A hankali Nafisa ta aje Hijab ɗin dake hannun ta juyo tana mai bawa Suwaiba wani irin banzan kallo kafin tace"Dan uwar ki kina so kice ko mene ya ɓata a ɗakin nan nice wato gani ɓera bugu da ƙari ma na rasa Abinda zan sata sai jambaki,jambakin ma na rasa na wane zan ɗauka sai na Khadijah wadda basir duk ya cinyewa baki,wallahi Suwaiba ki fita harka ta ,babu wani abu da kika iya bayan munafirci,to wallahi Ni cimmiki zanyi,ai kin san hali na ba wai baki sani ba,kal bura ubaki nakan ci na zauna lafiya,ina cewa nan da na ɗauki ɗan kunne ki kinsan cewa Ara nayi amma saboda tsabar kina san haɗani da uwata kika je kika faɗi mata wai na satar miki,to wallahi ta Allah ba taki ba,tsakanina da big mummy sai ta Allah bata mutum ba idan kuma kina ganin ƙarya nake to muje zuwa shege ka fasa".juyawa tayi dan ɗaukan Hijab ɗin ta,saka hannunta kai ke da wuya Muryar Suwaiba ta tsayar da ita inda take faɗin"yo uwarki ta gidan Marayu dai, babu wanda bai san tsintar ki tayi ba,cikin gidan nan wane bai san labarin yarda ta tsince ki ba ". A fusace Nafisa ta juyo ta nuna ta da yatsa tace"ki nuna mun wanda yake mai cikaken asali gidan nan,kece matsiyaciya sannan waɗan da basu san ke munafuka bace zaki yaudara amma bani ba ,duk taran tsintattu ne kilan ma ke cikin shegu kika fito"charaf Suwaiba ta kama inda take cewa"kila ke kuma ana karuwai duk inda akaje aka dawo kin haɗa iri dasu musamman yarda ki ke maƙalewa Brother AKRAM Allah kilan a karuwaci aka samu cikin ki shi yasa aka zo bakin gidan nan aka cillar dake duk da ruwan da ake sheƙawa,Allah ma ya temakeshi ƙasar zai bari ,kilan kuma sai ki nemi wani kibi tunda muna da yalwar mazan"bakin ta na rufuwa Hannun Nafisa na sauka kan fuskar ta,ai kafin kace ƙwabo faɗa ya kece tsakanin su ,sosai suke kaiwa juna duka wanda Suwaiba tafi dakuwa,a haka suna kan kokawar suka fita har ƙofar ɗakin su inda hakan ya jawo hankalin mutane suka fara zuwa kafin aka samu waɗan da suka shige tsakani domin raba su,zage zage suka cigaba tsakanin su,wata sister ɗinsu ce ta riƙe Nafisa wadda ke faman cilla ƙafa tana cewa a rabu da ita ta illata Suwaiba yayi da ita kuma Suwaiba ke kuka duba da raunin da Nafisa tayi mata a ƙasan ido.muryar Big mommy dake faɗin "ku sake ta"shine Abinda ya dawo da Nafisa ciki hankalin ta ,sai a wannan lokacin ta farga da cewa wai faɗa take,cike da mutuƙar takaici big mummy tasa aka kai Suwaiba sick Bay domin a mata dressing ciwan da Nafisa ta ji mata,Kallanta ta mayar kan Nafisa tace"idan na riga ki zuwa inda ya dace kije Wannan lokacin wallahi baza kiji daɗi na ba,sai nayi mutuƙar saɓa miki fiye da tunani".tana juyawa Nafisa ta kwasa da gudu tana kuka dan tasan ta kaɗe ne kawai,ta riga Big Mommy zuwa ɗakin horo wanda tana zuwa ta zube kan gwiwowinta ta ɗaga hannunta sama ta rufe idanu tana furta duk wata Addu'a da tazo mata baki,jin Muryar Big mommy data sargent ya saka tayi saurin buɗe idanunta tana mai cewa"Na shiga uku Ni Nafisa".Baki kai ga shiga uku ba tukunna ai,maza Sargent fara dukan ta har sai nace ka bari.murmushi dattijon yayi yana mai gyara kan dorinar dake hannun sa sharfefiya,dama yana jin Haushi Nafisa duk da kuwa babu abun da ya taɓa haɗa su amma jin kowa na koƙen ta yake fatan wani abu ya haɗa shi da ita ya tafarfasa ta,cikin zumuɗi ya ɗaga bulalar ya fara dukkan Nafisa Wadda guda ɗaya na shigarta ta hau kururuwa tana ihu,runtse ido Big mommy dake zaune tayi tana jin ihun Nafisa har cikin ranta,amma dole ne ta mata hukunci dan ta lura idan ta cigaba da sake da Nafisa za'a samu Babbar damuwa dole ne ta ringa nuna mata kurenta idan tayi ba dai dai ba.Duka Sargent ya cigaba da yiwa Nafisa Wadda ke faman ihun domin kuwa dukan baki ɗaya ya zautar da ita,yana ƙoƙarin sake ɗagawa ya zuba mata wata mai shegen zafin Akram ya shigo gurin da sauri ya saka hannun sa ya tare dukkan,sosai ta shige sa,cikin yanayi na jin zafin dukan sosai yace"Baba Idi duka akace kayi mata ba wai ka kashe ta ba,haba dan Allah wanne irin duka ne wannan".cike da jin kunya Baba Idi yace"wannan yarinyar bata jin magana Akram horo shine dai dai da ita".a hankali Big mummy dake gefen su tace"zaka iya tafiya Nagode".babu musu ya fita yana sake kallan Nafisa Wadda ke aikin kuka kamar an yanka ta,sallamar khadija da Suwaiba ne ya katse dukkan su daga yunƙurin yin Magana,Kallan Khadijah Big mommy tayi tace"ya ciwan nata?".kafin Khadijah tace wani Abu Suwaiba tace"wallahi Big mummy baki ji ba kamar ido na zai cire".cike da takaicin ta Akram yace"shin tukunna ma mene ya haɗa ku?wani kukan Munafirci Suwaiba ta ƙaƙalo ganin yarda Nafisa ke kuka gudun itama Kada a chasa tafara bada Abunda ya haɗa su tana mai cire Part ɗin da ta faɗawa Nafisa jinin Karuwai". tambayar Big mummy Khadija tayi shin Nafisa ta satar mata jambaki tace ta duba ne bata gan sa ba amma daga baya kuma ta gani cikin kaya, Nafisa na jin haka ta tashi ta fita a gurin da gudu dan idan ta tsaya wani damban zasu sake da Suwaiba bugu da ƙari kuma baza ta iya kare kanta ba saboda takaici.Nasiha Big mommy tayi musu tana mai sake tuna musu su ɗin Yan uwan juna ne kuma dole ne su koyi hakuri da juna.
ESTÁS LEYENDO
BA DUK KYALLI BANE GWAL
Romance(When their world collides) Rayuwarsu tayi kamanceceniya, lokaci guda kuma komai yayi ƙokarin tabarbarewa sabida gaskiya akan al'amarin rayuwarsu, ita marainiya ce a yarda ta sani ,wadda aka tsinta a bakin hanya ,shin mai zai faru idan tasan cewa iy...