A sannu a hankali yanayinta ya fara canjawa daga farin ciki da annashuwar da take ciki, zuwa fargaba da yawan faduwar gaban da ta kasa fahimtar inda suka dosa.
Har a yanzu da Sandra ta gabatar da ita a kofar dakin taron da aka bukaci ganinta, bata daina jin firgici da yawan alhinin da zuciyarta ta tsinci kanta a tsakaninsu ba.
Wasu sassa na zuciyar, na taimakawa wurin bata kwarin gwiwa, a bangare guda wasu wuraren na kara karfafa alakarta da rashin son cudanya da bakin mutane, har tana jin tamkar ta juya da baya ta kama hanyar gida.Sai dai ya zata yi?
Bata da wani zabi idan ta tuna da wannan ce kawai damar da take da, wannan ce kuma hanya guda daya da zata samu biyan bukatarta, ta kuma samu damar yin abinda ta fi kauna tun daga ranar da ta bude ido a duniyarta.
A hankali ta murda kofar tsararren dakin taron. Kamshin turaren da ta shaka yasa gaba daya gabban jikinta babu inda yake motsi mai kwari na wani dan lokaci. Sassan kafarta tamkar suna sarrafa kansu ne saboda rashin kuzarin da ta tsinci gangar jikinta da shi.
'Turaren ne kawai.'
Ta tsinkayi furucin daga wani sashe na zuciyarta.
Kanta a kasa, tana gyara jelar gyalenta da ke kokarin warwarewa, a lokaci guda tana kyafta ido ta cikin farin tabaran da ya zame mata abokin gani, ta ci gaba da takawa a daburce, zuwa tsakiyar dakin taron."Mashaa Allah. Karasa ga wurin zamanki nan Nasreen."
Muryar Mukhtar Jabbar ta sanya ta saurin dagowa a hankali, tana tunkarar wurin da ta ga hannunshi na mata nuni da kujerar da babu kowa a kai
Sai da ta da2idaita natsuwarta, ta fito da kayan aikinta, sannan ta dago a tsanake, tana kokarin tattara dukkan karfin halin da zai taimaka mata dan gabatar da abinda ya tara su.
Kusan mutum goma da ke kewaye da dogo faffadan teburin da aka kawata da robobin ruwa da na lemu tare da kofunan gilassai, sun mika hankulansu ga kyawawan zanukan da take nunawa ta hanyar amfani da na'ura mai kwakwalwa a jikin farin allon da ke like da bango (projector,) in banda mutum guda, wanda kujerarshi ta fi ta kowa tsawo da fadi da ya mika hankali da natsuwarshi a kan ipad din da ke girke a gabanshi yana dannawa.
Cikin ikon Allah ta gama nuna soft copies din, kafun ta gabatar da hard copies din zuwa ga kowacce kujera domin ganin ingancin aikinnata.
A sannu a hankali take jin natsuwa na saukar mata ganin yadda mutanen ke yaba hazaka da kwazo irin nata, kanta a kasa labbanta kunshe da murmushi take jujjuya zoben da ke sanye a yatsanta."Wannan shine abunda kamfanin ya dade yana nema a nan cikin gida Nigeria dan samun sauki daga yadda muke biyan makuden kudade ga mutanen kasashen ketare dan mu samu aiyuka masu inganci mu kuma bunkasa tattalin arzikin kasarmu. Zata iya fara aiki daga yanzu zuwa ko wanne lokaci. I mean as soon as possible.."
Idan turaren ya kasance iri guda, sosai murya da kamannin mutumen da take jin kalamanshi na shiga ta kofar kunnuwanta, suna zarcewa cikin kirjinta, suna masu yi mata suka a kahon zuciya ba gizau suke mata ba.
'Shine.'
Zuciyarta ta gama amincewa.
Sai dai me yasa yake wanzuwa a tsakiyar duk wani farin cikinta ya wargaza shi ya hana mata moruwa da shi ko na minti guda?
Me yasa yake son wargaza wannan tubalin da ta shekara biyar tana ginawa bayan hali na ha'ula'in da ya jefa zuciyarta a baya?
Sam baza ta iya daukar wannan tashin hankalin a karo na ba adadi ba.
