Kai tsaye ɗakin su ta wuce tana mai jin ran ta yayi sanyi,babu sallama ta shiga domin kuwa duk da cewa tayi alƙawarin baza tayi faɗa ba bashi ne ke nufin bata daina jin haushin mutanen ɗakin ba har da wanda bata shafa ba, babu wanda ta tarar cikin sai mara mutuncin ƙawar khadija ,Asiya zaune gefen gadon ta wanda kana kallo kasan kwanciya tayi a kai yarda zanin gadon yake very unkept, Kallo ɗaya Nafisa tayi mata tayi ƙoƙari wajen danne Ashar ɗin dake neman taso mata domin kuwa ta tsani ta gyara gadon ta a hau bugu da ƙari ma a rasa wane zai hau mata sai Asiya wadda ƙwataƙwata bata ƙauna,tashi Asiya tayi daga kan gadon tana mai cewa,ɗan zo ki gyara ban san ma bacci ya ɗauke Ni ba ,kin san saboda tsantsar san kai ɗakin nan katifar ki tafi ta kowa laushi,Zuciya ke neman ɗaukar Nafisa amma tayi ƙoƙari wajen ganin ta danne ta tana mai gudun sake zuwa ɗakin horo,a yau ɗaya abun ya isa haka dan tasan wannan karan idan ta koma kuma kilan Big mummy tayi mutuwar da take faman kirawo kanta dan haka kawai ta nufin gadon ta gyara sannan ta doshi hanyar Bathroom.cike da jin haushin ƙin kula ta ɗin da ba tayi ba Asiya tace"Ɗan uwarki wane kike sharewa haka?shegiya Annoba kawai kinbi kin ishi mutane kamar nan ɗin gidan Uban ki ne,Allah ya taimake ki ki shiga sabga ta dan wallahi illa zan miki Babba kada kiga kina da ɗaurin Gindi Ni kunce sa zan.still Nafisa bata kula ta ba ta shige bayin domin yin uzurin gaban ta , baki Asiya ta saki da mamaki ganin Nafisa bata kula ta ba a Nafisan da ta sani kuwa yanzu da ta maida mata martani,sallamar Khadija ne ya katse mata Hanzari,Murmushi Khadijah tayi tana ganin Asiya tace"kin tashi kenan,gwara dai da kika tashi kika gyarawa Nafisa gadonta kafin ta shigo ku samu damuwa "gatsine Fuska Asiya tayi tace"dan na hau gadon Nafisa shine sai na gyara?to uwarta ma tayi kaɗan balle uban ta wallahi tsinanniyar yarinya kawai,Ni Ko wallahi naso ace Nafisa ɗakin mu take ,wallahi sai na gyara mata zaman ta yarda bata tunani.cike da damuwa Khadija tace"Nafisa nada Hali mai kyau fa Asiya musamman idan ka kasance baka shiga shirgin ta sai kiga an zauna lafiya,amma wani lokacin ne idan tana Abu wani mai Aljannun ma ba zai yi ba ,Ni har tsoro take bani wallahi ,ina mutuƙar tausayin ta,yau baki ga duka da Baba Idi Yayi mata ba kamar ya samu jaka ".dariya Asiya tasaa tace"to da Nafisa mecece baya ga jaka?ke Ni fa tunda nake ban taɓa ganin jaka kamar Nafisa ba,yo jaka mana , akwai wanda kika ga An yiwa repeating sau uku cikin gidan nan banda Nafisa,babu wani irin salo na jakan ta da bata iya ba,wane ma ya sani kila a jaka zata zo Allah ya taimaka mata tazo a mutum, wallahi na tsani wannan yarinyar kuma ki rubuta ki aje duk ranar da ta shiga sabga ta sai nayi mata dukan da ya kamata ayi wa jaka irin ta".ɗan haɗe rai Khadijah tayi tace"ya isa haka Asiya dan Allah,ko mai dai lalacewar Nafisa ƙanwa tace bazai iyu kuma gabana kina aibata ta ba har kina Kiran ta da jaka,kin san idan Misali taji ki baza ku zauna lafiya ba,bana so Allah". dariya Asiya tasa tace"Allah Sarki ai ta gama ji,kuma da kike maganar na kira ta jaka ke kika fara siffanta ta kina tsoron ƙarasawa na ƙara sa miki,maganar gaskiya kuma ai jakar ce,beside kike wani kiran ta ƙanwar ki,ina fatan zaki farka ki san inda ke make ciwo domin kuwa tsakanin ki da Nafisa babu wata alaƙa da ta wuce ta gidan Marayu kuma a iya nan zata tsaya bugu da ƙari kuma ba sai na faɗa miki cewa