ONION SOUP

2.8K 83 3
                                    

Onion soup (miyan albasa)
Ingredients
-onions
-meat
-garlic and pepper (attaruhu)
-oil
-corn flour or wheat flour
-peas
-spices
METHOD
1. A tafasa nama tare da maggi, thyme da albasa
2. Sai a yanka naman suyi kanana sosai
3. A yanka albasa ta tsaye kar yayi sirara kar
suyi luti yanda zai ishe ki (wajen cikin roba ko
karamin plastic)sai a wanke su
4. A jajjaga tafarnuwa (garlic)sai a yanka
attaruhu (guda 2 ma dasu isa)
5. A dora tukunya a kan abin dafawa sai a saka
mai, a juye jajjagen garlic da yankakken
attaruhun a cikin mai din
6. A juye yankekken kananun naman a ciki
7. Sai a juye yankakken albasan a cikin mai din
tare da peas din a yi ta juya su, albasan zai fara
lamushewa yana fidda ruwa, ayi ta juyawa har
sai albasan ya dahu
8. Sai a saka spices (maggi, ajino, onga, curry,
thyme, salt)a kara juyawa na minti daya sbd
spices su ratsa sosai
9. A juye ruwan nama a ciki, in bai isa ba a kara
da ruwa
10. A dama corn flour ko asalin flour da ruwa a
cup sai a juye a ciki a gwauraya sbd yayi kwauri.
A rufe shi na minti biyu shknn a kashe gas ya
dahu kenan....
- da a iya cin shi da farar shinkafa ko taliya ko
macaroni ko cous-cous ko a sa kadan akan jollof
rice a ci..

Nigerian food recipesWhere stories live. Discover now