"Yaaa Huzaif?"
"Unnhumm. Ko kina mamaki ne?"
"Ba dole ba, yaushe ka dawo?"
"Mintina arba'in da suka wuce."
Ya fito daga bangaren direba, ya bude sashen mai zaman banza
"Shiga muje, tun hawayenki basu kafe a wurin ba."
"Yaa Huzaif!"
Muryarta cike da wasu sinadarai masu bayyanar da farin ciki, a wani bangaren kuma suna inganta bakin cikin da zuciyarta ke ciki.
"Dan sunce baza su dauke ki aiki ba shine abun kuka?"
Bayan sun dauki hanya sosai, yayi maganar idanunsa na kan titi ba tare da ya kalle ta ba.
Itama din ci gaba tayi da goge gilashinta da farin kyallen da ta fitar daga ma'adanar gilas din"Ni fa ba kuka nike ba. Abu ne ya fada idona."
Shiru yayi tamkar bai ji abinda ta fada ba, domin kuwa ya san koma menene ba zai rasa nasaba da Aqeel Mukaila ba.
Ko da Ummi ta je mishi da shawarar sama mata aiki a kamfaninsu bai bata goyen baya ba, kasancewar ya san babu abinda hakan zai haifar bayan koma ma yar gidan jiya.Da Allah yayi rantsuwa, da ace Aqeel ba jininshi ba ne, da babu abinda zai dakatar da shi daga kona mishi zuciya fiye da yadda ya shafe shekaru yana hura wuta mai tsanani a raunatacciyar zuciyar yar uwar, da ya fi kauna fiye da kowa, fiye da komai.
"Ba zan iya aiki da su ba Ya Huzaif. Ban san me yasa Ummi ta boye mun abinda zan tarar a can ba."
Idanunta na kallon waje tayi maganar, hawaye masu dumi suka cicciko a fararen idanunta, suka kuma taimaka wurin canja launinsu.
Bai yi mamakin jin furucinta ba, dan ba wannan ne karo na farko da ta kan kona zuciyarshi da kalamanta ba, ba wannan ne karo na farko da su kan bayyanawa juna sirrikan da zukatansu ke ciki ba.
A wasu lokutan, su kan fahimci halin da junansu ke ciki tun basu furta ciwon da ke kasan zukatansu ba. Hakan baya rasa nasaba da shakuwa da kaunar da iyayensu suka gina su a kai tun fil azal.Duk da tazarar kusan shekaru goma da ke tsakanin Huzaif da yan biyun kannenshi, hakan bai hana shi zame musu abokin shawara ba, in banda Areefa da a wasu lokutan ta kan nuna fandarrarrun halayenta, da sai yace basu da wata matsala ta rayuwa. Sai dai kusancinsu da Nasreen yasa ko murmushi tayi, zai iya bashi fassara dai-dai da abinda ke kasan zuciyarta ba tare da ya kuskure ba.
"To kuma meye abun kukan?
Ya san baza ta ansa shi ba, ya dora da
"Shekaru biyar Nasreen..
Five good years, amma baki manta da shi ba?
Yaushe zaki motsa a rayuwarki?
Yaushe zaki manta abubuwan da suka shude a tarihin da, da ni, da ke, da duk wani mai kaunarmu ba zai so ya maimaita kanshi ba?Zan iya rantsuwa da Allah, na san irin zafin da zuciyarki ke ciki, but Nasreen, you've to move on.
Forget about him and all that happend because of him. I'm here Nasreen, ga Ummi, a kullun burinta bai wuce mata son ganin farin cikinmu ba..and Abba, duk da bashi da isasshen lokaci, haka yake wadatar damu da duk abinda ya san zai faranta rayukanmu.
Ta bangaren Umma ma babu abinda zamu ce da ya wuce Alhamdulillah. It's just Areefa.."
YOU ARE READING
HAWAYEN ZUCIYA!
RomanceBetrayal, love, and tragedy. Dive into the most beautiful love story of Nasreen Izzaddeen and Aqeel Mukaila AbdulWahab.