Ba'a dade ba suka iso aka daukeshi Ummu ta bisu Khameelarh tanata kuka ta bisu amma Ummu taki yarda dakinta ta kuma ta fada kan gado tana cigaba da kukanta.
Ummu suna isa Hospital aka fara gwada Abbu aka gano irin wancan ciwon da yayi ne da aka kaishi Saudiya amma suna ganin kaman tashi yayi ko wani abu ko kuma akwai raguwan guban a cikinshi saboda haka nan da nan aka shirya a maidashi ta private jet nashu ba'a bata lokaci ba aka kama hanya shide be cikin hayyacinshi Ummu kowa na gefanshi tanata mai add'oi kala-kala duk wanda yazo mata kai seta mai ta tufa mai
Haka ta ringa mai. Khameelarh kowa bayan ta dade tana kuka can seta dauka wayanta ta kira number El_Armeen bwesty ta tace mai yazo gidansu she needs a frnd right now
Be bata lokaci ba yazo kowa daya shiga gidan dayake sunsanshi(securities) suka bude mai ya shigo parlo ya shiga babu kowa a ciki dan haka ya zauna ya kira number ta. Bata dauka ba seta sauko kasa yana ganinta ya mike da sauri cus her hair was a mess and idon nan sunyi ja gashi ya fara kunbura
"Dude what's wrong?" (Sunan da suke kiran junansu kenan dashi for fun)
"Abbu..." Seta fashe da kuka
Huging nata yayi niyan yi but yasan be kamata ba dan haka seya tsaya yana tambayanta meyafaru dashi
"Beda lafiya"
Kwantar mata da hankali ya shigayi yana bata shawara akan addu'a ya kamata tayi mai ya samu sauki. Harde ta dena kuka amma still bata sake ba.
***"A yau din nan nakeson ayi poster na WANTED asa hotan Marwan din dead or alive duk wanda ya ganshi 10million har a gidan radio da T.v a baza kun gane koh!?"
Vice president ne ke maganan nan shida Dove da Eagle a parlo yana tsaye ya kasa sukuni se zaga parlon yakeyi
"Mun gane Boss. Amma ina zamu sama hotanshi" Dove ya tambayaWani mummunan kallo Vice yamai daga baya a tsawace yace
"Kai wanna irin dakiki ne? Kai jahilin karshe ne wlh, baga social media ba ko Instagram! Wait ba phone dinshu na nan ba? Mstewww jaki kawai"
Ya sake aeka mai da zagi yayi gaba a zuciye
Kallonshi sukeyi dansun fara gajiya da wulakancin da yake mashi.Acan dakin kowa Mammi batayi bacci ba kuka kawai takeyi kaman ranta ze fita har muryanta ya dashe. mijinta kowa har'a lokacin be cikin hayyacinshi, a yanxin muryanta a hankali yake fita abun tausayi ita abunda ke damunta batasan ko yaranta sun tsira ba, watakila ma sun kashesu ko kuma wani abu ya samesu. Abunda keta mata yawo aka kenan har gari ya waye.
Can tayi zurfi a tunani kaman daga sama se taji Abbah yana karanto addu'oi a hankali idonshi a kulle, hawaye ne ya cigaba da kwaranyo mata ita a rayuwanta bata taba saka wannan abun a tunaninta ba wai tau sune aka kamo kaman karnika duk arzikinsu da gatansu amma yau sune a daure gashi basusan halinda yayansu ke ciki ba 'Ohh Allah'
"Allahunma ajirni fi musibati fi haza wa kalifni kairan minha. Allah ga bayinka na neman taimakonka Allah ka tsirar da yarana da mijina Allah ka tuna ma wa'an nan mutanen asiri ka turatasu a duniya"
A zuciyanta take wanan addu'oin
Can Abbah ya bude ido dan yaga matanshi ae kowa acan ya hangota duk karfinta ya kare se wani ajiyan zuciya take ta jingina da kujeran abun tausayi
Mikewa yayi niyanyi amma babu hali cus an daureshi da kacha an daure kafanshi gu daya se hannayenshi gefe-gefeDa yagade ba iyawa zeyi ba seya kuma shima ya gingina da bango yana cigaba da addu'a a zuciyanshi da kariya dan shine kawai ze taimakeso at this moment.
