SHINE GATANA NA BIYAR

167 9 0
                                    

🌸 *SHINE GATA NA*🌸

Story &written By
           👇🏻
'''Aysher Abbakar(m eerah)'''

® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
    ​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on wattpad @aysherabbakar.

Wannan shafin nakune shine gata na fans,nagode da kulawarku,ana mugun tare 🤝

*Akwai Wanda sukemun magana ta private akan na turo musu book d'innan daga farko,maganan gaskiya kunyi yawa masu buk'ata amma tun jiya nafara tura ma wasu, da Allah ina rok'on duk Wanda yamun magana yaga banturoba yayi hak'uri zan tura in shaa Allah ,in kuma anjini shuru ban turaba seku tunamun plx saboda zan iya mantawa,I heart u guyx,ana tare irin sossai dinnan*

*9-10*

Fitowa bintu tayi bakin k'ofar kangon su ta tsaya tana lek'e-lek'e ko zataga ta inda kamal ze fito amma shuru,takai kusan minti talatin tsaye ta sa k'a wannan ta kwance wancan,ta sake lek'a bayan gidan nan ta hangoshi tafe rik'i -rik'i da kayan kara da chiyayi akanshi,zuba mishi ido kawai tayi tana tunani da tausayin d'an nata har ya iso yanda take.

Zuba karan yayi a k'asa ya dubeta cikeda kulawa yace"Amma na mekike nema?"

Murmushi tayi tace"kai nake nema kamal,naganka shuru ne shine hankalina ya tashi kuma naga baka San ko inaba"

Dariya yayi yace"Amma gani nan na dawo to,mushiga ciki kinga zan rufa mana jinkan mune kinga jiya sanyi ya damemu"

Hawaye ne ya cika mata ido tayi saurin kau da kai karya gani.

Tayashi tayi suka shiga da ichen da karan,sama ya hau sannan ya dubeta yace"Amma na zaki iya mik'amun ina sakawa?"

"Eh xan iya kamalu na"

Nan ta rink'a mik'a mishi yana rufawa har ya rufa musu d'aki d'aya sannan ya sauko duk kararen sun kuje mishi jiki wasu kuma sun yanka mishi hannu.

Bayan ya sauko ne ya tattara shirgin d'akin ya kaisu d'aya d'akin da babu komai,ya nemo chiyayi ya d'aure ya share d'akin sannan ya shinfid'a musu tabarma,ya d'au labule Amma ta d'agashi sama ya buga musu da dutse da k'usa sannan ya sauko.

Cikin k'ank'anin lokaci waje ya gyaru,komawa sukayi suka zauna yana mayar da numfashin gajiya,can ya d'ago ya dubi Amma yace"Amma na kinga yau zamuyi bacci me dad'i ko?"

Rungumeshi tayi cikeda tausaya wa Kansu tace"in Allah ya yarda kamal,Allah maka Albarka Allah ya baka memaka"

Dayake yarone kawai se yayi dariya.

Seda ya huta sannan ya mik'e ya dubeta yace"Amma barinaje na kad'o shanu kinga yamma tafara yi,gashi ban tatsa mana madarar da zamu shaba har yanxu.

"Allah kiyaye hanya banda wasa"

"Yanzu zan dawo"

Fita yayi ya nufa jeji bakin kogi yanda ya kad'a shanun,Ahanya yana tafiya ya tsaya ya musu itace ya d'aure sannan ya nufo hanyan gida,seda ya kora shanun inda suke kwana sannan ya dawo yashigo d'aki,yanda yatafi ya barta haka yadawo ya sameta tayi tagumi.

Zama yayi yace "Amma kinga nayi mana icce a hanya Dan nasan kingaji da shan d'anyen madara kinga semu dafa kuma mubar wani yazama nono ko?"

Kaman dama yasan Abunda ya dameta kenan tace "yauwa kamal Allah maka Albarka,barina had'a mana wuta"

Mik'ewa tayi ta kunce kayan da kamal ya had'a musu ta fiddo tukunyar k'asa da tulu guda d'aya,tsayawa tayi tana tunanin inda zata samo ruwa,kaman yasan tunanin da take ya d'au tulun ya fita da gudu,be tsaya ko inaba se bakin rafi,seda ya ciko sannan ya dawo yace "gashi kinga sekiyi amfani dashi sauran kuma semu sha muyi sallah,gobe da safe kafin natafi kiwo sena d'ibo na wanka ko?"

Itadai batace mishi komaiba Dan basirar yaron yana bata mamaki.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya tsakanin kamal da mahaifiyarsa,inda suke rayuwarsu su kad'ai hankali kwance.

Yau gaba d'aya cikin tunani tatashi,kamal ne ya dubeta yace"Amma bakida lafiya ne?"

Girgiza kai tayi tace "lafiyata k'alau kawai naga zaman ne yayi yawa yakamata musan abin yi"

Da sauri yace"Amma gashi munada shanun madara dayawa,kawai zanna shiga gari ina siyarwa tunda duk k'auyen nan mune masu shanun madara"

Dubanshi tayi tace"nayi tunanin haka,amma wa zena kula mana da shanun ya kaisu kiwo?"

Shima shuru yayi baice komaiba,can ta dubeshi tace"kaga ni zanna shiga gari in rink'a siyar da nono da kuma madarar shanun,kai sekana kai shanun kiwo ko?"

Shuru yayi badon ranshi yasoba yace"Amma bakida lafiya fa,kuma kinga akwai nauyi"

Murmushi tayi tace"a.a kamal,naji sauk'i,zan iya karka damu,mudai Allah sanya mana Albarka kawai"

Yace "ameen"

Hakan kuwa akayi,kullum zatana fita tallan nono da madara shikuma yatafi kiwo,cikin rahama ta ubangiji cikin k'ank'anin lokaci kayanta ya kar6u,Dan madarar shanu har rasawa akeyi,kullum masu kud'in garin zaka gani cike wajanta suna siyan madara da nono,tun tanayin k'warya biyu ta koma fita da biyar,wani lokacinma kasa mata yakeyi,ganin ko yaushe ana samun k'arin masu siya tasa aka mata d'an bukka kaman shago a wajan da take siyarwan.

Yanzu bata iya d'aukan nono da madara saboda yamata yawa,sai dai tasamu d'an amalanke ya turo mata tundaga gida har inda take siyarwa sannan ta biyashi.

Intayi ciniki kuwa haka zata siyo musu K'wan zabbi da kaji tazo su dafa suci.

Ana hakane ranan tafito talle,d'aga kan da zatayi sukayi ido hud'u da .........

   For comments. 08144932303

SHINE GATA NAWhere stories live. Discover now