Ya barta taji da yadda ta samu rayuwarta a yanzu mana. Ya barta ta ci gaba da jinyar da take fama da ita a tsakanin kirjinta na iya shekarun da ta samu a duniyarta.Me yasa zai bayyana kanshi a lokacin da ta manta da cewar Allah ya taba halittarshi..?
"Congratulations Ms. Izzaddeen and welcome to TCZ."
Muryar da yawa daga mahalarta taron, ta dawo da ita daga tirka tirkar da zuciyarta ta mika ta.
Ta dago a hankali, labbanta na kokarin boye damuwar da take ciki ta hanyar sakin dan gajeren murmushin da iyakacinsa fatar baki, tana mai sinne kai, da nufin amsa marabar da suke mata, wanda hakan ba bakon abu bane a wurinta ba. Hakan ne kuma ya ke faruwa a duk kusan lokacin da tsautsayi zai ratso da ita tsakiyar taron mutane.
Tana kallon yadda bai damu da ya kalle ta ba, ta san ba wai bai gane ta ne ba, sai dan rashin muhimmancin da har yanzu take da shi a tattare da tashi rayuwar.
Hawaye masu dumi da ciwo suka nemi kwacewa kwarmun idonta, hakan ya yi sanadin yi mata fami a kasan ruhinta, ya taso mata ciwon da ta shafe shekaru goma sha ukku tana faman jinyarsa.
Da taimakon gilashin idanunta ta dakatar da hawayen cikin dabarar da ba kowa ya fahimci halin da take ciki ba.
Bata ga amfanin shekarun da ta dauka domin ta manta da shi ba, bata ga amfanin shekarun da ta shafe tana mai nisantar iyayenta da mahaifarta ba.
Da ace tana da masaniyar karatunta zai kare ne a karkashin Aqeel Mukaila, tabbas da ta zamo abinda Dr. Aqaq da ma Barr. Jidda suka so ta zamo. Ta tabbata, da babu abinda zai jaza musu yin haduwar nan ta ba zata.
Me yasa ba ta yi watsi da soyayyarta da zanunnuka ba? Duk da kasancewarsu ababe na farko da ta fara kauna a duniyarta, wanda sune suka gina soyayyar Aqeel Mukaila mai inganci a birnin zuciyarta, tun ma bata san shin yana rayuwa a wannan duniyar ba ko a'a.
"Ashe kin dawo?"
Ta tsinci zazzakar muryarshi mai zurfi, cikin kalamun da bata yi zaton zai zamo gaisuwarsu ta farko ba bayan shekaru biyar da suka shude basu ga junansu ba.
Rashin kuzarinta ya gama bayyana a fuskarta, ta dago a hankali, makoshinta ya gama bushewa, hakan yasa ba lallai magana ta iya fita a fatar bakinta ba.
"Uhnmmm.."
Shine kawai ta iya furtawa, tana mai cizon karshen dogon fensir din da ke hannunta, kafin ta fara tattara takardunta, ganin dakin taron ya gama watsewa tun lokacin da ta afka duniyar tunani. Bata ko kalli inda ta ke jiyo kasancewarshi ba, duk kuwa da yadda idanunta ke kwadaitar da ita da son kara kallon fuskar da ta shafe rayuwarta tana zanawa.
"Welcome to TCZ. It's an honour to have you here. Do have a pleasant day ahead."
Wannan karon bai jira amsarta ba, ya fara takunshi cikin fadi, tana mai jin dirin duk wani sawunshi a kasan ruhinta, ta bi bayanshi da malalacin kallo, har zuwa lokacin da ya bace a idanuwanta, kafun ta sauke ajiyar zuciya, ta mike da zuciyarta tattare a tsakanin kirjinta zuwa harabar adana motoci ta kamfanin.
Well.. Well... Well!
Here come another chapter Dearies😀😀😀What's the secret between the two of them?
Biko drop yo comments, vote nd share with your family nd friends.
Best regards, Lubbatu Maitafsir.
😍😙
YOU ARE READING
HAWAYEN ZUCIYA!
RomanceBetrayal, love, and tragedy. Dive into the most beautiful love story of Nasreen Izzaddeen and Aqeel Mukaila AbdulWahab.