SHINE GATA NA NA HUD'U

160 7 0
                                    

🌸 *SHINE GATA NA*🌸

Story &written By
           👇🏻
'''Aysher Abbakar(m eerah)'''

® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
    ​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on wattpad @aysherabbakar.

Wannan shafin nakune shine gata na fans,nagode da kulawarku,ana mugun tare 🤝

Akwai Wanda sukamun magana ta private akan sunaso nakara yawan typing,in Shaa Allah zanyi kokari,abubuwa sunmun yawane amma zansan yanda zanyi.nagode sossai

*7-8*

Cikin gida kuwa Fatima ce wajan matan sarki,seda tayi wajan awa d'aya da 'yan mintina sannan ta farfad'o,kuka tasaki tana "wayyo Umma na,Yusuf d'ina,Abba na sun mutu,nashiga uku"

'Daya daga cikin matan sane ta rungumeta tana rarrashinta,saboda gaba d'aya a birkice take,Abdulkareem ne yashigo d'akin,tana ganinshi tasake kuka tana cewa"wayyo Allah umma ta tatafi tabarni,banida kowa banida komai su kad'ai nakeda kuma Allah ya kar6e kayanshi.

Tausayinta ne ya kamashi ya kamata ya kwantar kan cinyarshi yana rarrashinta,se sauke ajiyar zuciya take.

Haka suka cigaba da zama gidan sarki,bintu kuwa kullum cikin kuka, cikin k'ank'anin lokaci gaba d'aya tafita hayyacinta,ta rame tayi bak'i gwanin tausayi,gashi wani lokacin intafara kuka tari idan ya sark'eta har suma takeyi.

Abdulkareem kuwa ganin rashin lafiyanta gaba-gaba yakeyi gashi koyaushe cikin wahala dasu ake yaje yasamu sarki yace zasu tafi zeje gida iyayenshi sumata jinya.

Sarki yaso suzauna amma ganin hankalinshi yafi kwanciya ta gida hakan yasashi amincewa.
  Washe gari suka shirya tsaf yashiga wajan matan sarki yamusu godiya ya d'au kayan bintu suka fito suka shiga fa'da,bintu ne da Abdulkareem zaune gaban sarki,nan sarki yayita mata nasiha da banbaki,dasuka tashi tafiya yamusu goma ta arziki sannan ya had'asu da fadawa yace su rakasu Dan bintu taga garken shanun da iyayenta suka bari da tumakai Dan sune kawai suka tsira sanadiyyan tafiya kiwon da sukayi.

Hakan kuwa akayi,bayan sunje sunga garkenne daga nan sarki yake tanbaya ya za.ayi dasu,Abdulkareem ne yace"ranka ya dade idan munkoma gida lafiya ni zanzo da k'anina mukorasu zuwa mubi.

"Hakan yayi" inji sarki.

Nan sukayi musu sallama suka nufa tasha suka kama hanyan mubi,tunda bintu wannan Abu ya afku magana ya gagareta,sedai ta amsa da kai,hakan ba k'aramin d'agawa mijinta hankali yayiba,kai tsaye gidansu Abdulkareem suka nufa,Inda yayi wa iyayenshi bayanin abunda yafaru,sossai hankalinsu ya tashi suka tausayawa halin da bintu take ciki,ga rashin lafiya kullum gaba gaba yake,ganin abun ba sauk'ine suka yanke hukuncin kaita asibiti,tunda anyi na gargajiya amma bawani cigaba.

Hakan kuwa akayi,asibiti aka kaita,basu gado akayi saboda batada isheshen jini balle ruwa,seda tasha ruwa Leda goma sha biyar jini Leda uku sannan likitotin suka soma shirin yimata test d'in abunda ke damunta.

Gwajin farko da.aka mata aka gano ciwon zuciya ya kamata,ba k'aramin birkicewa sukayi ba,tayaya za.ace 'yar shekara goma sha tara ace ciwon zuciya.

Itakuwa bintu ko damuwa bata nunaba saboda rashin iyayenta shiyafi komai damunta,saboda batasan kowa aduniya ba se su kuma sunkoma wajan mahaliccinsu.

Nan aka fara mata magani,cikin sati biyu tafara samun sauk'i sedai duk abunda taci setayi amanshi.hakanne yasa aka mata test,gwajin faro aka gano tana d'auke da juna biyu,murna wajansu ba.a magana,kulawa na musamman suke bata,kwanansu sha biyu aka sallamesu suka koma  gida.

Wani d'aki aka gyara musu suka zauna itada Abdulkareem nan suka cigaba da jinyanta har cikinta ya girma ya Isa haihuwa ta Haifa kamal.

