SHINE GATA NA 9

162 7 0
                                    

🌸 *SHINE GATA NA*🌸

Story &written By
           👇🏻
'''Aysher Abbakar(meerah)'''

® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
    ​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on wattpad @aysherabbakar.


*17-~18*

'''wannan shafin nakune masoya kamal,allah bar zumunci'''


Sallama Malam sanda yake yana k'arawa,mai gari ne yafito ya dubeshi fuska a d'aure yace"kai banason rashin hankali,ko cemaka akayi gidan kurame ne?"

Sunkuyar da kai yayi yace"tuba nake ranka shi dad'e"

A tare suka Shiga d'akin,ganin kamal ne yasashi fara washe baki yace"aah ka kawo kud'in kenan"

Mai gari ya daka masa tsawa yace"kai in bazaka nutsu ka kama hanya kafita banason iskanci"

Shuru dukansu sukayi daga bisani mai gari ya dubi Malam sanda yace"wai ko zaka iya fad'amun yaushe marigayiya ta siya fili a wajanka kuma har kabata takardu batareda tagama biya ba?"

In ina Malam sanda yafari yace"umm umm ai saboda yardar da nayi da itane yasa Na bata takardun"

K'ura masa ido mai gari yayi,nan Malam sanda yayi k'ifi -k'ifi da ido yana sunne kai,mai gari ne yace"wallahi kaji tsoron Allah,dukiyan marayu in kaci babu abunda zai amfanar da kai,ba kuma zai cireka daga talaucin da kake ba"

Shuru yayi sannan yace"nifa ranka ya dad'e gaskiya nafad'a"

Girgiza kai yayi sannan ya Ciro dubu Biyar ya damk'awa Malam sanda yace"gashi,kud'inka saura dubu goma,nanda kwana uku kazo ka kar6a"

Washe baki Malam sanda yayi har hanunshi yana 6ari ya amsa kud'in,yana fad'in "ah madalla Allah ya kaimu"

Ko tsayawa yaji abunda mai gari ze fad'a mishi beyiba  ya saka takalminshi ya fice ya damk'e kud'in kaman za.a k'wace.

Mai gari ne ya dubi kamal yace"shikenan kamal jeka abunka,Allah zai saka muku"

Nan kamal ya mik'e ya fita ya samu su Amina da farzeen suna zaune.

Dubansu yayi "yace mutafi gida muje mu tatsa madarar gobe kafin magriba yayi ko Mubarak"

Ummi ce tayi saurin cewa"eh maza tashi kutafi,Amina ki goya farzeen kinga magriba yayi"

Goyata sukayi suka kama hanya suka fita,suna Isa kamal ya bud'e k'ofar gidan suka shiga,kai tsaye wajan shanun sukayi suka fara tatsan madara,seda suka d'iba Wanda zai ishesu siyarwan gobe,gida suka koma suka zauna.

Sunayin sallah suka kwanta.

Washegari kaman yanda kamal yayi da sassafe suka d'ura madara jarka biyar, kamal ne ya d'auko sauran Na jiya Wanda ya rage ya had'a,seda yayiwa farzeen wanka ya bata madara sannan suka tafi.

Cikin ikon Allah yau duka ya k'are,haka ya dawo da kudi dubu shida da 'yan canji,sauran ya siyawa farzeen tsaraba.

Kullum haka kamal yakeyi har yagama biyan Malam sanda kud'inshi.

Maimakon ya daina tallen bai fasa ba,haka kullum yake zuwa talle,da Mubarak ya tanbayeshi me zeyi da kud'i seyace farzeen yakeso yasata a makaranta kamar yanda yaga yaran masu kud'i suna zuwa.

Dariya Mubarak yayi yace"kai kud'in makarantar fa da yawa"

"Eh nasani kuma nan nakeso farzeen d'ina tayi,haka zanyita Tarawa kafinnan ta k'ara girma.

Kullum inyaje talle ya dawo zezo musu da abunda zasuci,Dan yadaina girki saboda Dama ba iyawa yayiba.

Haka duk cinikin da zeyi zekai kud'in wa Ummi mahaifiyar su Mubarak,yace Tatara mishi Na makarantar farzeen ne.

*Bayan shekara d'aya*

Kwanci tashi ba wuya shekarar farzeen biyu da rabi, ta dad'a girma gata da 'yar k'iba gwanin sha.awa gata fara,zaune take cinyan kamal yana tace mata gashi da comb,sai zuba mishi surutu take.

Ahankali ya dubeta yace" farzeen d'ina kinaso in saki a makaranta?"

Dubanshi tayi tace"meye makalanta hamma na?"

Shuru yayi yarasa me zaice mata,can yace"yanda su umar suke zuwa da safe kullum a mota"

Dasauri tace"nima a mota zakana kaini?"

"Banida mota ai farzeen"

"To zaka kaini a saniya?"

Can ya dubeta yace "eh zankaiki"

"To kasani a makalanta hamma Na"

Suna zaune Sega umar d'in kuwa akan doki,farzeen ne taduba yayanta tace

"hamma Na zaka siyamun irin wannan saniyan?"

Tayi maganan tana nuna dokin.

"Wannan ai ba saniya bane farzeen doki ne"

"Eh shi nakeso,kasiyamun se kana kaini makalantan akai"

Shuru yayi yarasa mai zai cemata,dubanshi tayi cikeda shagwa6a zatayi kuka tace"bazaka ciyamun ba?"

"Zan siya miki kinji?"

Rungumeshi tayi tace"yauwa hamma Na"

Washegari da yamma Sega kamal da doki d'an k'arami,tun daga waje kamal yake k'wala mata kira,da gudu tafito tana ayoyo hamma na.

Ganinshi da dokine ya sata k'arasawa da gudu tace"hamma wannan saniya nane?"

Yace"doki sunanshi farzeen"

Tsalle tafara tace "aurani"

'Daukanta yayi ya d'aurata yana zagawa da ita sai dariya take tana ihu.

Shima dad'ine ya kamashi Dan babu abunda yakeso kamar yaga farin cikin farzeen.

Seda magriba yayi sannan ya sauketa,nan ta tubure wai tare zasu kwana,lalla6ata yayi yace ze d'aure mata shi ta wajan windonta sannan ta yarda.

Dubanshi tayi tace"hamma Na yaushe zaka kaini makalantan?"


Wayyo kuyi hak'uri da wannan wallahi nagaji

   For comments only 08144932303

SHINE GATA NAWhere stories live. Discover now