Nafisa ta fiki cikin gidan nan gurin wancan Guzumar matan ba"rufe bakin Asiya ke da wuya Nafisa ta fito a bayin bayan ta gama jin komai , bata tanka ba ta Isa inda Hijab ɗin ta yake ta ɗauka ta fita.da mutuƙar Mamaki Khadijah ta kalli Asiya tace"kina so kice mun tun ɗazu Nafisa ce cikin bathroom ɗin nan amma baki faɗa mun ba kika zauna kina ta zagin ta haka"taɓe baka Asiya tayi tace"to sai mene?sai kina yin wani abu kamar kina tsoron yarinyar nan,Ni da na dasa mata tsoro na kinji ta tanka?gadon nan ina tashi ta gyara bisa umarni na ,ya kamata ace a ɗakin nan kin ɗauki girmanki ki riƙe sa da kyau ba Nafisa ba, ko Hamamatu tayi miki kici uban ta".cike da rashin jin daɗi na abun da Asiya tayi Khadijah ta tashi tana mai cewa "Ni ba ke bace and Bazan boye miki ba Abunda kika yi bai mun daɗi ba"da haka ta fita a ɗakin,bin ta Asiya tayi tana ƙwala mata kira amma tayi mata baza dan tabbas bata ji daɗin ba ko kaɗan.Bayan sallar isha'i kowa yana ƙoƙarin wucewa ɗakin sa Big Mummy ta Kira Nafisa,da baki gaba taje amsa kiran ita ala dole tayi fushi da abinda ya faru da rana,ita kaɗai ta tarar a ɗakin tana jan carbi,daga chan gefe ta zauna tana mai cewa "in wuni chan cikin maƙogwaro".tsayar da jan carbin big Mummy tayi tana mai kallanta tace"lafiya Lau,taso zo nan ki zauna kusa dani,ko fushin ne baki gama ba?"zumɓuro baki ta kuma yi ta dawo ta zauna, murmushi Big Mummy tayi tace"A rayuwar nan Nafisa dole ne ka koyi hali mai kyau yarda idan wani yace kayi abu mara kyau wanda ake faɗawa ɗin yayi saurin ƙaryata wa,amma muddin kuwa kace Hali guda zaka riƙe na ƙin jin magana ko mene akace kayi ta kayi fa sannan babu wahalar yarda tunda ansan halin ka ne, yanzu misali Abunda ya faru ɗazun,saboda kunyi case da Suwaiba dole ne na yarda bugu da ƙari fa Nafisa dambe na tarar kina yi da ita kamar Namiji,sam wannan ba ɗabi'ar mace bace,dole ne ki koyi danne fushin ki idan ba haka ba kuwa da kowa ma faɗa zakiyi,yanzu da ace da tsautsayi kin cirewa Suwaiba ido fa?"cikin kukan dake san ƙwace mata tunda big Mummy ta fara magana tace"Amma Mummy ai ko Allah ya sani tunda ta fara maganar ta ban kula ta ba sai da ta faɗa mun magana mara daɗi ,Allah Suwaiba munafuka ce a duk labarin da ta baki ai bata faɗin nata ba nawa kawai ta faɗa ,duk sun fi ni Hali mara kyau amma saboda ni nawa ne fitowa fili kowa laifina yake gani ba nasu ba".jawo ta jiki Big Mummy tayi tace"ya isa ya riga ya wuce dan Allah ban san kuma naji kin sake wani faɗan"ƙaɗa kai kawai Nafisa tayi amma a zuciyar ta bata gamsu ba ,jira take komai ya lafa na yau tasan ina zata Aje Asiya dan kuwa zagin da tayi mata bashi ne kuma sai ta biya,sai ta nuna mata Halin Jakai ɗin da take kiran ta tukunna hankalin ta zai ƙwanta,gwara idan an kira ka da dabba ka tabbatar da ka cike standard na wannan dabbar kada wanda ya faɗa ya Ji kunya.sakin ta Big Mummy tayi tace"Allah yayi miki Albarka ,maza kije ki ƙwanta bana san kalla ce kalla cen banza na daren nan ,idan na shigo ɗakin ku naganki bakin Tv kina wannan nacin Kallan naki baza mu shirya ba".tashi tayi tana mai faɗin to kafin tasa hannu cikin ƙwannan soyayyan Kifi ɗin dake gefen Big Mummy tana mai cewa Nagode.kaɗa kai Big Mummy tayi bayan fitar ta tace"Allah ya shirya mun ke Nafisa".Kai tsaye bayan ta fita ɗaki ta wuce ,Khadija Hama da Suwaiba ta tarar suna Kallan Favorite Indian series ɗin ta na Faltu a starlife,bata kula kowa ba ta wuce kan gadonta duk da