Chapter 15

827 40 0
                                    

Wannan page din naki neh safiya, Allah barmu tare.

Washe gari misalin karfe 2:15 aka daura auran Aliyu haydar da amaransa khadeejah naanaa da hajara kan sadaki dubu sittin sittin, sannan aka daura na Mubaraq da Aisha akan naira dubu sittin, sai fatima da Alhaji jafar, sannan Ameena da Ibrahim duk Akan naira dubu sittin. Bayan nan ne aka fara gaigaisawa tare da fatan alkhairi, imam ne ya tambaya Abba akan auran Mubaraq, wanda iya saninsa mata biyu zai aura, Abba yace toh shi angon ne yace ya fasa kuma bai fada mana dalilin fasawar ba, dana ce mai bai isa ba sai an daura cewa yayi ana daurawa wlh saki uku zai mata atake, shine na ga gwara dai kar amai da ita bazarwar dole a fasa kawai, masha Allah cewar imam, toh Allah sa hakan shi yafi alkhairi ameen.

Bangarensu naanaa kuwa taji labari mai dadi daga wajan haydar, na farko na daurin aurarsu sannan kuma nah plan dinta da ya inganta, hamdallah tayi tana mai gode mah Allah da tayi achieving goal dinta na hana auran ya baraq da nuratu, Aisha ce ta rungume ta tana kuka sannan take cema mata how would i make it up to o, you have done a lot for me, i wish i can prevent yours to, shush silent dear, u can make it up to me by taking care of my brother and kar ki damu dani, hajara bata da matsala sai dai kawai i don't like her neh, cox of some personal issues amma will be fine so don't worry kinji, toh tace sannan naanaa ta share mata hawaye, amaryanmu daina kuka kinji. Dariya suka yi sannan suka taahi don ana kiransu su je ayi hotuna,

Karfe uku aka kama hanyar kano kai fateema don kano za su zauna, ameena ma an wuce da ita Abuja, karfe shida aka kai naanaa da Aisha don tare akan shigar da su gidajensu, gidasu na facing din juna, gida dai yayi kyau kowa na santin gidansu, karfe takwas aka fara kwashe kawayen amare don zuwa wajan dinner, lokacin da haydar ya iso ya kira naanaa da hajara su fito don tare zasu tafi lokacin duk kowa ya wuce, kaya iri daya naanaa da hajara suka sa lemon green dinner gown da black head mai lemon green stone sai sheki suka dan kyau, daman naanaa mai kyau ce gashi kuma ta hada da simple make up, don cewa tayi she want it dah way, ita ma nuratu akwai kyau dan ita farace sosai gashi kuma tayi make up very heavy one sai kace yar ruwa, kallonsu yayi dukkansu biyu sannan yace masha Allah kunyi kyau murmushi hajara tayi sannan tace mun gode, naanaa yake tayi kawai babu ko uffan, bayan  sun kai wajan har sun shiga ayi settling neh aka fara program din inda abokan angwayen suka yi bayani ataikace, sannan kawayen amarya, da akazo kan naanaa neh aka kira Abdulkadir wato sweety, yazo yana ta koda amarya wanda har sai da kishi ya turnike hajara, naanaa na lira da ita daman da gangan tayi hakan don tasan sweety neh kawai yasan yarantar ta sosai so shi zai iya bayani akanta ya fada mah haudar ko ita wacece, and sakon da take so ya isar ya jsarko.

Bayan nan aka saki waka aka ba amare da angwaye siyi rawa, hajara bikin cikin duk ya isheta, ita ko naanaa rawa ta zage tana yi barin ma ganin yar uwarta Aisha afili sai abin ya kara mata dadi sosai, lika musu kudi aka fara barin mah naanaa don ta birge mutane da yawa wansu kuma suna zagin ta wai amarya bata da kunya tana rawa ranan bikinta.
Daga karshe haydar ya ja hannunsu suka koma wajan zamansu, wajan yanka cake da feeding neh ya ba hajara haushi kuma, don sai da ya sama naanaa cake abaki kafin ya sama mata drink kuma yasa mah hajara kafin naanaa, shi duk so yake ya kwatanta adalci amma ahaka wasu suna ganin baiyi ba,haka dqi aka rinka dinner har aka tashi taro wanda wasu ya musu dadi wasu bai musu ba.





