Teaser

37 2 0
                                    

BA DUK ƘYALLI BANE GWAL

(When their heart collide)

TEASER

NAFISA shine sunanta sannan Maraici shine mafarin ta,bata san dangin ta na jini ba face dangin ta na gidan Marayu,a Halayya ta ɗan Adam Tata daban ce domin kuwa iya zaman ta cikin wannan gida kowa kaji yace "wash" to daga ita ne,naci a duk wani abu da ta saka gaba shine Alƙibilar ta amma kash Abu guda da kowa ke so ta saka gaba baya gaban ta ballantana tayi masa naci,mutane kance Karatun Nasara shine Haske a abinda ka dosa cikin duniya sannan wasu gani suke idan babu shi baka ba jin daɗin madarar Arziƙi,magana ɗaya ce kullum daga bakin Nafisa wato zata tayi kuɗi amma fa kan nan a kulle yake,bata damuwa da duk wani surutu da za kayi mata kan karatu domin tace"nothing dey enter"magana ta fahimtar Yaren nasara fa?shima tace "nothing dey enter"amma fa a lokacin da ƙauna da zamu kira da abunda ya dangana da Kuruciya tayi mata mugun kamu tace"i go learn na kare kai"saboda wannan masoyi guda da kowa ke so ciki gidan marayun.

Rayuwa bata da tabbas, lokacin ɗaya ta rasa wani jigo nata a cikin gidan wanda yayi sanadi na barin ta,amma ina ne ƙaddara ta kaita?

Shin Nafisa maraniya ce ko kuwa akwai wani ƙulli dangane da Maraicin ta ?

Fitar ta daga gidan ta haifar da Abubuwa da dama wanda ita kanta batayi tunanin zuwan su ba.Amma tace da Babbar Murya"zan shirya wa komai"shine zata shirya ɗin ko kuwa abun zai zo mata kamar ɗirar mikiya fiye kuma da tunani ta?

AKRAM shine sunan sa abu mafi soyuwa ga Nafisa,ƙaddara ta zaman gidan maraici itace ta haɗa ƙadarar su ta ɗinke ,amma ko wanne daga cikin su yana da nasa Labarin da kuma abun fuskanta a waje,a tunanin kowa ya manta wanene shi wanda hakan yasa aka wofintar dashi gidan marayu,amma a nasa kiɗan da ƙwaƙwalwar sa keyi masa tsaf bai manta ba ,inda ya fito,Abun da ya fuskan ta,wane Mahaifin sa da duk wani abu da ya kamata ya sani akan sa,barin sa gidan Marayun shine Babban tikiti na daukar fansan abinda ya fuskanta wajen matar uba da uba wanda ya nuna ko in kula,a cewar sa "sai Na zama abun da zai saka su hawaye "shin zai zama ɗin ko kuwa wani abun zai dakatar dashi?baya tunanin da akwai wanda dalilin, hakan ya saka shi yin baya baya da Nafisa duk kuwa ƙwaɗayin sa na ganin cewa ta yi karatu ta zama wata ,Yana son taimaka mata Amma ganin sa Abinda yake dashi a waje ya kamata ya fara kafun ya iya taimaka mata.

Hmmmmmmm.

Ku kasance dani ɗiyar jameelu domin jin yarda wannan labarin zai kasance,Ina fatan zakuji daɗin sa,yana na tafe ciki sabon watan da zamu shiga idan Allah ya nuna mana da rai da lafiya.

Amina Jamil Adam

CHUCHU JAY

BA DUK KYALLI BANE GWALOù les histoires vivent. Découvrez maintenant