JIMETA YOLA, 1999
"Ummi ni wannan nike so."
"Ban san lokacin da kika fara son yellow ba Areefa."
"Ni dai shi nike so, idan ba shi ba kuma ba zan saka rigan ba."
"Zaki kwana a nan kenan. A gabanki Nasreen ta nuna shi, tace shi take so, ke kika nuna red din nan, sai yanzu zaki ce baki san zancen ba? Ko dan yana mallakin Nasreen? Yaushe zaki canja halayenki saboda Allah?"
"Tun dama can wannan nike so a raina fa Ummi, hannuna ne ya nuna wancan."
Tana tura bakinta gaba tayi maganar, idanunta a bushe.Yadda take furta kalamanta, babu wanda zaiyi zaton shekarunta duka-duka shidda ne a duniya.
Hankalinta na kan jerin kayan wasan da ke gabanta. Haka take ta faman jerawa suna tarwatsewa, bata gajiya haka zata kuma jera su wannan bai zamo abin damuwa ba a gare ta.
Gabanta Ummi ta karasa, tasa hannu ta juyo da fuskarta zuwa gareta, cikin sa'a idanunsu suka hadu cikin na juna, tamkar wacce aka tsirawa allura, haka tayi saurin kawar da kanta. Ummi ba ya san me yasa ba, amma zata iya cewa tunda take, bata taba hada ido da ita ba, da alama hakan tsarin halittarta ne.
"Nasreen."
Ummi ta kira a hankali. Bata jira ansarta ba, dan ta san ko zasu shekara dubu a wurin ba zata ansa ba, dan haka ta dora da fadin
"Zaki yarda kuyi masanyan riga da Areefa? Tace baza ta saka wancen ba."
Bata tanka ta ba, asali ma abinda ke gabanta ta ci gaba da jerawa.
"Ummi ba fa zata ansa ba, kin sani ni ki bani rigan kawai in saka, ita da bama gayyatanta birthday din aka yi ba."
Tana kallon yadda take aika harara setin da Nasreen din ke zaune, dubanta ummi ta tsaida a gare ta tana fadin
"Zaki bace mun a nan ko sai ranki ya baci?"
Wani irin kuka mai karfin gaske Areefa ta saki hakan ya jawo hankalin Abba da shigowarshi gidan kenan, ya karaso cikin falon da fuskarshi dauke da wani yanayi yana tambayar
"Me ya ke faruwa haka?"
Kukanta sosai ya razanar da Nasreen, da sauri ta dora hannayenta duk biyun a saman kunnuwanta, ta mike da gudu ta karasa inda Ummi ke zaune tana mai shigar da kanta cikin jikinta, a hankali take fadin
"Bana so... Ummi..bana so."
Ganin hakan ya sanya Areefa kara sautin kukanta, domin kuwa tana sane da cewar duk lokacin da Nasreen zata ji sautin kuka ko na wani abu mai kara hankalinta ya kan tashi, a wasu lokutan har ma ta rasa inda zata saka jikinta
"Ya isa haka Areefa. Kiyi magana. Me ya same ki?"
Abba ya karasa inda take, yana zaunar da ita a gefenshi, a lokaci guda yana maida dubanshi bangaren da Ummi ke rike da Nasreen.
"Abba Ummi ce.. Me yasa bata sona?"
Areefa ta tambaya tana shafe hawayen da ke kwarara a idanunta.
YOU ARE READING
HAWAYEN ZUCIYA!
RomanceBetrayal, love, and tragedy. Dive into the most beautiful love story of Nasreen Izzaddeen and Aqeel Mukaila AbdulWahab.