SHINE GATA NA

217 19 2
                                    

🌸 *SHINE GATA NA*🌸

Story &written By
👇🏻
'''Aysher Abbakar(meerah)'''

® ​PURE MOMENT OF LIFE WRITERS​
​ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş​

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
​#IG PML WRITERS​
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

Follow me on wattpad @aysherabbakar.

This page is dedicated to meerah novels group 1&2,I love u all,especially my honourable guests of d day,Allah barmu tare.

*3-4*

Jikin matar ne ya hau 6ari ganin abunda yake shirin faruwa,fitowa tayi a motar takira me motar, da gudu ya k'araso Dan tabbatar da abunda ta gayamishi,gaba d'aya jiyayi zuciyarshi tak'i gasgata abunda yafaru,direbobi 'yan uwanshi yakira,nan suka taho suka fito da ita a motar suka shinfid'ata kan tabarma,zagayeta akayi ana dubata ko tana numfashi amma ina,Dan har jikinta ya sassake,ganin hakane yasa kamal sakin wani kuka had'eda k'ank'ame farzeen,ji yayi sauran mutanen suna cewa"sedai fa hak'uri Dan tariga ta rasu"

Wannan maganan ba k'aramin girgiza kamal yayi ba,zubewa gaban gawar yayi yana kuka yana cewa

"Amma na Dan Allah kitashi,kinmanta bamuda kowa a rayuwa seke da farzeen?Amma na karki tafi kibarmu,Dan Allah kitashi mutafi gida,kece gatan mu,ni da farzeen muna buk'atarki a rayuwarmu"

Ganin ko motsawa batayiba balle yasa ran zata tashi yasa hankalinshi dad'a tashi,wani irin ihu yasake yana fad'in"Abba wlhy Na tsaneka,bana sonka,se Allah ya saka mana"

Mai anguwan sune yazo wucewa yaga kamal yanata kuka ga mamanshi kwance an zagayeta,tsayawa yayi yazo kusada kamal ya dafashi yace"kamal lafiya?meyafaru?"

Cikin kuka kamal yace"wai cewa sukayi Amma na ta mutu"

Dasauri me anguwa ya k'araso wajan ya ta6a ta Dan gasgatawa,salati yakamayi yana nanata wa,kamal ne yadubeshi yace "kagani bata mutuba ko?mu kaita asibiti Dan Allah"

Ganin anata cika awajan ne yasa me anguwan yin waya akakawo ambulance,kai tsaye gida suka wuce nan akasa likita ya dubata,nan ya tabbatar musu zuciyan tane ya buga lokaci d'aya kuma Allah yamata rasuwa"

Kaman Wanda farzeen taji abunda akace nan tafara zunduma kuka har bakinta da harshenta suna kakkarwa,kamal ma kukan yakeyi na tausayin irin halinda zasu shiga,mak'ota aka kira suka mata wanka da sutura suka fito da ita, anzo fita da ita ne kamal kuka farzeen ihu,gashi yak'i ajiye Farzeen,yana k'ank'me da ita,da k'yar yayarda wata mak'ociyarsu ta kar6eta akaje yima Amma sallah.

Tunda aka bisine Amma kamal yakasa kuka,juya kai kawai yake yana cije le6e,komai tsaya mishi yayi,Farzeen kuwa da k'yar aka samu Tasha madara tayi bacci.

Tunda Amma tarasu babu wani danginta dayazo,dama Kamal yasan babu Wanda zezo saboda Amma batada kowa se Allah.

*Bayan kwana bakwai*

Kamal ne zaune cikin gonansu dayake bayan gidan,yana zaune gindin bishiya,jikin bishiyan kuma zanin Ammanshi ya k'ulla yayi kaman lilon jira jirai yasaka Farzeen ciki yana mata lilo har tayi bacci.

Komawa yayi ya zauna ya buga tagumi yarasa me yake mishi dad'i.

Wani yaro na hango da baze wuce sa.an Kamal ba ya nufo inda Kamal yake d'aukeda kwanon abinci,sallama yamishi sannan ya zauna kusadashi,dubanshi Kamal yayi yace

"Mubarak ya kake?"

"Lafiya Kamal ya Farzeen?"

"Lafitanta k'alau gatanan tana bacci"

Shuru dukansu sukayi,Mubarak ne ya dubi Kamal yace"ga abinci nan mamana tace nazo muci"

Nan suka fara cin abincin har suka cinye,tashi sukayi suka nufa wajanda shanunsu kamal suke na madara Wanda a k'alla zasu kai Talatin,ga raguna da tinkiya sunkai 20.

Mubarak ne yafara taya kamal gyara wajan suka kwashe kashin sannan suka basu abinci suka d'ebo musu ruwa a rijiyan wajan.

Kukan Farzeen ne ya ankarar da Kamal, hakan yasashi ajiye bokitin da gudu yanufa bishiyanda ya kwantar da ita,d'aukanta yayi ya bata madarar saniyan d'aya tatsa mata,nandanan ta shanye,kuka tafarayi yayita jijjigata amma tak'i yin shuru,zama yayi shima yasaka kuka had'eda rungumeta cikin kuka yana cewa

"Farzeen d'ina kiyi hak'uri kiyi shuru Dan Allah,me kikeso nabaki Farzeen?"

Itakuwa kuka take tana fad'in "Ammaaaa"

Wani kukanne ya kwace mishi yace"Farzeen Amma tatafi tabarmu,bamuda gata bamuda kowa se Allah, Farzeen ki tausayamun kidena kuka Dan Allah, Amma na tace na kula dake bayan ranta nazama gatanki,Farzeen bakida kowa ni kad'aine *gatan ki*"

Tunda suke abun Mubarak yana tsaye yana kallonsu,hawaye shima yakeyi,juyawa yayi ya d'auko ruwa abokiti da sabulu,cire mata kaya yayi ya sakata a bokitin gaba d'aya yafara mata wanka,nan Farzeen ganinta cikin ruwa tafara dariya tana bubbuga hanunta cikin ruwan.

Seda yagama mata sannan ya shafa mata mai yasaka mata kaya ya goyeta.nan takoma bacci shima suka koma wajan shanunsu da Mubarak.

Suna cikin aikinne sukaji ana magana ta bayansu,juyawa Kamal yayi Dan ganin waye,wani mutumin k'auyensune ya gani zaune cikin keken shanu ya dubi Kamal yace"wannan gonan yazama nawa mamanka bata gama biyana kud'inba Dan haka kaje ka d'aukomun takardun filin nan"

Gaban Kamal ne ya fad'i idonshi ya cicciko da k'walla yace"..........


For comments only 08144932303

SHINE GATA NAWhere stories live. Discover now