🌸 *SHINE GATA NA*🌸
Story &written By
👇🏻
'''Aysher Abbakar(meerah)'''® PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303Follow me on wattpad @aysherabbakar.
*5-6*
Durk'usawa Kamal yayi gabanshi,idon shi cike da k'walla ya rungume farzeen yace"Dan Allah kayi hak'uri zan nema na biyaka"
Dariya Malam sanda yayi ya dubi kamal yace"kaida baka wuce raino ba tayaya zaka nema kud'ina kabani?kama San nawane kud'in?"
Shuru kamal yayi kaman yana tunani sannan yace"ko nawane zan nema na baka ahankali,Dan Allah kayi hak'uri dashi muka dogara se wannan garken"
Malam sandane ya dubeshi yace"baze yiwuba fa,katashi kashiga ka d'auko min takardun gonan nan kakawomin,inkuma bazaka d'auko ba ni nashiga na bincika na d'auko, inkuma kunfison gonan to Ku tattara kayan ku Ku bani gidan da kuke ciki sena bar muku gonan"
Kuka Kamal yasaka ya rik'e k'afan Malam sanda yace "Dan girman Allah kayi hak'uri wallahi zan biyaka"
Me anguwa ne mahaifin Mubarak yazo wucewa yaga Kamal durk'ushe yana kuka,k'ara sowa yayi ya dubi Kamal yace"Kamalu lafiya kuwa?"
Karap Malam sanda yace"k'udin gona nane da mahaifiyar su ta mutu bata cikamun ba,shine yanzu nazo ko yabani takardun gona na ko kuma yabani gidan da suke ciki amma ya tsaya kai da fata wai ze biyani,nikuma bansan a ina ze samo yabani ba"
Me anguwa ne yadubi Kamal yace"A ina zaka samu kud'inshi kabashi Kamal?"
Yace"ko madarar shanu zanna shiga cikin gari in rink'a siyarwa harna gama biyanshi"
Malam sanda zeyi magana me anguwa ya d'aga mishi hannu yace "haba sanda,wani kan ci albarkacin wani,amma inba rashin tausayi ba wannan marayun ae abun tausayine,tunda yace ze baka kayi hak'uri mana"
Shuru Malam sanda yayi sannan yace"yaushe zaka kawomun kud'ina?"
Kamal yace"kullum zanna shiga cikin gari idan na siyar zanna kawo kud'in wa ranka dad'e(me anguwa) se yana baka"
Girgiza kai kawai Malam sanda yayi ya koma kan keken shanunshi ya tafi.
Me anguwane ya d'agoshi yace "tashi kaji Kamalu,Allah ya muku Albarka"
Mik'ewa yayi ya koma wajan garkensu d'aukeda Farzeen hanunshi ya zauna,Dan tunda Amman shi tarasu gaba d'aya bayason zaman gidan,Dan kuka zeyita yi inbai ganta ba.
*WANENE KAMAL DA FARZEEN*
Kamal da Farzeen 'ya'ya ne ga Fatima Wanda suke kira da *Amma* Fatima asalinta bafulatana ce ta jihar Adamawa,ita kad'aice mace Wanda iyayenta suka Haifa se k'aninta na miji guda d'aya me suna Yusuf,Fatima tataso cikin gata da kulawa tun tana k'arama harta girma,tanada shekara sha takwas ne taje kiwon shanu itada k'anninta yusuf suka had'u da mahaifin su Kamal wato Alhaji Abdulkareem moh'd,da farko Fatima k'inshi tayi,seda mahaifinta yayi bincike akanshi aka tabbatar mishi mutumin kirkine sannan mahaifanshi mutanen arzikine sannan mahaifinta yasata agaba yana mata nasiha,dayake Fatima 'ya ce me biyayya seta amince batareda wani gardama ba.
Cikin k'ank'anin lokaci shak'uwa da soyayya me tsanani ya shiga tsakanin mahaifinsu da mahaifiyarsu,ba.a d'au wani lokaciba manya suka shiga magana har aka musu baiko daga bisani aka Sanya ranan aure.
Akwana atashi ba wuya,yau aka d'aura auren Fatima da Abdulkareem,da k'yar Fatima aka rabata da k'aninta Yusuf da mahaifanta,kuka take sossai dayake a mubi zata zauna,lokacinda akazo tafiya da itane mahaifinta ya kira Abdulkareem ya dank'a mishi amanar Fatima,ba musu ya mishi Alk'awarin rik'eta amana.
Bayan aure da sati biyune rikici ya 6arke a Adamawa,yanda akayi ta.adi sossai aka kashe mutane,lokacinda Fatima taji labari ana fad'a garin Adamawa kuma ta yankinsu hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba,Dan kuka tayita yi tanace mishi yakaita gida taga mahaifiyarta,haka dai yayita nusarta yace tayi hak'uri in fad'an ya lafa ya mata Alk'awari zasuje.
Da k'yar yasamu ta hak'ura amma ba Dan hankalinta ya kwanta ba.
Bayan anyi fad'a da sati d'aya Fatima suka d'au hanyar Adamawa,Wanda tunda suke tafiya gabanta Ke fad'uwa,lokacinda suka iso k'ofar gidansu hankalinta ba k'aramin tashi yayiba,Dan numfashinta sark'ewa yayi,ganin gidan a k'one kaman babu halittar da yata6a rayuwa cikin gidan.Zaman dirshan tayi awajan tasaki wani irin kuka Wanda babu hawaye,Abdulkareem kuwa yarasa abundan ze fad'a,inna lillahi wa inna ilaihir raji'un kawai yake maimaita wa,sunkai minti talatin ahaka, ganin basuda mafitane yasashi k'arasawa kusa da ita ya tsuguna ya kama hanunta yace"bintu tashi mu gangara gidan sarki muji abunda yafaru,kinga nan babu kowa ballantana musamu Wanda zamu tanbaya"
Shuru tayi babu alaman tanada niyan tashi,se numfashinta dayake fita da sauri-sauri,kamata yayi ya d'agata suka fara tafiya ahankali har suka iso fada.
Labarin da aka Sanar dasu ba k'aramin firgitasu yayiba,barinma bintu da tayanki jiki ta fad'i a sume.
Sarkine ya umurci masu mishi hidima dasu d'auketa su shiga da ita ciki,haka kuwa akayi.
Abdulkareem kuma anan ya zauna cikin birkici da rud'anin jin abunda ake fad'a mishi.
For comments only 08144932303
YOU ARE READING
SHINE GATA NA
Fanfictionlabarine me cikeda tausayi,nishad'i,had'eda fad'akarwa,Ku biyoni don jin yanda zata kasance