***Manal ce ta fara bude ido a hankali saboda hasken da ta gani
Tana ganin inda suke se abunda ya faru ya fara dawo mata juyawa ta farayi tana neman Ya'Marwan
Can ta hangoshi a sume dakyar ta iya mikewa danta bege waist nata sosai tana kuka tana jan jiki harta isa gunshi
A hankali ta fara
"Ya'Marwan Ya'Marwan" tana tabashi kawai se taga jini a gashinshi da sauri takai hannunta gun ae kowa sega inda jini yake fitowa
Burgicewa tayi ta fara girgizashi da karfi amma shiruKanta takai kan kirginshi tayi placing kunnenta a kirginshi tana gin heart bit dinshi
Ae kowa taji a hankali ajiyan zuciya tayi sannan ta ciro dan kwalinta ta daura mai akai inda ta tabbata anan yaji ciwo. Jakan har yanxin yana bayanshi a goye.
Kallonshi ta tsayayi hawaye na kwaranyo mata kaman ruwa 'Wai itace yau ke tausayin kanta. What did they did to deserve this? Sun rabu da iyayensu which she is not sure ko zata kara sakasu a idonta ga only hope dinta yana kwance rai a hannun Allah gashi they are in the middle of no were. Kuma ba iya fita zatayi ba balle ta nemo taimako'
Kuka ta sake saki ta jingina da jikin Marwan abun tausayiAn fara ma Abbu aeki amma the worst part is wancan Doctor da yayi mai aiki wancan karon an kasheshi dan two days back aka cince gawanshi a gidanshi bayan ya dawo daga masalaci
(Allah ka kara mana imani)
Tou yanxin wani aka samu yana mai aikin Ummu tana waje ta zauna tayi shiru kawai itade wannan mulkin bala'i kawai yake kawo masu ba komai ba.--hrs later--
Khameelarh ta rasa inda zatayi ta kira Ummu taji jikin Abbu gashi har'a News an fara yadawa Mr. President babu lafiya an maidashi Saudiya. Shiru kawai tayi tana kallon T.v El_Armeen na kusa da ita.Vice president kowa da yaga News dariya suka saki da Senate president hadda rawa (tsofafin banza) wai komai yazo masu da sauki sede suyi focusing akan su Marwan kafin a kawo gawanshi Nigeria.
A yanxin har an baza a ko'ina ana neman Marwan wanda ya fita da kanwanshi akan yayi kisan kai ko'ina maganan ake ga posters ko ina
Shi bema san abunda ake ba yana can kaman gawa. Manal tayi kuka tayi kuka ta girgizashi harta gaji ta mike ta fara kokarin fita daga ramin dan neman taimako amma ta kasa ta duba babu ko inuwan mutum a wajan tayi ihu harta gaji ta kuma ta kwanta baccin dole ya kwasheta badan dadi baCan kawai Marwan ya motsa kanshi ya wani amsa besan lokacin daya saki ihu ba dan azaba a furgice Manal ta tashi tana kallonshi yana rike da wajan rikeshi tayi shi kowa kallonta ya tsayi
"Ya'Marwan karka taba"a hankali tayi maganaCire mata hannunta yayi daga jikinshi yana kallonta da mamaki
"Waye Ya'Marwan and who are you?"...💋💋💋
Love and kisses
Queen Tye
YOU ARE READING
The Presidential Throne!
Fiksi UmumThe choices we make in life are between good or bad! Sometimes we don't get to make the choices for ourselves. In every bad memory I could still remember that happened to me, in every pain i went through that i could still feel on my flesh, in every...