kuwa yarda zuciyar ta ke ingiza ta taje tayi kallon,Kallan Juna suka fara kafin Hama tace"Yaya Khadijah yau kunyiwa Nafi ba dai dai ba gaskiya,ki kalla fa duk santa da Kallan Faltu ta wuce ta ƙwanta".Ajiyar zuciya Khadija ta sauke tana mai tuna irin aibatata da Asiya tayi ,ƙin ɗaukar matakin ta shine Babban damuwar ta dan tasan akwai sauran rina a kaba,Kallan Suwaiba khadija tayi tace",Suwaiba kin san yau Abunda kika yi baki ƙyauta ba ko?Ni dake na faɗa miki Nafisa ta ɗauka mun jambaki?mene yasa zakiyi confronting ɗin ta har Abun ya kai ku ga faɗa?"ƙasa da kai Suwaiba tayi tace"yaya Khadija baki ji ɗan Abinda nace bafa Wallahi bai kai ayi faɗa ba ,kin san Halin Nafisa.".Hararar ta Hama tayi tace"habawa Suwaiba kema fa nasan Halinki,na Nafisa ne kawai ya fito amma kema baki da hali ko ƙaɗan,baki san a zauna lafiya kullum Kuma idan kun yi faɗa ke da Nafisa kece ke fara takalarta ban san mene matsalar ki ba".Ita dai Nafisa bata ce uffan ba ta koma ta ƙwanta bayan ta gama abunda take dan a yanayin yarda take jinta idan aka cigaba da tada magana sai ta sake chasa suwaiba.
Bayan ƙwana biyu da abinda ya faru Nafisa ta zama wata very collected,Bata yi rigima da kowa ba cikin ƙwana biyun Amma zuciyarta na ta mata zuga dan jin ta take kamar ba ita ba,ta riga ta saba da rigima ƙwana biyu da batayi ba sai take jin ta kamar sabuwar mutum wadda aka takurawa,kasancewar ranar Asabar ne basu je boko ba Sai Islamiyya da suke jiran lokacin yayi kar ma ace Nafisa Wadda ke zuci zucin zuwa taga Akram ,tana zaune tana duba haddarta wadda tasan za'a sha gwagwagwa Khadija ta shigo da Sallama Asiya na biye da ita tana cewa"haba mana Khadijah sai binki nake akan gyalen da yapi shekaru wurin uku amma kina yanƙwana ni, wallahi dan ina san baƙin gyalen ne kuma banga Nawa ba amma baya ga haka ai kema kin san Nafi ƙarfin gyalen nan,amma dai still kiyi haƙuri ki bani kinga Yusuf Yana hanya Wallahi"Matsowa tayi ta dafa Khadijah cike da daɗin baki tace"Who knows idan na fita na sama miki miji cikin Abokan Yusuf kema a cire ki cikin Balain nan dan wallahi gidan nan bala'i ne shi yasa kika ga na dage ma Yusuf Allah yasa Big Mummy ta basa change na fara zuwa gurin a ,before you know it sai dai kiji ance ya Aure ni".Taɓe baki Khadijah tayi tace"abeg kada ki fara wani match making Dani ban so, kamar kuma yarda Yusuf ɗin ya gano ki ya yarda zai Aure ki muma mazajen mu zasu zo tunda ance matar mutum kabarin sa,sannan a yarda baki iya magana ɗin nan ba kina zuwa kina yiwa namiji irin wannan wallahi sai dai buzun ki,yo gyalen in ma shekara hamsin yayi ai dai nawa ne kuma gashi yana ƙoƙarin yi Maki Rana in ba haka ba kisa naki mana".sosai Asiya taji zafin maganar Khadijah amma sanin idan tayi fushi babu mai bata ɗin bayan khadija Yasa ta wayance tace" naji yi hakuri na ɗau laifina".wardrobe Khadija ta nufa ta ɗauko mata Gyalen, rungume ta Khadijah tayi tana mai cewa"idan babu ke nayi yaya a gidan nan"Dariyar da Nafisa tasa itace ta tsayar da Asiya daga abun da take faɗi,cike da Mamakin Dariyar ta Asiya tace"ke dan kutumar ubanki da wa kike?"cike da rashin Kunya Nafisa tace"da ɗan kutumar uban da ya tsargu wannan mara zuciya ɗin mai san Aran abun mutane "Kallan Khadijah Tayi tace"Khadija kina Jin abun da tsinanniyar yarinyar nan ke faɗa mun ko?to wallahi sai naci ubanta duk abinda zai faru sai dai ya faru,gadan gadan tayi kan Nafisa ,riƙe ta Khadijah tayi tana cewa"dan Allah