SHINE GATA NA SHIDA

141 5 0
                                    

🌸 *SHINE GATA NA*🌸

Story &written By
           👇🏻
'''Aysher Abbakar(meerah)'''

® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
    ​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on wattpad @aysherabbakar.

*wannan shafin nakune,pure moment of life(p.m.l),ina sonku irin sossai d'innan,ana mugun tare🤝*

*11-12*


Ido hud'u sukayi da Abdulkareem amma ya kau da kai yayi kaman bai ganeta ba,itama hakan yafi mata Dan bata k'aunan abunda zai had'ata dashi,hasalima bata son ganinshi.

Bayan tagama siyar da nono ne a hanyar ta na komawa gida suka had'u dawani mak'wabcinta Wanda suka zauna anguwa d'aya a mubi.

Gaisawa suka tsaya yi nan yake mata jajen abunda yafaru,tace bakomai haka Allah ya k'addara,nan sukayi sallama har ya fara tafiya ta tsayar dashi,k'arasawa wajanshi tayi,gani nayi sun tsaya suna magana amma dayake ina nesa banji Abunda suke fad'a ba.

Gani dai nayi ta kwance bakin zanin ta ta Ciro kud'i masu yawa tabashi sannan sukayi sallama yatafi.

Itama gida tanufa,isowarta kenan tasamu kamal harya gyara musu gidan ya share ya d'ibo ruwa.
Yana ganinta ya nufeta da sauri ya kar6a k'waryan hanunta yace"Amma na sannu da hanya"

"Yauwa sannu kamal"

Nan ta zauna ya kawo mata ruwa tasha ta jingina kanta,fatan ta Allah yasa maganan da sukayi da mak'wabcinta Allah ya taimaketa yasa mata hannu.

Haka rayuwa yacigaba da tafiya kullum idan ta tashi daga ciniki sai wannan mak'wabcin nata yazo ya amsa kud'i hanunta.

A cikin watannin dasukayine har bintu ta lura da tana d'auke da juna biyu,hankalinta ba k'aramin tashi yayi ba amma bata fad'awa koda kamal ba.

Hasalima zani take d'aurawa akai,haka tayita rainon cikinta har yakai wata shida.

Yau ma kamar kullum mak'wabcin nata me suna mallam hudu ne yazo,ji nayi yana cemata nanda wata biyu za.a kammala komai,saboda yau kusan shekara kenan kullum seyazo tabashi kud'i.

Kwanci tashi babu wuya,cikinta yashiga wata takwas kuma yaune sukeda shirin tashi daga cikin Adamawa zasu koma mubi.

Kamal ne yaga yau bata fita talle ba se faman had'a kaya take,duban ta yayi yace"Amma ina zamuje?"

Shafa kanshi tayi tace"mubi zamu koma kamal"

Zaro ido yayi yace"wajan babana zamu koma?"

"A.a kamal ba nan zamu koma ba,gidanmu zamuje"

Cikin rashin fahimta yace"Amma inace nanne gidanku?"

"Kamal banason yawan magana,idan munje zaka gani"

Daga haka bai sake cewa komaiba har tagama musu shirinsu tsaf,mik'ewa yayi yanufa garken su ya kwance duka shanu da awakan,tayata yayi suka d'aura kayansu kan wasu shanun,nan suka kama hanya suka fara tafiya,kai tsaye hanyar mubi suka d'auka,insun gaji su zauna su huta, ga Amman shi d'aukeda tsohon ciki ga tafiya me nisa,kwana uku sukayi amma gaba d'aya tafita hayyacinta,dubanta yayi cikeda tausayi da kulawa yace"Amma na ki hau kan saniya kawai"

Dariya maganan yabata tace"bafa jaki bane kamal,karka damu ae zuwa gobe da daddare ko jibi zamu Isa.

Haka sukayita tafiya,yau Allah yayi isarsu mubi,suna Isa suka had'u da mak'wabcin ta,nan naga ya shige gaba ya musu jagora,wani anguwa naga sun nufa,bawani tafiya mai nisa sukayiba naga sun k'araso wani tafkeken gida me girman gaske,key naga yasaka ya bud'e gidan,nan Amma tashiga kamal ma binta kawai yakeyi,nan suka zazzaga gidan.

Gida ne me girman gaske,d'akuna guda shida  ko wanne ciki da Palo,uku kuma duk da band'aki,se tafkeken Palo a tsakiya da kuma wani d'an fili ta gefe,bayan sungama zaga gidanne suka fito waje,can gefe kuma wani k'aton fili ne Wanda a k'alla ze d'au garken shanu biyu da k'arin dabobbi,ga rijiya ta chan gefe da k'aton rami da aka ginashi shima cike da ruwa.

Bayan ya gama nuna musu ne ya dubi bintu yace"ya kikaga wajan?yayi?"

Murmushi tayi idonta taf da hawaye tace"wallahi yayi, ban ta6a tunanin wajan yakai hakaba,Dan bansan kud'in da nake baka yayi yawa har haka ba"

"Ai kuwa kud'in sunada yawa,kinfi shekara fa kina bayarwa,kiyi lissafi kigani"

"A.a basai nayi ba,nagode sossai Allah bar zumunci ya baka Abunda kake nema duniya da lahira"

Nan ta kwance bakin zaninta ta Ciro wasu kud'i ta irga dubu talatin ta mik'a mishi sannan tace"gashi nasiyar da gidana na Adamawa Wanda muka tashi,dubu Ashirin sauran cikon kud'in wancan filin kiwon ne,dubu goma kuma naba ka ne nagode sossai"

Farin cikine ya rufe Malam hudu yace"a.a hajiya bintu ai kingama biyana"

"Eh nasani wannan kyauta ne kawai saboda dad'in abunda kamun na Alkhairi"

Zubewa yayi yanata mata godiya seda tace ya Isa"

Shikuwa kamal kuwa a ranshi fad'i yake wannan gidan waye?



   For comments only 08144932303

SHINE GATA NAWhere stories live. Discover now