07 - A RANAR NE..

5.4K 581 208
                                    

"Sai an bani izini kafun in samu damar ganawa da kai kenan?"

Ta fada tana gyara zamanta a kujerar da ke gaban teburinshi, fuskarta kunshe da murmushin da ya kan karkato da hankulan mazaje da dama zuwa gare ta.

Da alama bai yi aiki kan Aqeel Mukaila ba, domin kuwa kallonta yake cike da kosawa, yana son sanin dalilin da zai sa ta shigo mishi haka, tamkar ita ke da mallakin shi din, da ma ofis din nashi baki daya.

"Kina da wani matsayi ne da zai banbanta ki da sauran mutane?"

"Zata iya yiwuwa."

Tana mai dora kafarta daya saman dayar ta fada, har lokacin da kyakkyawan murmushi kunshe da labbanta.

"Zaki iya fadar abinda ke tafe da ke cikin mintina.."

Ya kai duba ga agogon da ke daure a hannunshi kafun ya karasa

"..biyu. Saboda Mu'iz bai sanar mun da ganinki a schedule dina na yau ba. Shall we?"

Sosai kalamanshi suke taba ta. Ba kuma wannnan ne karo na farko da hakan kan faru ba. Kusan duk lokacin da zasu hadu, sai yayi kokarin yadda yayi, ya ajje mata tabo a kasan zuciya, kuma mai wahalar goguwa.

"Ban san yaushe zaka daina jifa ta da duk maganar da ta fito bakinka ba."

Tayi murmushi mai zafi, tana ci gaba

"Ban san lokacin da damuwata zata kasance taka ba."

Kafarshi daya ya dauka, ya dora kan dayar. Babban yatsanshi na dama, yana kai kawo a saman kyawawan labbanshi. Da halin ko in kula ya tsaida idanunshi kyam a kanta yana fadin

"Ka da ki taba yaudarar kanki wurin tunanin rana irin wannan zata iya giftawa tsakaninmu."

Bai damu da mai zai fito bakinta ba, ya mike saman takalmanshi tare da manna aninin suit dinshi, kafun yayi amfani da hannunshi wurin nuna mata kofa, ya kara da fadin

"Out of my office Khairiyya Sulaiman. Now please."

Murmushi tayi, tare da mikewa, kallonshi take cike da birgewa, tana dora hannayenta saman teburin da yayi mata tsakani da shi, ta rankwafo ta yadda har yana iya jin kamshin turarenta.

"Hanya ta shigo da ni Mr. Mukaila, a ganina babu dalilin da zai sa ayi mun korar kare. I was about to leave."

Ta juya cike da karfin hali, a hankali ta fara takawa zuwa kofar da ta shigo da ita.
Ba zai iya jure kallon ko da bayanta ba, duk wani taku nata, sosai yake jin yana rura wutar kiyayyarta a kasan zuciyarshi.

"Baki ji ba."

Ta dakata a inda take, ta juyo a hankali ta sauke idanunta cikin nashi

"Wannan ya zama karo na karshe da kafarki zata kara takowa cikin ofis din nan."

Ta san baudaddun halaye irin na Aqeel Mukaila, ta san zai iya duk wani abu da ya furta a bakinsa.
Ta sanshi, zai iya fadar ko wacce irin magana ba tare da ya damu da ciwon da zata haifar ga mutumen da ya fadawa ba.
Ta sanshi farin sani, sai dai bata taba tsammanin zai wulakanta ta har haka ba, bata taba tsammanin zai bullo mata ta wannan hanyar ba.

HAWAYEN ZUCIYA!Where stories live. Discover now