SHINE GATA NA 8

175 6 0
                                    

🌸 *SHINE GATA NA*🌸

Story &written By
           👇🏻
'''Aysher Abbakar(meerah)'''

® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
    ​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on wattpad @aysherabbakar.

*da Allah amun hak'uri jiya bansamu halin typing ba,wlhy wayata ne ba chaji,kuma lokacin da nasamu chaji gaskiya bacci ya kamani bazan iya typing ba,shiyasa yau nayi k'ok'ari nayi da ya wa,dafatan masu cewa zasuci tarana zasu min afuwa,nagode da soyayyarku gareni,Allah bar zumunci,ina sonku irin sossai d'innan*

*15~-16*


Ganin bashida amsar tanbayar ne gashi ya zauna yana 6atawa kanshi lokaci ga yamma tayi ya sashi mik'ewa,kitchen ya shiga ya sauke shinkafar daya d'aura ya soya mai sannan ya sauke,zuba musu yayi shida Mubarak sannan ya zuba wa Amina ma,zama sukayi sunaci haka babu ko gishiri balle maggi,farar shinkafa ce kawai se mai,shi kanshi bajin dad'in abincin yake ba,turawa kawai yakeyi saboda yunwan da take k'wak'ular cikinshi,Amman shine ta fad'o mishi,tunawa da irin Abincin da take musu yayi,lokaci d'aya ya fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya,Mubarak ne da Amina suka bishi da kallon mamaki,kuka yakeyi sossai kamar yau Amma ta mutu.

Mik'ewa yayi da gudu yayi d'akinta,kulle k'ofar yayi da key ya zube k'asa ya takure  waje d'aya ya ciza gefen le6enshi se kuka yake yana fad'in"Amma na meyasa zaki tafi kibarmu?me yasa baki tafi damuba?Amma na kintafi kin barmu bamusan komaiba,bamuda kowa a duniya,bamuda gata  seke se Allah,gashi kintafi kin barni da farzeen,Amma kullum farzeen seta yi kuka tana kiranki,Amma na muna tsananin buk'atarki,Amma babu Wanda yake kula damu,Amma ya zanyi da Alk'awarin da kika barmin na farzeen"

Haka ya damk'e zaninta Wanda ta mutu dashi ajikinta yana kuka,kukan shine ya tayar da farzeen a bacci,itama kukan tasaka,da gudu ya k'arasa wajanta ya d'auketa ya rungumeta,dukansu kukan suke babu me rarrashin wani.

Seda yaga tanajin yunwa ne ya bata madara ya goyeta ya fito waje idonshi taf da hawaye.

Mubarak ne ya k'araso wajanshi yace"kamal meya sameka?"

K'wallan idonshine ya zubo ya dubi Mubarak yace"Amma na"

Abunda ya iya fad'a kenan ya wuce ya nufa wajan garkensu.

Basu abinci yayi da ruwa sannan ya kwashe kashinsu ya Tara chan gefe sannan ya kulle su.

Gida yashiga ya d'auko manyan jarakunan da Ammanshi take zuba madara ciki guda shida ya fito dasu waje ya nufa wajan rijiya.

Jan ruwa yayi ya zuba yashi ciki ya wanke,ganin jarakunan ne yasashi ganin Amman shi a idonshi lokacin tana talle.

Wani kukan yafara yanayi yana wankewa yana fad'in"Amma yanzu ni zan fara tallen,ina buk'atan kud'in da zan kula da farzeen.

Seda ya wanke duka sannan ya shiga dasu gida ya shanyasu,lokacin har magrib yayi,alwala yayi sannan ya shinfid'a sallaya ya kwance goyon farzeen ya ajiyeta gefenshi yace"farzeen d'ina karkiyi kuka sallah zanyi"

Nan yayi sallah kaman yanda Amma ta koya mishi sannan ya kunna musu fitila ya rungume farzeen ya jingina da kujera.

Salamar kamal da Amina ne ya sashi daina tunanin da yake ,dukansu kowa d'aukeda abinci ahanunshi,Amina ce ta kar6a farzeen ta zaunar da ita tafara bata tuwo,nan farzeen ta fara ci sossai,seda ta k'oshi sannan Amina ma taci nata,seda kamal yaga farzeen ta k'oshi sannan hankalinshi ya kwanta ya fara ci shima.

SHINE GATA NAWhere stories live. Discover now