KANA SONA?

3.4K 135 11
                                    

Naaanaaa naaanaaa muryar ummah nah tsinkayo tana kirana da sauri na mike tsaye na karasa wajanta don amsa kiranta, umma ga ni,yauwa Nana kije gidan kawu dahiru kice mah inna RABI wai ta baki sakon,saboda gobe zan wuce bauchi kuma babu daman nah amsa gobe saboda jirgin 8:00 zan bi,sannan idan kina dawowa ki biya ta gidan hajiya saudat itama ta baki sakon wajanta,kar ki tsaya yin shirme ki kai dare awaje Nana,toh na dai gaya miki domin indan kika yi dare babu ruwana zaki hadu da yayanki.ga key din motana ki tafi dashi,Nana b fast don't stay long.



GIDAN INNA RABI

Salama alaikum
Wa'alaikumus salama,muryar Waye nake Ji kamar naanaa eh,hhhhhhhhh inna ni ce
Ina wuni,lafiya lau ya gida ya ummarki lafiya lau inna,itama ta aiko ni wai na amsa sako awajanki domin da safe za ta fita gobe,Allah sarki ai jiya yarima ya tafi bauchi sai kawai na bashi sakon ya kaimin,Ashe itama tafiyar tazo,eh wallahi inna sai sa mah ta aiko ni, inna ina su ummeeter neh da rahma ko tare suka je bauchin,a'a Ba tare suka je ba ummeeter taje gidan kawunku Bello ita Rahma bata dawo makaranta Ba,au nazata sunje ganin tsofonfi neh,inna bari na tafi kafin nayi dare ki gaida baffa da su rahma,toh Yar albarka zasu Ji ki gaida ummanki,toh inna zata ji ,said da safe


Driving take tana listening to song din Ariana grande na Everyday bata ankara ba tazo kwanan Layin gidan hajiya saudat kawai suka gama kai da wani mota,sai da ta ja numfashi tukun kafin ta kalli motar da suka yi karo da ita,baki ce motar kirar highlander mai tintet glass,tana kallon motar neh taga mai motar ya zura kafa ya fito daga motar a fusace,ya doso motar ta,kyakyawa neh na karshe,fari neh yana da tsayi ga hancin kamar fensir da karamin bakinsa a ovary shape na fuskar shi,sanye yake da farar wandon jins da bakin T-shirt ga side buns din dake fuskarsa da Dan gemu sai ya Sanya fuskar sa yayi kyau sosai,bata gama kare mai kallo ba ya kwankwasa mata glass din mota,zuge glass din tayi tace am sorry without giving him d privilege to yell at her,he just kept quite and turned without saying a word.
Numfashi ta ja sannan ta kunna mota tayi baya dashi sannan tayi gaba abinta,shima juya kan motar yayi zai koma gida domin mood dinshi ya chanza,horn tayi a wani tangamemen gida mai gadi ya bude mata kofa ta kusa ciki tayi parking sannan ta fito ta kalli gaban motar Ashe mah batayi komai ba sanna tayi cikin gidan da yanayin tafiyarta mai sanyi,sallama tayi sannan ta shiga bayan an amsa sallamar, oyoyo oyooyoo Abdulkareem ne yayi huging din naanaa yace didi sannu da zuwa bari na kira miki momy,didi Aisha ta fita shopping, dariya tayi tace good my boy,yaron da bazai fi shekara goma ba yayi gudu ya haura stairs yana momy ga didin gidan ummana tazo,momy dake daki ta fito tace hala batar hanya didin naka tayi tana fada tana saukowa daga stairs murmushi naanaa tayi sannan tace momyn naaanaaa ina wuni,kar kiyi min dadin baki domin nasan wannan zuwan aiko ki akayi Ba haka nan kika zo ba,momyna knan wlh kinsan yanayin karatuna ban samu tym sosai kuma abokin fadana bayanan sai sa,momy tayi murmushi Faisal manya amma ai kuna waya koh,sosai momy kinsan mai rabamu sai ya shirya,lallai kam amma yayanku ya dawo,ido ta zaro wah? badai yaya haidar Ba eh shi fa,lallai kam yananan neh a'a kun sha bambam ya fita,Wow what a relieve, momy kin San mai na tuna,a'a naanaa momy lokacin Idan muna wasa da Aisha ya haidar will Neva let us bee,he bully us very much,Sallama yayi kafin momy ta bata amsa domin daman tun dazu yake kofa yana jin zance dah suke yi domin had zai shigo yaji an kuma sako shi cikin maganar,shiru tayi bayan kallo daya da taimai daman wannan gida wannan guy din yake,muryar momy taji tana cewa ka dawo babana,hakan neh yasa ta gane cewa ya haidar neh,ana cikin haka sai ga Aisha ta shigo da gudunta tana ihu ta kiran sunan naaanaaaa,tashi Naanaa tayi ta rugume ta suna ihun jin dadi,wani tsawa sukaji an daka musu sai da suka tsorata musamman man naanaa Wanda bata son fada balle tsawa,da sauri ta ruga waje ta bar Jakarta da key din motar a wajen tana mai da numfashi wannan ai ko thunder albarka,dariya Aisha ta fashe dashi domin daman ta San naanaa da shegen tsoro gashi kuma tana mata sha'awar aurar ya haidar,wani mugun kallo yayi ma Aisha tayi sauri gimtse dariyarta momy ma dariya tayi tace ajiye kayan ki ki kai mata gyalenta da jaka sannan ki bata wannan ledar kice mata na CE sai da safe,aifa saboda Ba dawowa ciki za tayi Ba sarkin tsoro shi knan yaya daga yau kuma ka zama dodo domin da ta ganka zata rinka tashi awajan.murmushi yayi sanan ya wuce bangarensa ya tunani shirmen naanaa,ke matsarociya kin badani wallahi,dariya tayi Nima Addu'a nake Allah ya yaye min donmin wani lokaci abin nima tsoro yake ban domin maimakon na rage tsoro sai wani karawa nake,uhmmmmm Allah dai ya kyauta kizo ki koma gida domin babynah duk Inda yake nasan yana hanyar gida gashi magrib ya kusa,masu baby anji jiki hhhhhhhh ta Shiga mota tayi reverse tana mata waving sannan tayi hanyar fita daman baba mai gadi ya bude mata gate koh,baba sai an kwana biyu yauwa yata Allah yayi Albarka.