kiyi hakuri Asiya ki wuce kada kuzo ayi abun kunya"cike da baccin rai Asiya tace"Abun kunya kamar wanne?ki rabu dani na banbanta mata tsakanin Aya da tsakuwa"cike da rashin Kunya Nafisa tace"mu banbancewa juna dai dan wallahi duk abinda kike ji nima ina ji kilan na nawa yafi naki,ko dan kin ga ranar ban kula ki ba shine kike ganin kamar ina jin tsoron ki,to wallahi Ni uwarki ce a rashin Kunya banbanci kawai Ni bana zuwa a danne ni".ai cikin wani kukan kuran ta sake yin kan Nafisa Amma Khadija ta riƙe ta.fizgewa tayi tana mai Kallan Nafisa dake fama girgiza ƙafa tace"kin ci sa'a yanzu ina da abinda ya fiki muhimmanci Wallahi da babu abinda zai hana Ni cin bura ubaki,Ni ba khadija bace ,amma ki sani zan lokacin ki,Allah yasa ma Aure zan na bar muku God forsaken place ɗin nan".Turo baki gaba Nafisa tayi cike da fitsari tace"dama ya za'ayi ki zama Khadijah ,ita ai bata zagayawa sannan duk lokacin da kika tashi lokacina ai kin san inda zaki sameni ina nan ina jiran ki ,wallahi zakiga jakanta,Aure kuma kiyi mugani mana magana kuma da kika karasa da turanci "Allah da guri"kawai na fahimta amma idan zagina kikayi wallahi kanki kika zaga,har zaki faɗawa ɗan yau iya shege,ɗan yau ɗin ma Ni Feenah".cike da wani kululun takaici Asiya ta kalle ta kafin tace"ki shirya amsa kiran Big Mummy".tsaki Nafisa tayi tace"ya kamata dan dama akwai tone tonen da tuntuni ya kamata a ce anyi."bata sake faɗin komai ba ta fita ranta a bace.Kallon Nafisa Khadijah take kafin tace"" Nafisaahhh,ɗan juya ido tayi tace "mene?ai gabanki ranar take tsine mun kinji na tanka ta?badai ƙarata ne zata kai ba, wallahi taje ni kuma sai na tona mata asiri,Kallan biri take mun ina yi mata na ayaba,duk iskancin da suke ita da hudu mai gadin babban Gate wallahi a ido na sau biyu ina kama su sani ne batayi ba,kuma jin na faɗi akwai tone tone babu abinda zata iya bari kuma ki gani tasan ai bata da gaskiya,Aure kuma da take cika mana baki tayi mugani mana,gidan nan da bata so ,tayi ta zaman sa ke nan,zata wani kwaso kayan jiki da baki kamar na shaida tana yiwa mutane fi'ili, wallahi ki rabu da Asiya dan ba ƙawa bace".Kafin Khadijah tace wani abu Hama da Suwaiba sun shigo,cike da kallon tuhuma Hama tace hala mun katse wani abun.zama Khadijah tayi tace "mene kuwa zaku katse,har kun dawo daga kasuwan?"murmushi hama tayi tana mai miƙawá Nafisa ledan dafaffiyar gyaɗa tace"gashi nan Muna dawowa Suwaiba ta ga gyaɗa tasan kina bala'in san gyaɗa tace a siyo miki"ɗaga ledar tayi kamar Kashi tace"Munafircin Banza,Nagode".zama Hama tayi kusa da ita tace"zo nan Suwaiba"ba musu tazo ta zauna,kamo hannun Nafisa tayi tace"yanzu dai kiyi hakuri Nafisa komai ya wuce dan Allah"yatsuna fuska tayi tace "in dai ta daina mun munafirci lafiya zamu zauna,Amma Allah ta sake mun Abinda tayi mun babu wanda ya isa ya raba Ni da ita".tashi tayi tace"bari naje muyi tilawa da sa'adatu"da sauri Khadijah tace"dan Allah Nafisa kada kije ɗakin su Asiya yanzu"kwata kwata ita ta manta wai Asiya ma ɗakin su Sa'adatu take,Ƴar dariya tayi tace"Allah bazan kula ta ba waje ma zan tsaya Sa'adatu ta fito".
Please vote and share
TBC08130229878
CZYTASZ
BA DUK KYALLI BANE GWAL
Romans(When their world collides) Rayuwarsu tayi kamanceceniya, lokaci guda kuma komai yayi ƙokarin tabarbarewa sabida gaskiya akan al'amarin rayuwarsu, ita marainiya ce a yarda ta sani ,wadda aka tsinta a bakin hanya ,shin mai zai faru idan tasan cewa iy...