Tun daga lokacin bata sake koda 6ari ba,kiwon shanunta ya koma hanun mijinta yanda taga yana kula dasune yasata damk'a mishi komai ahanunshi,abunda bata saniba kuwa shine duk ranan kasuwa yakan d'auka shanu biyu da kuma madarar daya tatsa yaje yasiyar batareda kowa yasaniba.

Bata ankaraba dayake sunada yawa se watarana da yamma kamal yafita wasa tanaso tamishi wanka bata ganshiba,gyalenta ta d'auka tafita tanufa wajan garken shanu dayake anan yake wasa,tsayawa tayi tana kallon yanda shanun suka koma basufi guda hamsin da biyarba cikin d'ari.

Batace komaiba ta kira kamal tamishi wanka zuciyanta fal tunani,aranta kuwa fad'i take toko kiwo ya kaisu.

Ganin bece mata komaibane yasata yin shiru bata mishi maganaba.

Kamal Nada shekara shida aduniya Abdulkareem ya saki bintu saboda taga shanu sun k'are sun koma talatin da shida, raguna kanma Biyar ne yarage,maganan data mishine tace"meya sami shanun taga sunata k'arewa ko rashin lafiya sukayi suka mutu be fad'a mataba"

Shikenan ya hauta da masifa wai  ya kula Dan taga dukiyantane shiyasa take mishi gadara,Dan haka shi baze iya zama da Wanda bata yarda dashiba taje ya saketa saki uku.

Lokacinda haka yafaru ba k'aramin firgita bintu tayiba,Dan zubewa tayi awajan ta suma, bayan ta farfad'o kuma ciwonta ya tashi nan tafara aman jini,ko tausaya mata beyiba dayake iyayenshi basu nan sun tafi k'auyensu,Duk Abunda yafaru kan idon kamal ne,shikuwa ko ajikinshi yawuce yafita ya barsu sannan ya nuna kamal yace idan yadawo ya samesu wallahi seya kashesu,jin hakane yasa kamal sakin kuka ya rungume Ammin shi datake ta faman amai,mik'ewa yayi yashiga d'aki ya d'aure musu kayansu da duk abunda Ammin shi tanuna mishi da hannu Dan takasa magana duk ya had'a ya d'aure musu yana kuka.

Kamata yayi tatashi suka nufa wajan garkensu ya d'aura wa shanu biyu kayansu ya kwancesu duka shanu da tumakan ya d'au Sanda suka d'au hanyan Adamawa,insun gaji su tsaya su huta,in yunwane ma su tatsa ruwan madarara shanu susha,ahaka seda sukayi kusan sati ahanya sakamakon rashin lafiyarda Ammi takeyi.

Gidan iyayenta dayaci wuta suka nufa Inda yazama kango,ahaka suka shiga wajan duk yayi k'ura,kamal ne ya zaunar da ita yashiga ya kad'e sannan ya shinfid'a musu tabarma,gidansu ko rufi babu Ballan tana katako,tsoro ne Yakama kamal ganin dare yafara yi gashi duhu ya mamaye wajan,duban Ammin shi yayi yace"Amma wajan yayi duhu gashi bakida lafiya,barina nemo Abu na kunna mana wuta",kafin tace wani Abu har yafita ya zaga ta bayan gidansu,itace ya nemo yazo yahad'a musu sannan ya kunna musu da dutse,da k'yar Yakama sannan wajan ya haska,shinfid'a yayiwa mamanshi yace"amma na zoki kwanta anan"

Dubanshi tayi tausayinshi ya kamata,kwalla ne yacika mata ido,da sauri ya k'araso yace"amma na inane yake miki ciwo?k'irjinki ne?"

Rungumeshi tayi tasaka kuka,ganin haka shima seya kama kuka seda sukayi me isarsu sannan tayi shuru,cikin sheshshek'ar kuka tafara magana"Allah seya saka mana Abdulkareem in shaa Allah,Allah shine zezama gatanmu"

Bacci 6arawone yayi awon gaba dasu rungume da juna,da safe kamal yatashi ya tatso musu madaran saniya suka sha,ya fita yace mata yana zuwa.

Seda tabarshi yafita tsoro yacika ta,ganin besan ko ina agarinba,hasalima be ta6a zuwaba Dan tahowansu ma itace take masa nunin hanya da hannu.

Hankalinta ba k'aramin tashi yayiba ganin har awa uku ya shafe amma babu kamal babu labarinshi.

To ina kamal yayi?




For comments only 08144932303

SHINE GATA NAWhere stories live. Discover now