ta bar su suna mai da yarda akayi,tana fita bakin Ajin taci karo da Akram,giftawa tayi zata Wuce sa ya kamo hannu ta ya jata suka bar gurin, ƙoƙarin ƙwacewa ta fara amma yaƙi bata damar har sai da suka fita daga cikin Islamiyya kafin yace",Kalle Ni nan Nafisa"haɗe rai tayi sosai tace"Ni Boda Akram ka rabu dani dan wallahi yau duka haushin ka nake ji,daga mari sai kuma tsawa,ɗaya dan kawai na ganka kana cin amana ta ɗaya kuma dan kawai ina nemawa kaina yanci na shi kenan ka hau yi mun tsawa,Ni ka rabu dani na tafi".cike da nutsuwa yace"Ko mene kika ga nayi Nafisa domin ke ne, marin ki dan bana san Safiyya ta kai ki ƙara ne , yanzu kuma bana san a miki kallan mara tarbiyya, Amma na ji ki yi haquri"ɗan taɓe Fuska Yayi wanda yasa tayi saurin faɗin"kai Boda Akram mene hakan kamar wani yaro Ni ka bari"dariya yasa yana mai ƙarawa yace"indai zaki yafe mun naji Ni yaro ne,and ni Safiyya ba budurwa ta bace mene zanyi da ita ina da cika kamar Feenah"lakace mata hanci yayi da ya kai ƙarshen maganar wanda yasa ta rugawa da gudu tana dariya cike da kunya.kaɗa kai yayi a hankali ya furta "Nafisatu ikon Allah".
Bangaren Suwaiba kuwa sosai Malaman suka yi mata Nasiha sannan Headmaster ya bata hukuncin sharar makarantar na sati guda wanda ta fara a ranar ,kai tsaye bayan Nafisa kuwa ta koma sashen Big Mummy ta nufa dan tana kan bakar ta na ba zata zauna ɗaki guda da Suwaiba ba kada ta
Kashe ta cikin dare ,zayyanawa Big Mummy Abunda ya faru tayi wadda bata yarda ba a cewar ta sai Suwaiba tazo taji ta bakin ta tukunna wanda hakan ya shaƙawa Nafisa ainun.bayan dawowar Suwaiba Big Mummy ta Kira su baki ɗaya har da Khadijah da Hamamatu,yarda Nafisa ta zayyana mata haka nan Suwaiba ta zayyana dan ta ƙarya ta ƙare,da mutuƙar Mamaki Big Mummy tace"yanzu Suwaiba har kin san zafin kiyayya haka?"sunkuyar da kanta tayi tana kuka yayin da Nafisa ke faɗin ita dai wallahi sai an raba musu ɗaki,da ƙyar Big Mummy da Mummy Nadiya wadda ta shigo taji ana abun suka shawo kan Nafisa akan Sulhu za'a musu tunda dai Suwaiba tace baza ta ƙara ba,Mummy Nadiya ce ta ƙara da cewa"dole ne dama a zaman tare a fuskanci haka,idan akace raba ku za'ayi ta ina zaku gyara?dole ne ku gyara kuren ku a tare"a haka dai suka sallame su bayan Nafisa tayi alƙawarin bazata ta bari faɗa ya shiga tsakanin ta da Suwaiba ba amma fa baza ta manta cewa Suwaiba ba abokiyar ta bace.
*******************************************
" Safiyya Ni ban san mene matsalar ki ba muddin akace abu ya shafi Akram ya kamata ace kin farka tun wuri fa dan hakan bazai haifa miki ɗa mai ido ba , yanzu dan Allah ki kalli bakin ki yarda ya kumbura saboda Nafisa sannan wai Akram yace miki kada ki kai ƙarar ta saboda wasu lame alƙawaruruwan da baki da tabbas idan zai cika,wake up girl ki farka"ƙawar Safiyya Rabi'ah ta faɗa tana mai duban Safiyyah..Murmushi Safiyya tayi ta dafa ta tace"Rabi'ah kenan ,ke shaida ce yarda na dage babu wasa wajen ganin na cike gurbin da ya kamata ace gidan nan sun kaini waje karatu,kina kallo ai bana yiwa karatu wasa ,to dalilin mene nake hakan idan ba dan Akram ba?ina mutuƙar san Akram kema kin sani , wannan haƙorin kuma da ya karye tikiti ne na sake samun kusanci da Akram,yayi Alƙawarin kulawa dani na shekara guda ni kuma ina faɗa miki zai kula dani ne har ƙarshe rayuwar mu,shin wacece Nafisa?wata ƙaramar marainiyar yarinya ce fa wadda bata da komai da zata bada, She's just Young ,shitty and lame poor girl wadda take hauka akan Akram kafun ta gama sanin menene so ɗin ma, kawai obsession ke damunta ,ki yarda dani Muddin jirgin mu ya ɗaga ni da Akram daga ƙasar nan to labarin Nafisa kuma ya ƙare"..Ajiyar zuciya Rabi'ah tayi tace"Allah yasa Ni fata na ma cikin masu Adopting na Shekarar nan wani ya ƙwasa alaƙaƙai,yarinya duk tabi ta Addabi jama'a ,na godewa Allah ma Aure zanyi na bar gidan ,me ake da Nafisa".Kallon Mudubi Safiyya ta cigaba tana murmushi dan taci alwashin mantar da Akram Nafisa ta hanyar basa Support a duk inda yake buƙata,tafi kowa sanin Akram sannan abubuwa da dama nasa da yake faɗa mata tasan bazai faɗawa Nafisa ba ,After all babu wani abu da zata fahimta a ciki ballan tana ta bashi wani goyon baya,duk inda aka je aka dawo itace dai SAFIYYA.
Please vote, comment and share
To be continued
BINABASA MO ANG
BA DUK KYALLI BANE GWAL
Romance(When their world collides) Rayuwarsu tayi kamanceceniya, lokaci guda kuma komai yayi ƙokarin tabarbarewa sabida gaskiya akan al'amarin rayuwarsu, ita marainiya ce a yarda ta sani ,wadda aka tsinta a bakin hanya ,shin mai zai faru idan tasan cewa iy...