SHINE GATA NA

583 30 1
                                    

🌸 *SHINE GATA NA*🌸

Story &written By
           👇🏻
'''Aysher Abbakar(m eerah)'''

® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
    ​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on wattpad @aysherabbakar.

*Bismillahir Rahmanir Raheem*

*dukkan godiya ya tabbata ga Allah mad'aukakin sarki daya bani ikon dawowa Dan Isar da sak'on dayake k'unshe cikin wannan tak'aitaccen labari,wannan labari nayishine badan kowaba,wannan k'irk'irarren labari be,ina rok'on duk Wanda wannan labari yayi dai-dai da rayuwarshi,da yayi hak'uri badan shi ko it's nayiba,dafatan zaku bani had'in kai kuma kubiyoni a sannu danjin yanda labarin ze kasance.*

*1-2*

Matace y'ar kimanin shekara talatin da biyu zaune kan sallaya ta idar da sallan asuba,gefenta kuma yarone k'arami da baze wuce shekara goma ba yana zaune ya zuba mata ido,bayan da idar da sallan ne ya gaisheta cikeda ladabi,shuru ne ya ratsa d'akin na kusan minti biyar, dubanta yayi yace"Amma yaushe zaki kaimu wajan babanmu"?

Share hawayen da yake shirin gangaro mata tayi sannan tace"kamal yau zakaga babanka"

Tana gama fad'in haka ta mik'e ta nufa wardrobe ta janyo k'aramin jaka da baze d'auka kayan da yawuce kala uku ba,kayanta ta d'auka kala d'aya Dana kamal shima kala d'aya sannan naga ta d'auka kayan 'yarta mace Wanda take goyo 'yar shekara d'aya da rabi,seda ta tabbatar ta had'a duk wani abunda zasu buk'ata sannan ta rufe jakar.

Toilet ta shiga ta had'awa kamal ruwa yayi wanka sannan itama tayi tata wankar,jinjirarta ta d'auko Wanda naji suna kiranta da *farzeen* itama tayi mata wankan.

Basu wani 6ata lokaciba suka gama shiryawa,k'arfe shida da rabi suka fito agida suka nufa tasha,kai tsaye motar daze kaisu cikin garin Adamawa daga mubi suka shiga,basu wani 6ata lokaciba mota tacika suka d'auka hanya.

Cikin ikon Allah suka isa, adaidaita suka nema suka shiga yakaisu har k'ofar gidan.

Wani katafaren gida naga sun nufa,knocking k'ofar sukayi nan megadin ya lek'o,gaisawa sukayi sannan ya tanbayesu wasuke nema,a tak'ice tace mishi 'yan uwanshine daga mubi,d'an Jim kad'an yayi sannan ya dubeta yace"gaskya hajiya Alhaji be fad'amun yau yanada bak'i ba kiyi hak'uri"

Dubanshi tayi tace"Dan Allah katemaka mun akwai dalilin zuwana"

Kaman bazeyi maganaba sekuma yace"ki d'an jirani zanje in sanar dashi"

Bejira amsar da zata bashiba ya juya ya nufa cikin gidan.

Alhaji Abdulkarim da duk abnda ake akan idonshi yayi nuni wa megadin da hannu alamar yashigo dasu,ba musu kuwa yajuya da Sauri ya musu iso har cikin palour.

Waje suka nema suka zauna,kamal se bin parlour yake da kallo a ranshi fad'i yake"wato ubanmu yanada wannan kud'in amma yabarmu wani duniya?"

Kusan minti talatin suka shafe suna zaune,harsun gaji da zama sannan sukaji alamar tafiya,d'agowa tayi ta bi kan steps d'in da kallo,Alhaji Abdulkarim ta hango shida wata mace bafulatana da bazata wuce shekara ashirin da biyarba biye dashi.

Atare suka k'araso,gaisheshi sukayi a dak'ile ya amsa kaman be ta6a ganinsu ba,dubanta yayi cikin rashin kulawa yace"inace dai lafiya"?

