01 - NASREEN IZZADDEEN

15.8K 1K 234
                                    

Ummi ta sha fada mata cewar akwai ranar da zata yi rayuwa irin ta ko wacce mace, ta kan ce da ita

"Nasreen Allah ma ji rokon bayinsa ne, haka zalika babu wanda ya kaishi nuna kauna da soyayya ga bayinsa. Hatta mu din nan iyayenki, baza mu taba hada soyayyar da muke miki da ta mahaliccinki ba, dan haka ki yarda da ni, lokaci yana zuwa da zaki yi dariya."

Duk da irin wannan kwarin gwiwa da Barr. Jidda Izzaddeen ta kan bata, hakan bai sa ta taba tunanin taka kofar katafaren wuri irin wannan ba, hakan bai sanya ta hasashen aiki da TCZ ba. Asali ma bata taba tunanin daidaituwar lamurranta ba, daga ciki kuwa hadda samuwar cikakken tunaninta.

Kalmar 'tunani' ta jefa ta a duniyar hasashen inda Dr. Aqaq Saifullah ya nufa, mutumen da ya sadaukar da komai na shi dan ganin ya tsamo ta daga kallon hadarin kajin da mutanen duniya kan mata.

Murmushi mai ciwo, ya kufce ta gefen kumatunta, tayi sama da kanta, tana mai kare ma dogon ginin da a kalla zai tasan ma hawa goma sha biyu kallo.

Tunaninta a yanzu, ya ta'allaka ne kan yadda zata gina rayuwarta, ta inganta ta, ta kuma mori sauran kuruciyar da ta yi mata saura. Dolenta ta shafe babin rayuwar da ta yi a baya, tana da tabbacin tuna al'amurran da suka gabata, ba komai zai haifar gareta ba illa tashin hankali, da fadawa duniyar da bata kaunar tunawa.

Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, ta gyara hannun jakar kwamfutarta, ta rungumi kakkauran dogon fayil din da ke tsakanin hannunta na dama da gefen kirjinta ta tasar ma kofar gilashin da take juyawa tana karasar da mutane zuwa cikin tsararren tafkeken risefshan din kamfanin.

"Barka da zuwa Hajiya."

Fara doguwar matashiyar da ta yane kanta da gyalen bakar abayar da ke jikinta ta fada da dogon murmushi saman fuskarta.
Murmushin ta dora a kan labbanta itama, ta karasa tana mai dafa teburin da ya yi katanga tsakaninsu.

"Uhnmm.. Ofishin Mukhtar Jabbar."

"Mukhtar Jabbar."

Kyakkyawar matashiyar budurwar da ke kula da risefshan din ta maimaita tana mai bincika kwamfutarta, sannan ta dago

"Hawa na goma sha daya, ofis na biyu daga hannunki na dama."

"Na gode."

Ta fada da kyakkyawan murmushi a fuakarta, ta gyara farin gilashin da ke like a idanunta, kafin ta doshi liftar da zata sada ta da hawa na goma sha dayan.

"Nasreen Izzaddeen."

Ta sanar da matar da ta samu a zaune tana hada takardu, a lokaci guda tana aika mata da kallon da ya fi yanayi da na wulakanci.

"Sai dai ban ganki a jerin mutanen da zasu ganshi yau din nan ba."

Kamar baza ta ce wani abu ba, domin kallon da take mata kadai, ya sanya ta fara zargin kanta. Cikin yanayin da ya zame mata jiki, ta kai hannu ta dai-daita gilashinta. A hankali ta furta,

"Ya san da zuwana, ki sanar da shi idan babu damuwa."

Sai da ta gama abinda take, sannan tasa hannu ta gyara dogon gashin kantin da ya sauko ya rufe rabin fuskarta, ta mike a saman dogayen takalmanta masu zira'i hudu da digo biyar, ta fara takawa cike da rangwada, da jan hankali.

HAWAYEN ZUCIYA!Where stories live. Discover now