10 - DR. AQAQ SAIFULLAH

6K 589 293
                                    

Ranar ta kasance alhamis, a cikin yanayi na hunturun watan janeru.
Iskar sanyi mai dauke da hazo tana busawa, da yawan mutane suna cikin gidajensu a kulle.
Kusan kwanaki takwas da faruwar al'amarin kenan, amma walwala da jin dadi nema suke su yi kaura a wurin jama'ar gidan Arch. Izzaddeen Abdulwahaab.
A hankali ta fito zuwa inda Ummi ke zaune, ta samu gefenta ta zauna, ba tare da tace kala ba.
Tausayinta Ummi ta ke ji, tun ranar da abun ya faru, bata kara furta ko kalma daya ba, har izuwa yanzu.

"Ummi kun gama shiryawa ko?"

Ta dago tana kallon Huzaif da ke daura agogonsa, yana karasowa inda suke zaune.

"Mun gama Huzaif, amma ai ba da kai zamu je ba ko?"

"Ya za ai in barku ku tafi ku kadai? Bayan shima wannan ba sanin halinshi muka yi ba? Ni wallahi kowa ma tsoro yake bani yanzu."

Murmushi tayi, wanda iyakacinsa fatar baki,

"In banda abinka wa yace maka duka aka taru aka zama daya kuma? Shima wancen kaddara zamu kira shi. Zai fi kyau ka zauna, saboda Areefa, na san Abbanku ma zai iya kira ko wanne lokaci."

Ta mike tana sanya hijabinta. Shima komawa yayi ya zauna, bai ce komai ba, ta kama hannun Nasreen suka doshi kofar fita.

"Ummi.."

A hankali ta juyo tana kallonsa,

"Ya aka yi?"

"Ummi dan Allah ki kula da ita, ko da wasa kada ki barta daga ita sai mutumen da baki sani ba."

Murmushi mai ciwo tayi, ta girgiza kai kawai, ta juya suka fita.

Yola Central Psychiatric suka dosa, ba su sha wahala wurin ganin likitan ba, kasancewar Dr. Jameela ta yi musu tanadi a wurin, sunansu na cikin jerin wadan da zasu gana da shi a ranar.
Mutum na karshe da ke gabansu ne ya fito daga ofishin likitan, kafin wani ma'aikaci yayi musu izinin shiga.

Fari, dogon likitan, mai shekarun da za su kai hamsin da bakwai, zaune a bayan teburinsa mai cike da fayil-fayil, da kwamfuta mai zaman kanta ya dago ya fara nuna musu wurin zama, cikin turancinsa da yayi yanayi da harshen Indiyawa.

Gaishe shi Ummi tayi bayan sun zauna, ya ansa da murmushi kunshe a kan fuskarsa.

A hankali ya dago yana kallon Nasreen, idanunta a kasa, tana wasa da yatsun hannuwanta.

"Me ke tafe da ku?"

Ya tambaya bayan ya maida dubansa ga Ummi.

Bata san ta ya zata fara bayani ba, bata san yadda zata saka matsalar 'yartata yadda zai iya fahimta ba, domin kuwa, abu ne da zata iya cewa ya samo asali, tun daga lokacin da ya kamata a ce yaro ya fara tasawa.

Hannayenta ta hade wuri guda, ta dora su a teburin da ke gabanta, kafin ta fara jawabin da bata san ya karshenshi zai kama ba.

"A lokacin da ya kamata ace yara sun fara tasowa, zai zamana kamar tsakanin watanni takwas zuwa goma na farkon haihuwarsu. Yawancin yarana a wannan lokacin zaka ga suna tafiya ma, da bakinsu, da kuma wayonsu. Sai dai abun ya sha ban-ban ta bangaren Nasreen. Ko alama, bata yi wannan ba. Har ta cika shekara guda, bata san komai ba, bata wasa irin na yara, idan anyi mata, bata maida martani. A lokacin da ta cika shekara biyu, ya kamata ace ko sunanta ta iya ansawa, to amma, idan zaka kwana kiranta, baza ta taba nuna alamun da ita kake yi ba. Bata da aikin da ya wuce mata jera ababen wasa. Ko da suka isa shiga makaranta, bata maida hankali a karatun, illa yawan zanunnuka da take yi a littafin darussanta. Bata kaunar kasancewa kusa da kara ko mun kankantarsa, bata iya hada kallonta da na mutane, uwa uba, bata iya magana ko da ta minti guda, a yanzu haka, da ta ke da shekaru shidda kenan."

HAWAYEN ZUCIYA!Where stories live. Discover now