Shuru tayi sannan tace"dama kamal ne yatakura yanason ganin babanshi shine nakawoshi yayi kwana biyu kafin sukoma makaranta"

Yatsina fuska yayi had'eda dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu sannan yace"ni in ina buk'atan ganinsu zanzo,kedai kawai kicemun kud'ine bakidashi shiyasa,Dan haka zan baki kud'i kiyi maza kijuya base anjima ba"

Hawayene yacika mata idonta tadubeshi tace"tunda nake nata6a zuwa Neman alfarma wajanka?ba Abunda ya kawoniba kenan"

Ko kallonta beyiba yazaro bunch na dubu d'add'aya guda biyar ya wurga mata yace"ga wannan inya k'are kituro a kar6a miki wani amma karki sake zuwamun"

Kamal da tunda aka fara wannan bala.in ya koma gefen Amman shi ya k'ank'ame ka'fanta se 6ari yake na tsoro.

Hawayenda  ta 6oyene ya gangaro mata,tsugunawa tayi ta kwaso kudin duka,shikuwa ganin ta d'iba kud'inne yasashi juyawa shida matarsa Wanda tunda aka fara maganan batace komaiba se murmushin da take,tana gama kwashe kud'in ta d'ago ta dubeshi,ganin har yakai kan step yana shirin komawa sama yasata had'a kan kud'in ta jefeshi dashi a k'eyanshi,da sauri ya juyo jin an kwad'a mishi Abu,kud'inda yabata yagani ta jefeshi dashi,cikeda bak'in ciki da kuka tafara magana tace

"ba Abunda ya kawoniba kenan,Allan daya hallicemu be hanamu Abunda zamu ciba,kuma in Allah ya yarda se kaga k'arshenka"

Tana gama fad'in haka takama hanun Kamal ta gyara goyon Farzeen ta d'au jakanta ta fice tana kuka.

Kamal ma kukan yake yace"Amma na kiyi hak'uri kiyafemun bansan haka zemiki ba"

Shafa kanshi tayi tace"babu Abunda kamun Kamal,Allah ya muku Albarka"

Dubanta yayi yace"Amma bazan sake zuwa wajanshiba kuma banasonshi"

Kasa cewa komai tayi saboda tsananin k'una da zafin da zuciyar ta ke mata.

Tafe suke suna kuka daga ita har Kamal har suka Isa tasha,motar mubi suka shiga Dan komawa gida.

Zaune suke a mota,gaba d'aya ta nema kukan tarasa,zuciyanta ne kawai ke mata zafi,duban Kamal tayi dayaketa faman ajiyan zuciya tace

"Kamal ko bayan raina kamun Alk'awari zaka kula da k'anwarka *Farzeen*,kaga ynxu bamuda kowa se Allah,bayan raina zaka kasance *Kaine gatan ta*"

Gyad'a mata kai yayi yace"Amma na bazaki mutu ynxu ba in shaa Allah "

Murmushi kawai tayi tace"nidai kamun Alk'awari"

Yace"namiki Alk'awari Amma zanzama gatan Farzeen"

Tunda ga lokacin bata sake cewa komaiba ta mayar da kanta ta jingina jikin window, motar ta cika tafara tafiya.

Farzeen kuwa tana cinyan Amma kamal yana mata wasa,basu tsaya ko inaba se tasha,fitowa akafarayi a motar,Kamal ne ya dubi Amman shi dayaga ta k'urawa wani waje ido ko k'yaftawa batayi,ta6ata yayi yace"Amma na kizo mutafi gida mun iso"

Shuru bata amasaba,ta6ata yayi yaga ko motsi batayiba,girgizata yafarayi yasa kuka yana Amma na kizo mutafi gida.

Wata matace ta lek'o tadubeshi tace "samari lafya"?

Yace" Amma nane inata mata magana bata amsaniba,dubanshi tayi tace"d'auko 'kanwarkar kufito"

Bamusu ya d'auko Farzeen yafito ya tsaya,nan matar ta shiga motar ta ta6a Amma,salati tasake had'eda ta6ata ko motsi batayi bare numfashi.


For comments 08144932303

SHINE GATA NAWhere stories live. Discover now