BAYAN BIKI DA SATI UKU

Naanaa ha hango a main palour tana waya da deejarh, Allahu akbar deejarh Allah yasa abarni nazo kaduna wayyo babynah, Dan Allah ki turo min hoton jaririyar ta whatsApp nagani, ihun take tayi tana tsalle don murna tayi da aganin, azuciyata ne ummeeter kuma nace kar ki je ki samu ki haifi naki dai, hajara wanda ihun naanaa ya tashe ta fito azuciye tace mata wai ke mai sa bazaki rinka abun irin na masu hankali ba, naanaa tace tab wlh kinsan waye mara hankali amma bani ba, tsaki hajara tayi zata wuce naanaa tace zama dai zaman mijina nake ba zaman wata mai hankali ba, tayi dariya sannan ta wuce dakinta ta bar hajara awajan, hajara kuma ta shaka ita dai tasan ba zagin ta naanaa tayi ba amma abinda ke mata ciwo shine naanaa zata takalo fada amma ko ta zage ta bata ramawa da zagj sai ma tayi praising dinta, kuma abin na bata haushi, yau kwanar haydar uku da komawa aiki duk gidan baya ma hajara dadi domin shi ke debe mata kewa s
daman, ita naanaa daman bata damu da sabgarsa ba so kusan kullum cikin fada suke, barin ma idan ranan dakinta zai kwana toh fada za suyi mai girma su kwanta suna fushi da juna, amma don iskancin naanaa sai ta tashi tace mai ina kwana, tayi kamar basu suka kwana fada ba, tun abin na bashi haushi sai ya fara bashi tsoro, gata da dariya babu gyara babu dalili, abin ya na tayar mai da hankali. Kuma ya lura da cewa duk ranar girkinta neh hakan keh faruwa, ana gobe suna ne ta kira ya haydar da safe, bayansu gaisa sai tace mai yana maganar zuwa kaduna,ce mata yayi yau zai dawo ta bari gobe ya kaisu ita da hajara, kj tayi ta fara mai kuka, oh my god toh ya isa yi shiru kuji, tsit tayi, ajiyar zuciya yayj sannan yace naanaa maisa rigimarki sai karuwa take yanxu mai abun kuka anan, shasheka ta fara, ya isa nace koh,uhmmmm tace sannan gace Mubaraq zai kai Aisha yanxu domin zai je Abuja wani seminar kuma jibi zai dawo so sai ki bisu, dariya tayi sannan tace thank you so much dear, u re welcome yace sannan suka yi sallama, daman kayanta ashirya take bayi ta fada sannan tayi wanka ta zauna ta tsalla kwalliya Kamar mai shirin zuwa gasar kyau, bayan ta shirya ne ta fito taje dakin hajara tayi mata sallama akan ita ta tafi kaduna, har da kara neman magana, tana cemata wai ta bar mata mijin ta dafa shi ta cinye, kuji nimar zance fa, hajara ba amsata ba, kaeai cewa tayi adawo lafiya, fita tayi da sauri don aisha na kiranta, tana fita ta ga motar su ta fito daga gida, gaishe da yayanta tayi bayan ta shiga motar sannan ta juya kan aisha, a'aa matan yaya wannan kyau, ga fresh ga kara kiba gaya mana sirrin mana kodai abin ya iso neh, dariya aisha tayi sannan tace sannu yar sa ido, Mubaraq dai bai gana zancensu ba, lokacin da suka kai dankande neh taji kanta ya sara sannan gabanta ya fadi, addu'oi ta rinka karantawa tana istigifari, jingina tayi da kujera motar sannan ta rufa ido. Bata ma san an kawo gidan deejarh ba kawai ji tayi aisha na ce mata toh fito gimbiya, murmushin karfin hali tayi sannan ta fito ta wuce jikin gidan, wajan la'asar taji ita kawai malt take jin sha ta fito ta sami yaro ya bakin gate ta gaggara ya siyo mata mai sanyi kuwa, baba mai gadi ta gani ta gaishe shi, zata wuce ya kirata, yaki 'yata, mai sunanki tace khadeejah baba, Allah sarki sunan matana gare ki Allah sunan kawarki kika zo, eh kawatace sosai sannan mijin ta yayana neh, Ayya amma shine baki son zuwa wajanta, Allah sarki baba nima auren gare ni ai sai an barni ka gani zai yi wuya ba sha'ani ba ace an barni na zo, haka neh cewar baba, toh baba bari na shiga daga ciki nasan ana nema na yanxu, toh 'yata sai kin kara fitowa, tana shiga deejarh tace keh daga zuwa siyan malt sai ki dade haba, dariya tayi sannan tace haba ai  ni barci zanyi yanxun nan, ta magana ga sha malt, bayan ta shiga ta kwanta dayan dakin ne wata yar uwar deejarh ta takalo tace keh naanaa ki tashi zan kwanta, mardiya ban gane in tashi ba, ba anan kika zo kika ganni ba, toh don na ganki sai meye gado dai ba ubanki bane ya siya so maisa zaki zo kij, ji kake kau.......  Naanaa neh dauke ta da mari har kin isa ki tsaya ki tsagi mahaifina, ehhhhhhhh wlh sai na,,,,,,,,,,, kawai sai ta tafi luuuu ta fadi kasa, deejarh neh ta ahigo dakin domin anje angaya mafa abunda mardiya take aikatawa, na shiga uku ni khadeeja naanaa, shiru tayi sannan tace ma sauransu fita ya rage sai ita sai Aisha da farida, kuka Aisha take oh ni ai don't want to experience these again, ihun naanaa tayi, these isn't about mardiya, akwai wani abun, ihu naanaa take, farida ma hawaye take, matsowa tayi kusa da naanaa sannan ta dago ta tasa a kafarta, please ku sake haka, ku idankun motsa ba'a iyawa da ku ku hanata ibada kuma kuki magana dan Allah ba don mu ba ku yi hakuri ku barta haka nan, aisha tace nasan tun amota kuna kusa amma ba zata zaku zo ba, haka suka rinka ba aljanun hakuri har suka gaji suka koma kallonta, tun karfe 10:00 har karfe hudu shiru sai wajan karfe biyar da kwata suka yi tafiyarsu bayansun barta da azababben ciwon kai, barci take mara dadi, don mummunar mafarki take tayi wai gata gefen wani kogi babu hanyar gudu gashi wani abu na dumfaro ta amma ta kasa guduwa, addu'a ta fara yi kawai sai ta farka a firgice..

Pls do comment and vote love you all.



KANA SONAWhere stories live. Discover now