KUNUN KWAKWA

3.3K 163 11
                                    

INGREDIENTS
Kwakwa
Danyan shinkafa na tuwo
Siga
Citta
PROCEDURE :
Ana son uwargida ta wanke danyar shinkafa kamar yadda ake wanke gero, sai ta sanya mata citta, sannan ta markada ta.
Bayan haka, ta tace ta kamar dai yadda ake na kamu.
Bayan ta jira ta kwanta, sai ta samu kwakwa, sannan ta kankare bayanta (mai launin ruwan kasa) har sai tayi fari tas.
Sannan ta yanka ta kanana yadda za ta iya nika ta da na'urar blender cikin sauki.
Idan ta yi laushi sai ta samu tukunya ta tace a ciki.
Idan ta kawo fatasa, sai ta dama kullin danyen shinkafa nan daidai misali, sannan ta zuba.
Daga nan ta ci gaba da gaurayawa har sai ya yi kauri, sannan ta sauke.
Idan ya dan huce sai ta zuba madarar gari da siga daidai dandano.

Please do vote, comment and follow... It will means alot!

Nigerian food recipesWhere stories live. Discover now