Tana kai wa gida ta hango motar yaya mubaraq,wayyo na bani am dead duk momy neh ta wani jani da magana uhmmmm,parking tayi ta dauko Jakarta da ledar sakon sannan ta fara tafiya tana kalle kalle kamar munafuka tazo shiga cikin gida suka ci karo da umma,Allah ya so ki bai tambayi idan kike ba da kin Sani,kai umma wlh momy da Aisha neh suka tsaida in,babu wani surutun ki ya tsaida ki dai,murmushi tayi ta wuce daki ta ajiye mata sakon sannan taje dakinta,sallah tayi ta shiga wanka tana fito wa ana kiran isha'i zani ta daura tayi sallah sannan tasa kayan barcinta Riga da wando baki tana hula sannan ta fito palour,ummah wai daman ya haidar ya dawo neh baki fada min Ba,tab ai yau sai daya ban tsoro wlh duk na zata thunderstorm ne da yayi tsawa agidan momy daxu don kawai muna murna ni da Aisha,ai yayi min dai dai domin Ku Ba hankali gare Ku Ba dake da Aishar,ya baraq neh ya shigo yana cewa ai aishar ta fita ahankali,tab ta ina ta fini ai wlh na fita,ummah race toh da meye kwadu ta fi gaya,dariya tayi tace ummah da mai(oil) dariya baraq yayi ya Dana mata duka,wayyo ya Burma min baya,kai yaya wlh akwai zafi fa,wlh baku da banbanci da ya haidar,murmushi yayi kawai,ummah wai yaushe Abbana mai sona zai dawo neh,ki kira shi ki tambaye shi mana,kai ummah bakya sona na
Zan koma gidan momynah mai sona aiko Dana Ji dadi domin daman ke kika ki komawa,tab ai wlh babu inda zani yanxu da thunderstorms ya dawo naija ai gwanda yayana na kaina yafi Ji dani,ko ya baraq murmushi yayi sannan yayi side huging nata yace yes my baby sisto amma kinsan kene baki jin magana koh a gyara hali mu zauna lafiya u hear.yes sir ta Sara mai duk sukayi dariya.


Please rate me,this is my first write up and if there ix any mistake please kindly comment no insult pls,thank you........

KANA SONAWhere stories live. Discover now